Sunday, July 12
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Masu Ikirarin Jìhàdì sun shiga Uku, An fito da rundunar sojojin da basu taba yin rashin nasara ba an kaisu Arewa Maso gabas, sojojin kansu sai murna suke

Masu Ikirarin Jìhàdì sun shiga Uku, An fito da rundunar sojojin da basu taba yin rashin nasara ba an kaisu Arewa Maso gabas, sojojin kansu sai murna suke

Duk Labarai
Rahotanni da hutudole ke samu na cewa Rundunar sojojin Najeriya ta fito da daya daga cikin rundunar sojojin ta mafi karfi da bayar da sakamakon da ake so wajan yaki inda aka kaisu Arewa maso gabas. Sunan rundunar shine 134 Special Forces Battalion Wanda a baya sun yi yaki tare da rundunar sojoji da Najeriya ta dauoo haya daga kasar Afrika ta Kudu a shekarar 2013 suka yaki Boko haram,. Rundunar ta kuma taba yaki a Kangarwa dake jihar ta Borno a lokacin da aka yi fama da 'yan Bindiga wadanda ba B0k0 Hàràm ba kuma ta gama dasu. Sannan a shekarar 2019, sun kuma yaki B0k0 Hàràm inda kuma suka yi nasara. Hakanan a shekarar 2022 an kai rundunar jihar Kaduna inda ta yaki 'yan Bindiga a camma kuma ta yi nasara. Sojojin dake Arewa maso gabas rahotanni sun bayyana cewa sai murna suke d...
Ji yanda dan majalisa yawa abokan aikinsa tonon silili, yace yanzu kowane Sanata ana bashi Naira Biliyan 2 dan majalisar wakilai kuma Naira Biliyan 1 dan suwa mutanen mazabarsu aiki tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur

Ji yanda dan majalisa yawa abokan aikinsa tonon silili, yace yanzu kowane Sanata ana bashi Naira Biliyan 2 dan majalisar wakilai kuma Naira Biliyan 1 dan suwa mutanen mazabarsu aiki tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur

Duk Labarai
Wani dan majalisar tarayyar Najeriya yawa abokan aikinsa Tonon Silili inda yace babu dan majalisar dake samun kasa da Naira Biliyan 2 na yiwa mazabarsa aiki a majalisar dattijai. Yace hakanan a bangaren 'yan majalisar wakilai, babu wanda ke samun kasa da Naira Biliyan 1 shima dan yiwa 'yan mazabarsa aiki. Ya bayyana hakane a jihar Osun, kamar yanda jaridar Sahara reporters ta ruwaito. Saidai ba'a bayyana sunansa ba, yace 'yan majalisar sun samu karin kudinne bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur. Hakanan yace suma Gwamnoni an kara musu kudaden da ake basu na yiwa jihohinsu aiki. Wannan dai ya zowa mutane da mamaki ganin yanda 'yan majalisar ke kukan suma suna cikin wani hali a yayin da 'yan Najeriya ke kokawa da tsadar rayuwa.
Sojojin Najeriya sun tsere daga sansaninsu a Gubio dake Jihar Borno bayan da masu ikirarin Jìhàdì suka durfafesu zasu kai musu hari

Sojojin Najeriya sun tsere daga sansaninsu a Gubio dake Jihar Borno bayan da masu ikirarin Jìhàdì suka durfafesu zasu kai musu hari

Duk Labarai
Rahotanni da hutudole ke samu daga garin Gubio na jihar Borno na cewa, Kungiyar ÌSWÀP ta yi yunkurin kaiwa garin hari ranar Litinin amma Sojoji suka dakile harin. Saidai Ranar Talata, Kungiyar ta sake durfafar garin inda ta nufi sansanin sojojin da afka mai da yaki. Saidai mutanen garin na sanar da sojojin, a wannan karin sai aojojin suka tsere. Rahoton yace ko da kungiyar ta ji sojojin sun tsere sai ta fasa kai harin suka juya. An ce dai daga baya sojojin sun koma sansanin nasu.
In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati

In ka cika Kwallon Shege ka fito mu yi dambe a bainar jama’a a ga wanene gwani ni da kai>>Oshiomhole ya gayawa Reuben Abati

