Thursday, January 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Duk Labarai
Najeriya ta aika da wakilai na musamman zuwa kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za'a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu C-130. Wadanda aka aika din daga ma'aikatar harkokin kasashen waje ne da kuma ma'aikatar tsaro ta kasa. Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya jagoranci tawagar. Zasu tattauna maganar sasanci tsakanin kasashen biyu da kuma inganta tsaro.
Kalli Hoto: Nuna wayar ta ta iPhone 17 Pro Max ta jawowa kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom cece-kuce inda da yawa ke cewa Albashinta bai isa ya saya mata wayar ba

Kalli Hoto: Nuna wayar ta ta iPhone 17 Pro Max ta jawowa kakakin ‘yansandan jihar Akwa-Ibom cece-kuce inda da yawa ke cewa Albashinta bai isa ya saya mata wayar ba

Duk Labarai
Kakakin 'yansandan jihar Akwa-Ibom, Timfon John ta dauki hankula bayan da aka ganta rike da wayar iPhone 17 Pro max ta Naira Miliyan 2.5 a yayin da Albashinta bai wuce Naira 300,000 ba. Da yawa dai sun rika caccakar ta da cewa ina ta samo wayar dan Albashinta dai ba zai iya saya mata wayarba. https://twitter.com/officerTimzy/status/2000986882457371048?t=jgvbDoV1hReDR0MGGKKa_g&s=19 Saidai kakin 'yansandan jihar Delta, Bright Edafe ya kare abokiyar aikin nasa inda yace watakila ta tara kudinne ta siya. Yace akwai wanda da gaske suna satar amma an zuba musu ido. https://twitter.com/Brightgoldenboy/status/2001283075662025113?t=g01jqwU9KgVSOJXaRylpsw&s=19
Tauraron Dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya kwallo

Tauraron Dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya kwallo

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya wasa bayan shekaru 15 da ya shafe yana buga wasa. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta. Ahmed Musa ya bugawa Najeriya wasanni 111 inda kuma shine wanda yafi kowane dan wasa yawan kwallaye a gasar cin kofin Duniya a Najeriya. https://twitter.com/Ahmedmusa718/status/2001265044110135753?t=lKaDFBWYJpufeS7G-QIDjQ&s=19
Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abinda ya faru a masallacin Hotoro Kano, ya sake faruwa a Arewa

Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abinda ya faru a masallacin Hotoro Kano, ya sake faruwa a Arewa

Duk Labarai
A yayin da ake tsaka da alhinin abinda ya faru a Masallacin dake Hotoro Kano inda wani yawa Ladani yankan Rago ya ciro Makogoronsa. A jihar Bauchi kuma wani gidane aka kama ma matsafa dake daukar 'yan mata suna zuwa suna tsafi dasu. Saidai dubunsu ya cika. https://www.tiktok.com/@usmaniyya61/video/7584529260925259029?_t=ZS-92Ik6NRW9hZ&_r=1 Hakanan a Kanon dai a shekar Mai Daki an samu wasu marasa Imani sun shiga har gida suka qàshè wata mata da danta, sannan suka Qònà Gawarsu. https://www.tiktok.com/@shataaliyu/video/7584775592344718613?_t=ZS-92IkYNI269Q&_r=1 Sai a Legas kuma da Wani Uba ya Hallaqa dansa har lahira wanda shima dan Arewa ne. https://www.tiktok.com/@danhajia_ojo/video/7584599644395556117?_t=ZS-92Il0bOAmPZ&_r=1
Kalli Bidiyon Sarkin Mota cikin shigar Father Christmas irin ta Kiristoci data jawo cece-kuce

Kalli Bidiyon Sarkin Mota cikin shigar Father Christmas irin ta Kiristoci data jawo cece-kuce

