Thursday, March 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers

Majalisar Dattawa ta jinkirta muhawara kan ƙudirin dokar ta-ɓaci a Rivers

Duk Labarai
Majalisar dattawan Najeriya ta ɗage tattaunawa kan ƙudirin farko da za su tafka muhawara a zamansu na yau game da amincewa da dokar ta-ɓaci a jihar Rivers ba tare da bayar da dalilin jinkirin ba. A yanzu majalisar za ta zauna kan wannan batu da ƙarfe uku na rana. An yi tsammanin za a tafka muhawara kan ƙudirin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele ya gabatar, da safiya sai dai ƴanmajalisar sun ɗage tattaunawar. Ƙudirin dai ya bayyana damuwa game da ruruwar tashin hankali da ya jefa jihar Rivers cikin garari tare da haifar da koma-baya a tafiyar da al'amuran gwamnati. Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa kafin dokar ta-ɓacin ta soma aiki, dole ne sai ƙudirin ya samu goyon bayan kashi ɗaya bisa uku na ƴanmajalisar - 73 cikin sanatoci 109. A ...
Yadda gobara ta lalata dukiya ta biliyoyin naira a Kano

Yadda gobara ta lalata dukiya ta biliyoyin naira a Kano

Duk Labarai
Wata gobara da ta tashi a wata kasuwar ƴan gwangwan da ke Dakata a jihar Kano ta lalata dukiya ta biliyoyn naira. Kakakin rundunar ƴansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da labarin inda ya ce ba a samu asarar rai ba. Bayanai sun ce gobarar ta soma ne bayan da aka ga tartsatsin wuta daga wasu sandunan wutar lantarki inda kuma nan da nan ta bazu zuwa masana'antar sarrafa gyaɗa. Kwamishinan ƴansanda na Kano, Ahmed Bakori ya kai ziyara inda lamarin ya faru inda ya bayyana yanayin a matsayin abin takaici. Ya kuma ce an kama wani mutum da ya yi koƙarin sace wasu kayayyaki a wurin gobarar. A cewarsa za a gudanar da bincike mai zurfi domin kare sake afkuwar haka. Ya kuma yi yaba da hanzarin da jami'an hukumar kashe gobara da sauran mutanen gari suka yi wajen kashe...
Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne – Atiku

Dokar ta-ɓaci a Rivers cin zarafin dimokraɗiyya ne – Atiku

Duk Labarai
Ɗantakarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar PDP a babban zaɓen ƙasar na 2023, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka a jihar Rivers a amatsayin nuna iko a siyasa. Ya bayyana cewa ga masu bibiyar yadda rikicin Rivers ke kasancewa sun san cewa Bola Tinubu ya kasance mai ruwa da tsaki a rikicin siyasar da ya mamaye Rivers. "Kau da kai da kuma nuna ko oho wajen kare ta'azzarar rikicin abin kunya ne." kamar yadda Atiku ya bayyana. Ya ce abu ne da ba za a yafe ba, yadda aka ƙara jefa yankin Neja Delta cikin rikici da rashin kwanciyar hankali - lamarin da ya warware ƙoƙarin samar da zaman lafiyar da tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar'adua ya yi. "An wanke shekarun da aka shafe da samun cigaba saboda kawai wata buƙata ta ƙashin kai." in ji Atiku. ...
Duk da kokarin dan shugaban kasa, Seyi Tinubu na raba abincin Shan ruwa ‘yan Arewa da yawa na ta sukarsa da cewa ziyararsa a jihohin Arewa bata amfanesu da komai ba

Duk da kokarin dan shugaban kasa, Seyi Tinubu na raba abincin Shan ruwa ‘yan Arewa da yawa na ta sukarsa da cewa ziyararsa a jihohin Arewa bata amfanesu da komai ba

Duk Labarai
Da yawan 'yan Arewa ne suke sukar ziyarar da dan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihohin Arewa inda ya raba kayan abincin buda baki. Wasu dai na ganin wannan rabon abincin da yayi ma cin fuskane kamar ya mayar da mutane mabarata ne ko mayunwata. Daya daga cikin wadanda suka soki dan shugaban kasar akwai dan gwamnan Bauchi, Shamsuddeen Bala Mohammed Shamsuddeen ya nemi dan shugaban kasar maimakon raba abinci a hannu, ya karfafu matasa da jari ko ayyukan yi zai fi inda ya bayyana cewa irin wannan rabon abincin da yake alamace dake nuna cewa mahaifinsa ya gaza. Hakanan a kafafen sada zumunta da yawa ma an samu masu sukar dan shugaban kasar. Da yawa sun bayyana ra'ayi irin na dan Gwamnan Bauchi inda suke ganin kawowa mutane musamman matasa abubuwan ci gaba shi yafi fiye ...
Yanzu-Yanzu: Dangote yace zai daina sayarwa da Najeriya man fetur

Yanzu-Yanzu: Dangote yace zai daina sayarwa da Najeriya man fetur

Duk Labarai
Rahotonni sun bayyana cewa, Attajirin dan kasuwa Aliko Dangote zai daina sayarwa da Najeriya man fetur. Jaridar TheCable ta ruwaito cewa Dangote na son daukar wannan mataki ne biyo bayan kasa cimma matsaya akan ci gaba da cinikin man fetur din da kudin Naira maimakon dalar Amurka. Saidai majiyar tace matatar man zata ci gaba da fitar da man fetur din zuwa kasashen waje dan kuwa dama daga kasashen wajen take siyo danyan man da take tacewa. Matatar Dangote na sayarwa da Najeriya man fetur din data tace ne da Naira saboda a kudin Naira take sayen danyen man fetur da take saya daga hannun gwamnati. Saidai wannan yarjejeniyar a yanzu ta kare.
Kalli Bidiyo: “Tuhajjud da Maulud hukuncin daya ne a Musulunci.”>>Inji Sheikh Makari

