Wednesday, March 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Majalisar Dattijai ta yi watsi da zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar Godswill Akpabio na Làlàtà

Majalisar Dattijai ta yi watsi da zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar Godswill Akpabio na Làlàtà

Duk Labarai
Majalisar dattijai ta ce bata da masaniya game da zargin da sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio na neman yin lalata da ita. Me magana da yawun majalisar, Senator Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana haka a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace Sanata Natasha Akpoti bata gabatar wada kwamitin ladabtarwa na majalisar zarge-zargen da takewa Sanata Godswill Akpabio ba. Yace dan haka ba ruwansu da maganar ba zasu dauki mataki akan abinda ke faruwa a kafafen sadarwa na yanar gizo ba ko kuma gidajen watsa labarai ba.
Gwamnatin tarayya zata baiwa kananan ‘yan kasuwa da suka yi zarra Kyautar Naira Miliyan 220, duba rabar da za’a fara rijista

Gwamnatin tarayya zata baiwa kananan ‘yan kasuwa da suka yi zarra Kyautar Naira Miliyan 220, duba rabar da za’a fara rijista

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da aniyarta ta baiwa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa kyautar kidade da gidaje da motoci. Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar kananan da matsakaitan masana'antu Temitola Adekunle-Johnson ne ya bayyana hakan ranar Litinin. Yace zasu bude shafin yin rijista nan da 7 ga watan Maris inda za'a kulle yin rijistar ranar 7 ga watan Afrilu. Yace zasu duba irin gudummawar da kasuwanci ya kawowa Najeriya kamin su zabeshi.
Sunayen Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Da Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ba Su Lasisi A Zaman Majalisar Zartaswa Ta Kasa, Yau Litinin

Sunayen Jami’o’i 11 Masu Zaman Kansu Da Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ba Su Lasisi A Zaman Majalisar Zartaswa Ta Kasa, Yau Litinin

Duk Labarai
Sunayen Jami'o'i 11 Masu Zaman Kansu Da Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ba Su Lasisi A Zaman Majalisar Zartaswa Ta Kasa, Yau Litinin. New City University, Ayetoro Ogun State University of Fortune, igbotako, Ondo State Eranova University, Mabushi Minaret University, Ikirun, Osun Annex Abubakar Toyin University, Oke-Agba, Kwara State Southern Atlantic University Uyo, Akwa Ibom State Lens University, ilemona, Kwara State Monarch University, Iyesi-Ota, Ogun State Tonnie Iredia University of Communication, Benin City Isaac Balami University of Aeronautics and Management, Lagos Kevin Eze University, Mgbowo, Enugu State Daga Jamilu Dabawa
Da Duminsa: An yi gàrkùwà da dansandan Najeriya a Abuja

Da Duminsa: An yi gàrkùwà da dansandan Najeriya a Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutanene sun sace dansandan Najeriya da wasu mutane. Rahoton yace an sace CSP Modestus Ojiebe ne akan hanyar Abuja zuwa Kaduna. Dansandan dake aiki a Kwara an yi garkuwa dashine a lokacin da yake kokarin gyaran motarsa da ta lalace a kusa da barikin 'yansanda dake Dei-Dei. Rahoton yace wata motace ta je kusa dashi ta yi fakin inda mutane dauke da makamai su 4 suka fito daga cikinta suka kwace mai wayoyinsa dana matarsa, saidai da suka ga shaidar katin aikin dansanda, sun yi garkuwa dashi inda suka jefashi cikin mota suka tafi dashi. Tuni dai aka saka jami'an tsaro a hanyoyin shiga da fita birnin Abuja. Wasu 'yansanda sun tabbatar wa da Jaridar Daily Trust da wannan labari saidai har yanzu h...
Malamin Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ya Rasu Yana Tsakar Sallar Tarawih

Malamin Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ya Rasu Yana Tsakar Sallar Tarawih

Duk Labarai
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN Allah Ya Yi Wa Dakta Musa Bara'u Gamji, Na Sashen Koyan Aikin Jarida A Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria, Rasuwa Yana Tsakar Sallar Tarawih, Jiya Lahadi A Birnin Gusau, Jihar Zamfara. An Yi Jana'izarsa Kamar Yadda Addinin Musulunci Ya Tanada A Masallacin Juma'a Na Imam Malik Dake Birnin Gusau, Jihar Zamfara Yau Litinin. Allah Ya Jikansa Da Rahama! Daga Jamilu Dabawa
Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

