Thursday, February 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari’ar musulunci a jihohinsu ba

Yarbawa sunce basu yadda da kotunan shari’ar musulunci a jihohinsu ba

Duk Labarai
Kungiyoyin dake fafutukar kafa kasar Yarbawa sun bayyana rashin amincewa da bullar kotunan shari'ar Musulunci a jihohinsu. Jihar Ekiti itace ta baya-bayannan da aka samu bullar kotun shari'ar Musulunci wadda har alkalai 3 Imam Abdullahi Abdul-Mutolib, Imam Abdulraheem Junaid-Bamigbola da Dr. Ibrahim Aminullahi-Ogunrinde sun yi zama sun saurari shari'ar rikicin aure guda biyu. Kamin nan a jihohin Lagos, Ogun, Oyo and Osun ma an samu ,aman kotun shari'ar Musuluncin. Zuwa yanzu, Jihar Ondo ce kadai bata da kotun shari'ar Musulunci a cikinta, hakanan itama Gwamnatin jihar Ekiti ta musanta cewa akwai kotun shari'ar musulunci a cikinta. Tuni dai aka samu wani Fasto me suna Pastor Oluwafemi J. Edafemi, ya jagoranci gamayyar wasu masu ruwa da tsaki a yankin na Yarbawa inda suka yi gang...
Duk da tallafin Gwamnatin tarayya, Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen yayi tashin gwauron zabi

Duk da tallafin Gwamnatin tarayya, Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen yayi tashin gwauron zabi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, duk da tallafin da gwammatin tarayya ta bayar a fannin shigo da kayan abinci daga kasashen waje, farashin kayan abincin yayi tashin gwauron zabi. Rahoton yace Farashin kayan abincin da ake shigowa dasu daga kasashen waje ya tashi da kaso 37.65 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta sanar. An fitar da wadannan alkalumane a tsakanin watannin Disamba zuwa Najairu. Hakanan rahoton yace duk bayan wata, farashin kayan abincin yana kara tashi da karuwa.
Bidiyo:Kalli yanda matar aure ta baiwa saurayi lambar wayarta

Bidiyo:Kalli yanda matar aure ta baiwa saurayi lambar wayarta

Duk Labarai
Wata matar aure wadda 'yarsanda ce ta jawo cece-kuce bayan da ta baiwa Saurayi lambar wayarta. Matar wadda sunanta Chioma an ganta a cikin wani faifan bidiyon dake ta jawo a kafafen sada zumunta inda Saurayin ya kirata gefen titi. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1883120117271413123 Ya tambayeta, tana da aure ta amsa mai cewa Eh tana da aure inda yace yana sonta sannan ya karbi lambarta. Da yawa dai sun yi Allah wadai da wanda ya dauketa bidiyon sannan wasu sun yi Allah wadai da saurayin da be kyaleta ba tunda tace ita matar aure ce.
Gwamnatin tarayya tace za’a rika koyar da sana’o’in Gyaran fanfo, Aski, Gyaran waya, kwalliyar mata da sauransu a makarantun b0k0

Gwamnatin tarayya tace za’a rika koyar da sana’o’in Gyaran fanfo, Aski, Gyaran waya, kwalliyar mata da sauransu a makarantun b0k0

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya tace an saka sana'o'in Aski, Gyaran waya, gyaran fanfo, kwalliyar mata, Gyaran waya da sauransu cikin abubuwan da za'a rika koyarwa a makarantun boko. Za'a rika koyar da wadannan sana'o'i ne a makarantun firamare zuwa makarantun karamar sakandare. Wannan ya biyo bayan garambawul da akawa bangaren ilimi. Hukumar wayar da kai ta kasa, NOA ta ce an saka wadannan sana'o'i cikin karatu ne dan koyawa dalibai hanyar dogaro da kai. Sauran sana'o'in da za'a rika koyarwa sun hada da noma, kiwon kaji, gini, saka tayil, saka POP, da dai sauransu.
Buhari ya koma Najeriya bayan gabatar da shaida a kotun Paris

Buhari ya koma Najeriya bayan gabatar da shaida a kotun Paris

Duk Labarai
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya koma kasar bayan gurfana a gaban wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa. Cikin wani bidiyo da tsohon mataimakinsa na musamman kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna lokacin da tsohon shugaban kasar ke sauka daga jirgi a jihar Katsina. A farkon makon nan ne tsoffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari suka bayyana a gaban wata kotun cinikayya ta ƙasa da ƙasa da ke birnin Paris na a ƙasar Faransa domin ba da bahasi dangane da kwangilar aikin gina cibiyar samar da wutar lantarki ta Mambilla da ke jihar Taraba. Wani kamfani mai suna Sunrise Power ne dai ya kai gwamnatin Najeriya ƙara kan saɓa ƙa'idojin kwangilar, inda yake neman gwamnatin ta biya shi dalar Amurka biliyan...
Tsaffin Janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya>>Oshiomhole

