Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ku Daina Takalarmu, Tinubu zai iya tsige kowane gwamna, na jihar Rivers ne tsautsai ya fada kanshi ya zama na farko>>Tinubu ya gargadi Gwamnoni

Ku Daina Takalarmu, Tinubu zai iya tsige kowane gwamna, na jihar Rivers ne tsautsai ya fada kanshi ya zama na farko>>Tinubu ya gargadi Gwamnoni

Duk Labarai
Babban lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi ya kare matakin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauka na dakatar da gwamnan jihar Rivers. Inda yace shugaban kasar na da karfin ikon dakatar da kowanw Gwamna. Fagbemi ya gargadi gwamnonin cewa duk gwamnan dake neman zama barazana ga Gwamnatin Tinubu na iya fuskantar dakatarwa. Yace a yau gwamnan jihar Rivers ne a gobe zai iya zama kowane Gwamna. Ya gargadi cewa babu wanda zasu bari ya mayar da Dimokradiyya abin wasansa.
Bidiyo Da Duminsa: Mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti sun fara zaben dan yi mata kiranye ta sauka daga wakilcinsu da take a majalisar Dattijai

Bidiyo Da Duminsa: Mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti sun fara zaben dan yi mata kiranye ta sauka daga wakilcinsu da take a majalisar Dattijai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi sun fara yin zabe dan yi mata kiranye ta dawo daga wakiltarsu da take a majalisar Dattijai. Bidiyo ya nuna yanda tuni aka fara kada kuri'a dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye. Sanata Natasha Akpoti dai ta zargi kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da nemanta da lalata zargin da ya karyata. Dalilin haka aka dakatar da ita daga ayyukan majalisar na tsawon watanni 6. kalli Bidiyon zaben anan
Shugaba Tinubu ya rantsar da Gwamnan Rikon kwarya na jihar Rivers

Shugaba Tinubu ya rantsar da Gwamnan Rikon kwarya na jihar Rivers

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Étè Ibas (retd.). Bikin rantsarwar ya samu halartar shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila, da babban lauyan Gwamnati, Mr Lateef Fagbemi, SAN, da kuma sakataren shugaban kasa, Mr Hakeem Muri-Okunola. Da misalin karfe 12:48 pm ne Ibas ya shiga fadar Shugaban kasar.
Kamfanin mai na Dangote ya sanar da daina siyar da mai a Naira

Kamfanin mai na Dangote ya sanar da daina siyar da mai a Naira

Duk Labarai
Kamfanin matatar mai ta Dangote ta sanar da cewa ta dakatar da sayar da man fetir da kuɗin Najeriya wato Naira. Kamfanin ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa dilallan man fetir a yau Laraba. Sanarwar ta ce ''Kamfanin tatar mai ta Dangote ta dakatar da sayar da fetir a naira na wani lokaci. Hakan ya zama wajibi ne saboda kaucewa rashin daidaito da ake samu tsakanin ribarmu da kuɗin da muke sanya wa masu sayen ɗanyan mai wanda a yanzu galibi da dala muke yi.'' Kamfanin ya kuma ƙara da cewa bisa wannan dalilin, wajibi ne su sauya kuɗin da suke siyar da man domin ya yi dai-dai da kuɗin da su ke siyan ɗanyen mai na wani ɗan lokaci. Sanarwar ta kuma ce kamfanin ya dukufa wajen biyan buƙatun kasuwannin Najeriya, kuma da zarar sun karɓi jiragen dakon mai da aka siya da Naira d...
Gwamnatin tarayya zata sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar Rivers kudaden jihar ta aka rike

Gwamnatin tarayya zata sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar Rivers kudaden jihar ta aka rike

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kudaden jihar Rivers da aka rike zasu sakarwa gwamnatin rikon kwarya ta jihar karkashin kulawar Vice Admiral Ibok Ibas (retd). Gwamnatin tace matakin da shugaba Tinubu ya dauka a jihar Rivers ya daukeshi ne a daidai lokacin da ya dace dan kaucewa lalacewa al'amura a jihar. Gwamnatin ta kuma ce, Tsohon gwamnan jihar, Nyesome Wike bashi da hannu a wajan rikicin siyasar jihar da ya kai ga saka dokar tabacin. Babban akanta janat na kasa, Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Laraba. Ya bayyana cewa shin sai yaushene ake son ganin shugaba Tinubu ya dau wannan mataki? Yace sai abubuwa sun rinchabe? Yace yanzu ne daidai lokacin da ya kamata a dauki matakin.
Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu – Fubara