Duk Labarai
Tsohon shugaban APC, kuma tsohon gwamnan jihar Edo wanda kuma tsohon shugaban kungiyar Kwadago ta NLC ne, watau Adams Oshiomhole ya nemi tsohon kakakin shugaban kasa, Reuben Abati da ya fito su daku idan ya isa. Ya bayyana hakanne a ganawarsa da gidan Talabijin na Channels TV. Yace hakane bayan da Abati a wata hira da aka yi dashi a Arise TV ya ce shin ko Ifeanyi Okowa ya tambayi Oshiomhole an yafe masa zunubansa kamin komawa APC? A baya dai lokacin yana shugaban APC, Adams Oshiomhole ya taba cewa, duk laifin mutum idan ya shiga APC an yafe masa. Saidai yanzu yace wannan magana da Abati yayi bata dace ba, shi a matsayinsa na Sanata menene hadinsa da binciken me laifi? Sannan yace shin ko Abati yana jin haushin kamun da EFCC suka masa ne bayan saukar Jonathan daga Mulki, yac...
An sake Kai wani mummunan hari jihar Filato

An sake Kai wani mummunan hari jihar Filato

Duk Labarai
An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da fiye da shanu 100 a jerin hare-haren da aka kai kan makiyaya a ƙauyuka biyu da ke cikin Kananan Hukumomin Jos na Kudu da Jos na Arewa na Jihar Filato. Hare-haren, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai ta hanyar buɗe wuta kan makiyayan da ke kiwo, sun sake jaddada yadda tsaro ya taɓarɓare a yankunan da ke fama da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, rikice-rikicen da a kullum ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi. Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren. Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin farfagand...
Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya bayar da Umarnin a dauki matasa 130,000 aiki dan su shiga daji su gama da ‘yan Bìndìgà da ake fama dasu

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya bayar da Umarnin a dauki matasa 130,000 aiki dan su shiga daji su gama da ‘yan Bìndìgà da ake fama dasu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron dazuka a ƙasar baki ɗaya, domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a Najeriya. A karkashin wannan shiri, za a ɗauki sama da masu tsaro 130,000 da za su kasance da kayan yaƙi da horo na musamman domin kare dazukan ƙasar guda 1,129. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fito daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, wanda ya wallafa ta a shafinsa na X. Sanarwar ta ce "Wannan mataki na tsaro an amince da shi ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka gudanar ranar Litinin.' "A cikin wannan tsari, shugaba Tinubu ya umurci kowace jiha da ta ɗauki ma’aikata tsakanin 2,000 zuwa 5,000 domin zama masu tsaron daji, dangane da ƙa...
Dalilin da ya sa na koma fashi bayan na yi zaman gidan yari – Matashi

Dalilin da ya sa na koma fashi bayan na yi zaman gidan yari – Matashi

Duk Labarai
Wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa, Olayinka Olwaseyi, da aka kama da laifin yi wa masu ababen hawa fashi a danja, ya amsa cewa ya koma aikata laifuka ne saboda rashin aikin yi. Wanda ake zargin, wanda aka sake kama shi watanni uku bayan fitowar sa daga gidan yari, ya yi ikirarin cewa ya so ya daina aikata laifuka amma yunwa ta tilasta masa komawa ruwa. “Ba zan koma fashi ba idan da ina da abin yi, komai kankantarsa. “Bani da aikin yi lokacin da na fito daga gidan yari, mutane sun fara guje min, babu wanda yake so ya yi mu'amala da ni. Mutane ne su ka tilasta min na koma ruwa,” inji shi. An kama Olayinka ne a ranar 13 ga Mayu, 2025, a lokacin da ya ke yunkurin yi wa wani direban mota fashi a kan gadar Mile 12, Legas. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ...
Ji dabarun da Shugaba Tinubu ke amfani dasu wajan jawo hankalin ‘yan Adawa zuwa APC

Ji dabarun da Shugaba Tinubu ke amfani dasu wajan jawo hankalin ‘yan Adawa zuwa APC

Duk Labarai
Kusan za a iya cewa da wuya gari ya waye a Najeriya ba tare da ƴan siyasa daga jam'iyyun hamayya sun sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ba, walau dai a matakin tarayya ko kuma jihohi da ƙananan hukumomi. Sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC da ya fi bai wa ƴan Najeriya mamaki a baya-bayan nan shi ne na ]tsohon ɗantakarar mataimakin shugaban ƙasa na babbar jam'iyya mai hamayya ta PDP, kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Efeanyi Okowa tare da gwamnan jihar mai ci, Sheriff Oborevwori. Bugu da ƙari, ko a wannan makon ma sai da jam'iyyar mai mulki ta karɓi sabbin masu sauya sheƙa daga jam'iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi, inda duka ƴan majalisar dattawan jihar suka koma APC. Wannan ya janyo ƴan Najeriya ke neman sanin irin dubarun da jam'iyya mai mulkin ke bi wajen...