Saturday, March 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyo yanda dubban mutane a Kano ke tururuwa zuwa Hotoron Arewa dan shan wani ruwan gulbi da wanka dashi wanda suka ce wai sun ga sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikin Gulbin

Kalli Bidiyo yanda dubban mutane a Kano ke tururuwa zuwa Hotoron Arewa dan shan wani ruwan gulbi da wanka dashi wanda suka ce wai sun ga sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikin Gulbin

Duk Labarai
Mutane da yawa ne a Kano ke tururuwa zuwa Hotoron Arewa inda suka ce an ga wani Gulbi a garin da sahun Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) a cikinsa. Mutane dai na kokawar shan ruwan da kuma yin wanka a cikinsa dan neman tubarraki. Mutane sun mayar da gurin kamar wani wajan Ibada inda masu fama da ciwuka da suka dade basu warke ba ke zuwa dan su sha ruwan gulbin ko su yi wanka dashi. A Bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sadarwa wanda hutudole.com ya gani, an nuna yara da matasa maza da mata suna kokawar shan ruwan da watsawa a jikinsu. https://twitter.com/bapphah/status/1914187045083247072?t=_r5ZFF-W63swwbcEDrnZGQ&s=19 A wajan an ga yanda Aljanun wata mata ya tashi sannan an ga yanda wata mata ko lullubi babu ta je wajan.
Fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na gwamna Bala Muhammad sun cika Titunan Bauchi

Fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na gwamna Bala Muhammad sun cika Titunan Bauchi

Duk Labarai
An wayi garin yau, Litinin da fastocin yakin neman zaben shugaban kasa na 2027 na Gwamna Bala Muhammad a titunan Bauchi. Rahoton yace an kika fastocin a guraren da suka fi faukar hankali irin su shataletale da jikin pol din wutar lantarki da sauransu. Masu lika fastar sun ce wasu 'yan siyasa Ya’u Ortega da Talolo ne suka basu aikin lika fastar. Daily Trust ta yi kokarin jin ta bakin wadanda suka bayar da aikin lika fastar amma abin ya ci Tura.
Fafaroma da ya mutu yau na ta shan yabo saboda goyon bayan ‘yan Luwadi da Madigo

Fafaroma da ya mutu yau na ta shan yabo saboda goyon bayan ‘yan Luwadi da Madigo

Duk Labarai
Fafaroma Francis Limamin cocin Katolika na ta shan yabo kan abubuwan da ya shahara akansu. Cikin abubuwan da ya sha yabo akansu shine goyon bayan 'yan Luwadi da Madigo. Duk da ya samu Turjira daga da yawa daga cikin limaman cocin amma ya tsaya tsayin daka dan nuna goyon bayansa ga 'yan Luwadi da madigo da kwatar musu hakkinsu. Hakanan yayi suna wajan nuna rashin jin dadin kisan da akewa Falasdinawa. Hakanan yayi suna wajan Ganin an samu jituwa tsakanin Kirista da musulmai. Ya kuma yi suna wajan ganin an baiwa 'yan ci rani kariya. Hakanan yayi suna wajan son kwallon kafa.
Masu garkuwa da mutane sun Kàshè wannan matar

Masu garkuwa da mutane sun Kàshè wannan matar

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutane sun kashe wannan matar me suna Maryann Oluchukwu Onwuchekwa 'yar Kimanin shekaru 30. Rahoton yace an sace tane tare da mahaifinta da bashi da lafiya da matar dan uwanta amma daga baya aka bar babanta saboda rashin lafiyarsa. Daga baya an sako matar dan uwanta amma ita daga baya an tsinci gawar ta a daji. Tuni 'yan uwanta suka bayyana sanda za'a yo jana'izarta. Lamarin ya farune a Amansea dake karamar Hukumar Awka North dake jihar Anambra.
Ji yanda aka kama Wata Babbar mace me danwake data yiwa Almajiri me shekaru 14 fyàdè a jihar Bauchi

Ji yanda aka kama Wata Babbar mace me danwake data yiwa Almajiri me shekaru 14 fyàdè a jihar Bauchi