Za mu bi hanyoyin da doka ta tanada wurin dawo mana da haƙƙinmu – Fubara

Duk Labarai
Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara ya ce tun hawansa mulki, ya yi ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma kawo cigaba a jihar, sai dai ƴan majalisar dokokin jihar suna ta kawo cikas ga ƙoƙarin nasa. Gwamnan da aka dakatar ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar bayan shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da shi da mataimakiyarsa na watanni shida saboda rikicin siyarsa da ya ki ci ya ki cinyewa. Fubara ya ce dukkanin abubuwan da ya yi da matakan da ya ɗauka ya yi su ne bisa rantsuwar da ya sha na kama aiki, inda ya ce hakan ne ya sa bayan da shugaba Tinubu ya shiga tsakani, ya yi gaggawar aiwatar da yarjejeniyar da aka amince ciki har da dawo da kwamishinonin da suka ajiye aiki. Ya kuma ce ba su yi ƙasa a ...
Shugaban riƙon ƙwarya a Rivers ya isa fadar Shugaba Tinubu

Shugaban riƙon ƙwarya a Rivers ya isa fadar Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban riƙon ƙwarya na Rivers, Vice Admira Ibok-Ete Ibas da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya naɗa kan wannan mukamin ranar Talata ya isa fadar shugaban ƙasa. Da alama zuwan nasa na da alaƙa da dokar ta-ɓacin da Tinubu ya ƙaƙaba a Rivers bayan da jihar ta faɗa rikicin siyasa. Tuni dai wannan mataki da Shugaba Tinubu ya ɗauka ya janyo mabanbantan ra'ayoyi inda al'ummar ƙasar da ƴansiyasa da ma masana ɓangaren shar'a ke ta tsokaci a kai.
Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers

Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers

Duk Labarai
Majalisar dattawan Najeriya ta ɗage tattaunawa kan ƙudirin farko da za su tafka muhawara a zamansu na yau game da amincewa da dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ba tare da bayar da dalilin jinkirin ba. A yanzu majalisar za ta zauna kan wannan batu da ƙarfe uku na rana. An yi tsammanin za a tafka muhawara kan ƙudirin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya gabatar, da safiya sai dai ƴanmajalisar sun ɗage tattaunawar. Ƙudirin dai ya bayyana damuwa game da ruruwar tashin hankali da ya jefa jihar Rivers cikin garari tare da haifar da koma-baya a tafiyar da al'amuran gwamnati. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa kafin dokar ta-ɓacin ta soma aiki, dole ne sai ƙudirin ya samu goyon bayan kashi ɗaya bisa uku na ƴanmajalisar - 73 cikin sanatoci 109. A ...
Yadda gobara ta lalata dukiya ta biliyoyin naira a Kano

Yadda gobara ta lalata dukiya ta biliyoyin naira a Kano

Duk Labarai
Wata gobara da ta tashi a wata kasuwar ƴan gwangwan da ke Dakata a jihar Kano ta lalata dukiya ta biliyoyn naira. Kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da labarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba. Bayanai sun ce gobarar ta soma ne bayan da aka ga tartsatsin wuta daga wasu sandunan wutar lantarki inda kuma nan da nan ta bazu zuwa masana'antar sarrafa gyaɗa. Kwamishinan ƴansanda na Kano, Ahmed Bakori ya kai ziyara inda lamarin ya faru inda ya bayyana yanayin a matsayin abin takaici. Ya kuma ce an kama wani mutum da ya yi koƙarin sace wasu kayayyaki a wurin gobarar. A cewarsa za a gudanar da bincike mai zurfi domin kare sake afkuwar haka. Ya kuma yi yaba da hanzarin da jami'an hukumar kashe gobara da sauran mutanen gari suka yi wajen kashe...
Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne – Atiku

Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne – Atiku

Duk Labarai
Ɗantakarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP a babban zaɓen ƙasar na 2023, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka a jihar Rivers a amatsayin nuna iko a siyasa. Ya bayyana cewa ga masu bibiyar yadda rikicin Rivers ke kasancewa sun san cewa Bola Tinubu ya kasance mai ruwa da tsaki a rikicin siyasar da ya mamaye Rivers. "Kau da kai da kuma nuna ko oho wajen kare ta'azzarar rikicin abin kunya ne." kamar yadda Atiku ya bayyana. Ya ce abu ne da ba za a yafe ba, yadda aka ƙara jefa yankin Neja Delta cikin rikici da rashin kwanciyar hankali - lamarin da ya warware ƙoƙarin samar da zaman lafiyar da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar'adua ya yi. "An wanke shekarun da aka shafe da samun cigaba saboda kawai wata buƙata ta ƙashin kai." in ji Atiku. ...