Tsaffin Janarorin soja ne ke satar ma’adanai a Najeriya>>Oshiomhole

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa, tsaffin janarorin soja ne ke satar ma'adanai a Najeriya. Oshiomhole ya bayyana hakane a yayin da shugaban kwamitin dake kula da harkar hakar ma'adanai a majalisar,Sampson Ekong ke muka sakamakon binciken kwamitinsa ga majalisar. Oshiomhole wanda shine shugaban kwamitin dake kula da harkokin cikin gida ya bayyana cewa, sun san wadannan tsaffin janarorin dan kuwa koda a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sai da ya rubuta mai wasika akan ayyukan nasu. Ya kara da cewa, wadannan masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba suna safarar muhgan makamai dan gudanar da ayyukansu kamar yanda ake yi a sudan ta kudu. Oshiomhole ya bayar da shawarar cewa, maganin wannan matsala shine a samar da rundunar jami'an tsar...
Bello Turji Ya Ce A Shirye Yake Ya Mika wuya – CDS

Bello Turji Ya Ce A Shirye Yake Ya Mika wuya – CDS

Duk Labarai
Duk da rahotannin da Turji ya bayar na mika wuya, babban hafsan tsaron ya ci gaba da cewa duk wanda ya aikata kisan kiyashi ba dole ba ne a tsira. Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa a ranar Juma’a ya bayyana cewa fitaccen Jagoran ‘yan ta’adda Bello Turji ya bayyana cewa a shirye yake ya mika wuya. Yayin da yake shugabanta na biyu da kuma wasu hafsoshin sojin kasar kwanan nan da sojoji suka kama, babban hafsan hafsoshin tsaron kasar ya ce an tilastawa Turji watsi da mafi yawan wadanda ke karkashinsa, wanda hakan ke nuna a shirye ya ke ya ajiye makamansa. “Su (’yan ta’adda) suna cikin al’umma; mutane sun san su. Don haka, wani lokacin idan sun gan su, kafin ka sami bayanin, kamar sa'o'i biyu ne - mutumin ya motsa. Don haka, lokacin da bayanin ya isa gare ...
Hukumar EFCC na tsaka mai wuya inda aka samu jami’anta da sace kudade da kadarorin da aka kwato daga ma’aikatan Gwamnati

Hukumar EFCC na tsaka mai wuya inda aka samu jami’anta da sace kudade da kadarorin da aka kwato daga ma’aikatan Gwamnati

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC na fama da matsalar jami'anta da ake kamawa da satar kudade da kadarori da aka kwato daga hannun jami'an gwamnati da masu rashawa da cin hanci. Wasu daga cikin jami'an hukumar an koresu daga aiki inda wasu kuma aka dakatar dasu dan yin bincike kan zargin satar kayan da aka basu kula wa dasu. Koda a shekarar data gabata, mutane 27 ne aka kora daga EFCC saboda satar kudaden da aka basu ajiya Hakanan kakakin EFCC a ranar 6 ga watan Janairu 2025 ya tabbatar da cewa suna binciken batan dala $400,000 da ake zargin wani jami'in hukumar ya sace. Hakanan akwai jami'an hukumar 10 da aka dakatar a reshenta na jihar Lagos inda ake zarginsu da satar Gwal da darajarsa ya kai na Naira Biliyan 1, da kudade dala $350,000 zuwa $400,00 wanda duka suka...
Kaso 77 na matan Najeriya na Amfani da man kara hasken fata>>Inji WHO

Kaso 77 na matan Najeriya na Amfani da man kara hasken fata>>Inji WHO

Duk Labarai
Kungiyar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cewa, kaso 77 cikin 100 na matan Najeriya na amfani da man kara hasken fata wanda ake cewa Bleaching. Hakan bmna zuwane yayin da wani rahoto yace ba matan ba kadai yanzu hadda kananan yara a Najeriya ana shafa musu man kara hasken fata. Rahoton na WHO yace mayukan kara hasken fata ne mafiya ci gaba da aka fi sayarwa a tsakanin mayukan shafawa a Duniya baki daya. Hakan na faruwa ne duk da irin illar da irin wadannan mayukan shafawar ke dauke da ita wanda ya hada da ragewa fata karfi da garkuwar da take dashi da kuma kara hadarin kamuwa da cutar daji.