Kalli Bidiyo: “Tuhajjud da Maulud hukuncin daya ne a Musulunci.”>>Inji Sheikh Makari

Duk Labarai
“Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Maqari ya bayyana cewa da Tahajjudi da Maulidi duk hukuncinsu daya a musulunci. Malam yace ko da hadisi me rauni da zai kare Tahajjudi babushi. Yace amma ba yace bai halatta ba, yace idan an samu abu da bashi da illa ko da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Bai aikata ba ana iya yi. Malam ya kara da cewa amma maganar gaskiya duk hujjar da me kare Tahajjudi ke amfani da ita, shima Maulidi za'a iya yin amfami da wannan hujjar a kareshi. Kalli Bidiyon anan
Wata Sabuwar cuta da ba’a santa ba ta bulla a Arewa inda zuwa yanzu ta kashe mutane 6 da yawa na kwance a Asibiti

Wata Sabuwar cuta da ba’a santa ba ta bulla a Arewa inda zuwa yanzu ta kashe mutane 6 da yawa na kwance a Asibiti

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kebbi na cewa akalla dalibai 6 ne suka rasu bayan bullar wata cuta da ba'a san kalarta ba a jami'ar kimiyya da fasa ta jihar me suna Kebbi State University of Science and Technology, Aleru. Rahoton yace wasu kuma na can kwance ba lafiya a asibiti. Rahoton yace duk da ana samun karuwar yawan daliban dake dauke da wannan cuta amma hukumomin makarantar sun ki su kulleta wanda hakan ya jefa iyayen dalibai cikin damuwa Wasu daliban makarantar sun koka da faruwar lamarin inda suka ce yana da alaka da rashin daukar mataki na hukumomin makarantar. Rahoton yace ba a makarantar kadai lamarin ya faru ba hadda ma cikin gari inda cutar ta kashe mutane da dama. An bayyana cutar da cewa yawanci ana korafin ciwon wuyane wanda kuma nan da nan sai mutum ya fita hayyacinsa...
Kaima Ka Aikata laifin da ya kamata a tsigeka>>Martanin Reuben Abati ga Tinubu bayan da ya dakatar da Gwamnan Rivers

Kaima Ka Aikata laifin da ya kamata a tsigeka>>Martanin Reuben Abati ga Tinubu bayan da ya dakatar da Gwamnan Rivers

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa kuma shahararren dan jarida, Reuben Abati ya soki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya aikata laifin da ya kamata ace an tsigeshi. Abati yace Gwamna ba zai ciru ba ta hanyar umarnin shugaban kasa ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi ranar Laraba a gidan talabijin na Arise TV. Hakan na zuwane bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Simi Fubara daga mukaminsa. Reuben Abati ya bayyana cewa, shu...
Kuma Dai:Farashin danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa zuwa kasar waje ya tashi inda hakan ke barazana ga kudin shigar Gwamnatin Tinubu

Kuma Dai:Farashin danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa zuwa kasar waje ya tashi inda hakan ke barazana ga kudin shigar Gwamnatin Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, farashin danyen man fetur da Najeriya ke fitarwa zuwa kasashen waje da ake kira da Brent crude oil ya sake faduwa. Farashin a yanzu ya doso Dala $70 akan kowace ganga. Hakan dai ya farune ranar Laraba inda aka alakanta dalilin da cewa Rasha ce dake shirin fara kara yawan man fetur din da take fitarwa zuwa kasuwar Duniya. Hakanan Suma kungiyar Kasashe masu arzikin Man fetur, OPEC suna shirin kara yawan man fetur din da suke fitarwa wanda hakan zai iya kara karya farashin. Kasancewar Najeriya a matsayin kasa wadda mafi yawan kudaden shigarta daga sayar da danyen man fetur suke zuwa yasa karayar farashin kewa kudaden shigar gwamnatin kasar barazana.
Ji abinda sojoji sukawa Gwamna Fubara bayan dakatar dashi da Shugaba Tinubu yayi wanda mutane da yawa ke cewa cin zali ne

Ji abinda sojoji sukawa Gwamna Fubara bayan dakatar dashi da Shugaba Tinubu yayi wanda mutane da yawa ke cewa cin zali ne

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Rivers sun ce bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Simi Fubara da mataimakinsa da Majalisar jihar, Ya baiwa sojoji umarnin kula da jihar. Tuni dai rahotanni suka bayyana cewa sojojin sun kai motocinsu da tankokin yaki gidan gwamnatin jihar. Sojojin kamar yanda rahoton jaridar Peoplesgazette ya nunar sun tsare Gwamna Fubara a gidan gwamnatin jihar ta Rivers shi da iyalinsa inda suka hanasu zuwa ko ina. Rahoton yace jim kadan bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da gwamna Fubara, sai sojojin suka kulle duka kofofin shiga da fita na gidan gwamnatin jihar. Rahoton yace Gwamna Fubara da iyalansa sun yi kokarin tattara kayansu dan ficewa daga gidan gwamnatin amma aka hanasu saboda sojojin sun hana shiga da fita daga cikin gidan gwamnatin j...