Duk Labarai
Shugaban Hukumar ta Hisbah na shiyyar Katagum da ke Azare, Malam Ridwan Muhammad  Khairan ya bayyana cewar, ana zargin matar, wadda ake kira Baba Mai Ɗan Wake da laifin yin fasikanci ta hanyar tilasawa da yaudara da wani almajiri dan kimanin shekaru 14, bayan ta sanya masa maganin ƙarfin maza a cikin lemon kwalba don ya riƙa biya mata buƙata. Ya ce almajirin ya haɗu da Nana Mai Ɗan Wake da yake mata wanke-wanke a Sabuwar Tashar Jama’are ne, a cikin garin Azare, inda ta buƙaci ya riƙa zuwa gidanta yana kwana, inda ta rika yaudarar sa har ta riƙa yin lalata da shi. A cewar Malam Ridwan Mohammed Khairan, sun cafke matar ne bayan samun labari cin zarafin almajirin ta hanyar neman sa da ya riƙa biya mata buƙata irin ta mata da miji. Ya ce almajirin da kansa ya gudu ya nemi mai unguwa...
Kalli Bidiyo: Ina jin Sharrin da Dan Bello Yawa Sheikh Bala Lau nasan karshen abinda Dan Bello yake yi yanzo, ana ba Karuwai Kwangilar Biliyoyin Naira wadda ba a baiwa malamai>>Sheikh Daurawa

Kalli Bidiyo: Ina jin Sharrin da Dan Bello Yawa Sheikh Bala Lau nasan karshen abinda Dan Bello yake yi yanzo, ana ba Karuwai Kwangilar Biliyoyin Naira wadda ba a baiwa malamai>>Sheikh Daurawa

Duk Labarai
Babban Malamin addinin Islama Sheikh Aminu Daurawa ya mayar da martani kan labarin da Dan Bello yayi na cewa, an baiwa Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Bala Lau Kwangilar gina azujuwa amma ba'a yi su ba. A bidiyon da hutudole ya ci karo dashi yana yawo a kafafen sada zumunta, Mun ji malam na cewa shi fa me da'awa ba ma'asumi bane. https://www.tiktok.com/@sobman_fans_pantami/video/7495645585404333318?_t=ZM-8vioM5dU3Nv&_r=1 Yace yau idan aka ce ga malami yaci kudin wani dan kada a zubar masa da mutunci kamata yayi mutane su hada kudi su biya. Yace akwai wani abu da yaje nema wani ofis amma ya bashi wahala inda wani yace malam ya daina wahalar da kansa yace akwai karuwar me ofis din da zaiwa magana a bashi abinda yake nema. Yacw karuwai ana basu kwangilar Biliyan da 'yan D...
Wata Sabuwa:Rikici ya barke tsakanin Jihohin Benue da Ebonyi, An kàshè mutane 6, wasu sun jikkata

Wata Sabuwa:Rikici ya barke tsakanin Jihohin Benue da Ebonyi, An kàshè mutane 6, wasu sun jikkata

Duk Labarai
Mutane 6 ne suka mutu a wani rikici da ya kunno kai tsakanin Al'ummar Ezza dake karamar Hukumar Ado a jihar Benue da kuma makwabtansu Effium na dake jihar Ebonyi. Wannan rikici ya dauki shekara da shekaru yana faruwa inda aka yi iya kokari dan kawo karshen shi amma lamarin ya faskara. Wata majiya daga yankin tace rikicin kwanannan ya barkene ranar Asabar da misalin karfe  2:30 p.m. inda wasu 'yan Bindiga da aka yi amannar daga Effium suke suka afkawa garin Ezza. 'Yan Bindigar sun bude wuta inda suke harbin kan mai uwa da wabi. Rahoton yace maharan sun kuma afkawa kayan mutane da sata. Kokarin jin ta bakin kakakin 'yansandan jihar ya ci Tura.
Kalli Bidiyon yanda kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja

Kalli Bidiyon yanda kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wannan Bidiyon ya nuna yanda Kyamarar CCTV ta kama wani Barawon Kwamfuta a Abuja. Mutumin yayi satar ne a wani asibiti dake Abujan saidai ba'a kai ga gane ko wanene ba. https://www.youtube.com/watch?v=Z6fCBJsFiEk Dan haka ake neman duk wanda yasan inda za'w sameshi ya gaggauta sanar da jami'an tsaro.