Duk Labarai
Tauraron me sayar da mota wanda aka fi sani da Sarkin Mota ya jawo cece-kuce bayan da aka ganshi sanye da kaya irin na Koristoci wanda ake kira da Father Christmas. Da yawa dai sun ce hakan bai dace ba a matsayinsa na musulmi koyi da Kirista ne. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/SarkinMota_AMF/status/2000990370394726771?t=6KcVmSIbHHqXtc6p1yMKHA&s=19 https://www.tiktok.com/@alamin_sarkinmota/video/7584584292257303829?_t=ZS-92IiunAYfjM&_r=1
Karya kuke babu yunwa a Arewa, Gwamnatin tarayya ta gayawa jaridar Daily Trust

Karya kuke babu yunwa a Arewa, Gwamnatin tarayya ta gayawa jaridar Daily Trust

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta karyata wani rahoton jaridar Daily Trust wanda yace akwai yunwa a Arewa inda suka ce mutane miliyan 33 na fama da yunwa ciki akwai miliyan 16 wadanda kananan yara ne A wata sanarwa da ta samu sa hannun me magana da yawin shugaban kasa tace Gwamnatin ta rabawa gidaje Miliyan 3 tallafin Naira 75,000 kowannensu. Sannan kuma akwai dalibai 396,000 da suka samu tallafin karatu. Sannan akwai kananan masana'antu da suka samu tallafin jari. Fadar shugaban kasar tace tana maraba da suka me ma'ana amma a rika fadar kokarin gwamnati.
Idan Saurayinki ya miki alkawarin zai aureki amma daga baya ya ki aurenki ko ya auri wata, zaki iya kaishi kara kotu>>Inji Lauya Emmanuella

Idan Saurayinki ya miki alkawarin zai aureki amma daga baya ya ki aurenki ko ya auri wata, zaki iya kaishi kara kotu>>Inji Lauya Emmanuella

Duk Labarai
Lauya Emmanuella Ojialor ta bayyana cewa mata zasu iya kai duk namijin da ya musu Alkawarin aure amma daga baya yaki aurensu kotu. Ta bayyana cewa, doka ta bayar da dama muddin mace na da hujja ko shaidu ta kai kara ta nemi a biyata diyya. Ta yi gargadi ga mata masu daukar doka a hannu ta hanyar aikata abubuwan da basu dace ba.
Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai

Da Duminsa: Dangote ta hannun gidan man fetur din MRS ya rage farashin man fetur zuwa Naira 739 a Legas kadai

Duk Labarai
Rahotanni daga Legas na cewa, Dangote ya rage farashin Man fetur inda gidan man MRS ya fara sayar da man akan Naira 739 akan kowace lita. An ga masu motoci na ta layin shiga gidaje man MRS a Legas dan sayen man me sauki. Hakan na zuwane bayan da Dangote ya rage farashin da yake sayarwa gidajen man fetur zuwa Naira 699 akan kowace lita. Dangote dai yasha Alwashin wannan ragi zai kai kowane sashi na Najeriya inda yace za'a rika sayen man aka Naira 740 akan kowace lita. Ya zargi 'yan kasuwar man fetur da ke shigo da man daga kasashen waje da kara masa kudi da gangan dan su ci kazamar riba. https://twitter.com/Imranmuhdz/status/2001239798380683416?t=-LTXiIhd9krAX3VvMMmQtw&s=19
Naso in samar wa da jihata wutar Lantarki da bata daukewa amma shugaban kasa ya hanani>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Victor Atah

Naso in samar wa da jihata wutar Lantarki da bata daukewa amma shugaban kasa ya hanani>>Inji Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Victor Atah

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Obong Victor Attah ya bayana cewa, ya so samarwa da mutanen jiharsa Wutar Lantarki da bata daukewa amma Shugaban kasa ya hanashi. Yace a wancan lokacin ya gina tashar samar da wutar lantarkin kuma har shugaban kasa ya je ya kaddamar da ita. Yace amma da shugaban kasa ya koma Abuja sai yayi sabuwar doka cewa jihohi ba zasu iya samar da wuta kuma su rarrabata ba. Yace a haka aikin ya lalace. https://twitter.com/NigeriaStories/status/2001195784100860330?t=y07yNhYPgverUhw3rthwOQ&s=19