Thursday, March 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon yanda Sojojin Najeriya suka lakadawa ma’aikatan wutar Lantarki dukan tsiya saboda yawan dauke musu wuta

Kalli Bidiyon yanda Sojojin Najeriya suka lakadawa ma’aikatan wutar Lantarki dukan tsiya saboda yawan dauke musu wuta

Duk Labarai
A dazu ne muka ji yanda sojoji suka sake zuwa Ofishin hukumar wutar lantarki ta jihar Legas inda suka lakadawa jami'an hukumar dukan kawo wuka. Lamarin ya dauki hankula musamman ganin ba'a dade ba hakan ta faru a baya. A wannan karin rahotanni sun ce sojojin sun dauki manyan ma'aikata biyu inda suka kaisu barikinsu suka lakada musu duka. Wannan bidiyon ya nuna yanda lamarin ya faru. Kalli bidiyon anan
Ji yanda Wani dan jarida yawa Sanata Godswill Akpabio Tonin Sillili inda ya bayyana dalilin da ya zama dole a kama shi a daure a gidan yari

Ji yanda Wani dan jarida yawa Sanata Godswill Akpabio Tonin Sillili inda ya bayyana dalilin da ya zama dole a kama shi a daure a gidan yari

Duk Labarai
Dan jarida kuma tsohon editan jaridar Daily Times newspaper me suna Chief Tola Adeniyi ya soki kasancewar Sanata Godswill Akpabio a matsayin kakakin majalisar Dattijai. Ya bayyana cewa, kamata yayi ace Sanata Akpabio na gidan yarine ba wai a majalisar dattijai ba. Yace Akpabio da masu hali irin nasa kamata yayi ace suna gidan yari, ya kara da cewa ka je ka duba zarge-zargen da akewa Sanata Akpabio inda ake zargin ya ci kudi Biliyan 44 da biliyan 90 da dai sauransu. Yace sannan kuma ga zargin lalata da sanata Natasha Akpoti ke masa. Yace abin kunyane ace irin wadannan mutanen ne akewa jiniya ana yawo dasu a kan totunanmu.
Ba neman izinin Komawa SDP na je yi wajan Buhari ba, najene in sanar dashi a matsayinsa na Uban gidana>>El-Rufai

Ba neman izinin Komawa SDP na je yi wajan Buhari ba, najene in sanar dashi a matsayinsa na Uban gidana>>El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ba neman izinin komawa SDP ya je yi wajan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba. Yace ya jene ya sanar dashi a matsayinsa na uban gidansa a Siyasa. Tsohon Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace wannan bayani ya dole yayishi saboda yanda ake ta samun rahotanni wanda ba daidai ba daga gidajen jaridu. Bayan komawar El-Rufai SDP kuma yace da sanin tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari yayi hakan, Tsohon shugaban kasar ya fito yace har yanzu yana Jam'iyyar APC saboda ta bashi dama ya zama shugaban kasa har sau 2.
Yayin da suka rasa yanda zasu yi, kasar Nijar ta roki Najeriya ta taimaka mata da man fetur

Yayin da suka rasa yanda zasu yi, kasar Nijar ta roki Najeriya ta taimaka mata da man fetur

Duk Labarai
Kasar Nijar bayan nuna cewa ba ruwanta da Najeriya ta sakko kasa inda ta nemi Najeriyar ta taimaka mata da man fetur. Wahalar Man fetur ta yi yawa a kasar ta Nijar inda ake ganin dogayen layuka a gidajen mai sannan lamarin ya taba 'yan kasuwa da yawa kuma ya na son durkusar da harkar sufuri. Dalilin hakane Shugaban soja na kasar Nijar ya aiko da wakilansa da suka hada da ministan man fetur na kasar da wasu suka je Abuja suna neman a taimakesu da man fetur din. Tuni dai aka aika da tankokin man fetur 300 zywa Nijar din dan tallafa musu.
Na rasa wace irin matace Sanata Natasha Akpoti, ta kawo mana korafi, ba’a gama bincike ba ta tsallaka ta kai kara kotu, ba’a gama shari’a ba ta sake tsallakewa ta kai korafi majalisar Dinkin Duniya>>Sanata Godswill Akpabio