Wasu bala’o’i sun aukawa kasar Amurka inda A birnin Los Angeles aka yi girgizar kasa, a South Carolina gobarar daji ce ta kunno kai

Duk Labarai
An samu girgizar kasa me maki 3.9 a birnin Los Angeles na Jihar California ta kasar Amurka. Hakan na zuwane bayan da aka kammala bikin bayar da kyautar Oscar 2025. Gurare da yawa da suka hada da Pasadena, Long Beach, San Fernando Valley, Torrance, Redondo Beach da Glendale sun bayyana cewa sun ji motsin kasa. Babu dai rahoton cewa wani ya ji rauni. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da aka samu mummunar gobarar daji a birnin na Los Angeles. Hakanan a jihohin South Carolina da North Carolina na kasar Amurkar ma Wutar daji ce ta barke inda ake maganar taci kadada sama da 1,600 a South Carolina inda a North Carolina kuma taci kadada sama da 500. Mahukunta a yankunan da gobarar ta tashi sun bayar da umarnin mutane su fice daga yankunan.
Masu aikata Zina ku tuba kamin Lokaci ya kure muku, Idan ka tuba ka ci banza, Allah ya yafe>>Sheikh Guruntum

Masu aikata Zina ku tuba kamin Lokaci ya kure muku, Idan ka tuba ka ci banza, Allah ya yafe>>Sheikh Guruntum

Duk Labarai
Babban Malamin addinin Islama Sheikh Yusuf Guruntum ya jawo hankalin masu laifi musamman Mazinata da su tuba kamin lokaci ya kure musu. Malam ya bayyana hakane a wajan wa'azin da yake na watan Ramadana inda yace idan ka yi laifi to zaga ka ba daidai ba saidai fa idan ka Tuba. Malam ya bayar da misali da mazinata yace su tuba su daina, idan ba haka ba kuwa suka bari lokaci ya kure musu, zasu hadu da fushin Allah.
Gwamnatin jihar kebbi ta rage awanni aiki ga ma’aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana

Gwamnatin jihar kebbi ta rage awanni aiki ga ma’aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya amince da dokar rage awannin aiki ga ma'aikatan jihar saboda Azumin watan Ramadana. Hakan na kunshene a cikin sanarwar da Kwamishinan haraji na jihar, Awwal Dogondaji ya fitar ga manema labarai ranar Litinin a babban birnin jihar, Birnin Kebbi. Yace sabuwar dokar lokacib aiki shine, daga ranar Litinin zuwa alhamis, za'a rika yin aikine daga karfe 8 zuwa karfe 1 na rana. Sannan ranar Juma'a kuma za'a rika yin aikinne daga karfe 8 zuwa karfe 12 na rana. Yace za'a koma a ci gaba da yin aiki kamar yanda aka saba bayan watan Ramadana. Ya jawo hankalin mutanen jihar da su dukufa da yiwa jihar dama Najeriya baki daya addu'ar zaman lafiya da ci gaba.
Yanzu da wata kungiyar Addinin Musulunci zata ce bata yadda da bada hutun Kirsimeti ba da ya zaka ji? Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda yace bai kamata kungiyar Kiristoci ta CAN ta soki hutun da jihohin Arewa suka bayar a makarantu ba saboda watan Ramadana

Yanzu da wata kungiyar Addinin Musulunci zata ce bata yadda da bada hutun Kirsimeti ba da ya zaka ji? Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda yace bai kamata kungiyar Kiristoci ta CAN ta soki hutun da jihohin Arewa suka bayar a makarantu ba saboda watan Ramadana

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya mayar da martani kan sukar da kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi ga jihohin Arewa da suka bayar da hutun makarantu saboda zuwan Azumin watan Ramadana. Jihohin da suka bayar da hutun sune, Kano, Katsina, Kebbi da Bauchi, Ita dai kungiyar CAN tace idan ba'a janye wannan hutu ba zasu shiga kotu da wadannan jihohi saboda ba musulmai bane kadai a wadannan jihohi ba. A martaninsa, Malam Bashir yace bai so yayi magana akan lamarin ba amma...