Na rasa wace irin matace Sanata Natasha Akpoti, ta kawo mana korafi, ba’a gama bincike ba ta tsallaka ta kai kara kotu, ba’a gama shari’a ba ta sake tsallakewa ta kai korafi majalisar Dinkin Duniya>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya koka da irin halayyar Sanata Natasha Akpoti inda yace bai san wane irin tunani gareta ba. Sanata Godswill Akpabio yace ta kawowa kwamitin da'a na majalisar dattijai korafi, ba'a gama bincike ba ta tafi ta kai kara kotu, can ma ba'a gama shari'a ba ta tafi ta kai korafi majalisar Dinkin Duniya. Sanata Godswill Akpabio yace irin wannan abun ne zai iya sawa a daina baiwa mata mukaman siyasa.
Bamu yadda da dawowar El-Rufai Jam’iyyar mu ba, yazo ne kawai ya cimma burinsa>>Kungiyar Matasan Jam’iyyar SDP

Bamu yadda da dawowar El-Rufai Jam’iyyar mu ba, yazo ne kawai ya cimma burinsa>>Kungiyar Matasan Jam’iyyar SDP

Duk Labarai
Kungiyar matasan Jam'iyyar SDP sun bayyana cewa basu yadda da komawar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai Jam'iyyar ba. Kungiyar ta bakin shugabanta, Abdulsamad Bello ta bayyana cewa, El-Rufai kawai yana son samun damar da zai cimma burinsa ne a Jam'iyyar. Sun kara da cewa, abin takaici ne yanda Jam'iyyar ta baiwa El-Rufai dama aka tarbeshi hannu biyu-biyu ba tare da la'akarin hadarin da ke tattare dashi ba. Matasan sun ce karamin misali shine yanda El-Rufai da ga zuwansa gashi yana son yayi kaka gida a Jam'iyyar har yayi yunkurin tsike sakataren Jam'iyyar, Dr. Olu Agunloye daga mukaminsa. Kungiyar tace zata yaki duk wani yunkuri na neman mikawa El-Rufai Jam'iyyar inda suka gargadi shuwagabannin Jam'iyyar kada su aikata haka.
Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai a tarihi

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai a tarihi

Duk Labarai
Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar Premier na wata-wata karo na bakwai a tarihin. Mohamed Salah ya lashe kyautar watan Fabrairu a matsayin ɗan wasan da ya fi hazaƙa a watan, bayan da bajintar da ya yi a watan, a ƙoƙarin da ƙungiyarsa ke yi na lashe gasar Premier. Ɗan wasan na ƙasar Masar ya ci ƙwallo shida, ciki har da biyu da ya zura a ragar Bournmouth da wanda ya zura a ragar Manchester City a watan, sannan ya taimaka aka ci huɗu. Mo Salah ya samu kyautar ne bayan doke Beto da Jean-Philippe Mateta da Yankuba da Djed Spence da kuma Dominik Szoboszlai. Da wannan nasara, a yanzu Salah ya kamo tarihin da Sergio Aguero da Harry Kane suka kafa na cin kyautar sau bakwai. Sannan ya zarta Steven Gerrard da Cristiano Ronaldo waɗanda suka ci k...
Wata mata ta kkàshè kishiyarta a jihar Jigawa

Wata mata ta kkàshè kishiyarta a jihar Jigawa

Duk Labarai
Hukumomin ƴansanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun cafke wata mata bisa zarginta da kashe kishiyarta ta hanyar zuba mata ruwan zafi. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Buju da ke ƙaramar hukumar Dutse babban birnin jihar Jigawa, kuma bayanai na cewa matar ta rasa ranta ne sakamakon rashin jituwar da ta kaure tsakaninta da abokiyar zamanta. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam ya shaida wa BBC cewa matar ‘yar shekara 20 ta watsa wa abokiyar zamanta tafasasshen ruwan zafi ne, sakamakon taƙaddamar da ta kaure tsakaninsu. SP Shi’isu Adam ya ce marigayiyar ta samu mummunan ƙuna, inda aka kai ta asibiti daga baya kuma ta rasu a can. Mai unguwar ƙauyen, Malam Kabiru Abbas ya shaida wa BBC cewa bayan ƙura ta lafa, wadda aka watsa wa ruwan zafin, kafin ...