Monday, March 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya hana ‘yansandan rike Bìndìgà idan suna sanye da kayan gida

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya hana ‘yansandan rike Bìndìgà idan suna sanye da kayan gida

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin cewa, daga yanzu kar dansandan daya sake rike Bindiga indai yana sanye da kayan gida. Ya kuma gargadi 'yansandan su kiyaye kada su rika take hakkin dan Adam dan kuwa aikinsu shine kare hakkokin al'umma. Ya bayyana hakane a yayin wani taro da aka yi a jiya inda yace ya samu korafe-korafe da yawa game da take hakkokin al'umma da wasu 'yansandan ke yi. Sannan Shugaban 'yansandan yace duk wanda aka kama da karya wadannan dokoki zai dandana kudarsa. Ya bukaci 'yansandan su gudanar da aikinsu bisa doka dan kare mutuncin hukumar ta 'yansanda.
Kalli Sojar Najeriya data kirkiro Jirgin saman yaki na farko

Kalli Sojar Najeriya data kirkiro Jirgin saman yaki na farko

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun samu nasara babba inda suka hada jirgin yaki na farko kuma wadda ta kerashi sojar sama ce me suna Lieutenant Nkemdilim Anulika Ofodile. Sojar dai ta yi karatu kimiyyar sararin samaniyane kuma an sajawa jirgin saman yakin data kirkiro sunan Tsaigumi Tactical UAV. Wannan nasara ba karamin abin ci gaba bane a hukumar sojojin Najariya dama Najeriya baki daya.
Ina shan Tabar wìwì ta Naira Miliyan 2 kullun>>Inji Mawakin Najeriya, Odumodublvck

Ina shan Tabar wìwì ta Naira Miliyan 2 kullun>>Inji Mawakin Najeriya, Odumodublvck

Duk Labarai
Shahararren mawakin Gambara dan Najeriya me suna Tochukwu Gbubemi Ojogwu wanda aka fi sani da Odumodublvck ya bayyana cewa, a kullun yana shan tabar wiwi ta Naira Miliyan 2 wanda hakan na nufin a sati yana shan ta naira Naira miki 14 kenan. Ya bayyana hakane a yayin da shahararren me wasan barkwanci, Carter Efe ke hira dashi. Wannan bayani nashi ya baiwa mutane mamaki matuka. Mawakin dai ya kara da cewa, matsin rayuwar da ake fama da uta a Najeriya ko a jikinsa.
Babu shugaban da zai cimma nasara ba tare da rufe ido da murza gashin baki ba>>Obasanjo

Babu shugaban da zai cimma nasara ba tare da rufe ido da murza gashin baki ba>>Obasanjo

Duk Labarai
,Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a bayyana cewa, babu shugaban da zai cimma Nasara ba tare da rufe ido da murza gashin baki ba da yin abinda ya dace. Ya bayyana hakane a yayin da sabon shugaban ma'aikatar lafiya ta tarayya dake Idi-Aba, Abeokuta, Dr. Dayo Israel ya kai masa ziyara. Tsohon shugaban kasar ya bayar da misali da kansa inda yace ya taba ya taba korar diyarsa daga aiki a gonarsa sabod ta je aiki a makare. Ya jaddada cewa muddin shugaba na son cimma nasara sai ya fuskanci kalubalen dake gabansa da gaske.
Ban damu ba dan an koreni daga aiki ba, har yanzu ina nan kan bakana, Binani ce ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa>>Inji Tsohon Kwamishinan Zabe, Barr Hudu Ari

Ban damu ba dan an koreni daga aiki ba, har yanzu ina nan kan bakana, Binani ce ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa>>Inji Tsohon Kwamishinan Zabe, Barr Hudu Ari

Duk Labarai
Tsohon Kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Barr Hudu Ari ya bayyana cewa bai damu ba dan an koreshi daga aiki ba saboda shi yasan cewa, A'isha Dahiru Binani ce ta lashe zaben Gwamnan jihar Adamawa. Hakan na zuwane kasa da mako daya bayan da majalisar tarayya ta amince da korarsa daga aiki. Tuni dai dama aka dakatar dashi saboda bayyana cewa Binani ce taci zabe a yayin da ake kan tattara sakamakon zaben. Saidai har yanzu, Ari ya bayyana cewa yana da takardu da hujjoji dake tabbatar da cewa A'isha Binani ce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, ba Gwamna me ci Ahmad Fintiri ba. Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a gidansa dake Bauchi inda har sai da ya rantse da Qur'ani. Yace an matsa masa sai ya bayyana gwamna Ahmad Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben kuma...
Ni ‘yan uwana ba ‘yan gargajiya bane kuma ni gyaran tarbiyya nake>>Martanin GFresh Al-amin ga wanda kw cewa shima ‘yan uwansa su zaneshi

Ni ‘yan uwana ba ‘yan gargajiya bane kuma ni gyaran tarbiyya nake>>Martanin GFresh Al-amin ga wanda kw cewa shima ‘yan uwansa su zaneshi

Duk Labarai
Tauraron TikTok, G-Fresh Al-amin ya mayar da martani kan masu cewa, shima 'yan uwansa su taru su dakeshi kamar yanda akawa Yahya Y America. G-Fresh yace shi 'yan uwansa ba 'yan gargajiya bane kuma ahi ba bata tarbiyya yake ba, Gyaran Tarbiyya yake. Yace kuma ya hada aure kusan 4 kuma babu wanda ya biyashi, Allah ne ya biyashi. Yace a lokacin da suke gwagwarmaya babu wanda ya damu dasu sai da suka samu daukaka ne ake neman a rika saka baki a rayuwarsu. Kalli Bidiyon nasa a nan
Sojojin mu sun yi kadan, Muna bukatar sojoji Dubu dari biyar kamin mu iya magance matsalar tsaro a Najeriya>>Janar Din soja ya koka

Sojojin mu sun yi kadan, Muna bukatar sojoji Dubu dari biyar kamin mu iya magance matsalar tsaro a Najeriya>>Janar Din soja ya koka

Duk Labarai
Janar din soja, Maj-Gen Pat Akem-Vingir (retd), ya bayyana cewa, ana bukatar karin sojoji a Najeriya muddin ana son sojojin su iya magance matsalar tsaron da ake da ita. Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na ChannelsTV suka yi dashi inda yace a yanzu sojoji 230,000 ne Najeriya ke dasu. Yace yawanci nasarorin da suka samu a Arewa Maso gabas akan B0K0 Hàràm an samu koma baya saboda kungiyar ta sake komawa ta kwace guraren da aka kwace daga gurinta. Yace dan haka akwai bukatar kara yawan sojojin da ake dasu zuwa 500,000 idan ana son dawwamar da nasarar tsaro da ake samu. Tsohon Janar din yace kuma Gwamnati ta daina kula sabuwar kungiyar masu tada kayar baya ta Lakurawa inda yace karamar kungiyace wadda za'a iya yin maganinta a lokaci guda, yace bai kamata ana maganarsu b...
Hotuna: Dansandan Najeriya me mukamin ASP ya kkashe kansa a jihar Naija

Hotuna: Dansandan Najeriya me mukamin ASP ya kkashe kansa a jihar Naija

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, dansandan Najeriya me mukamin ASP ya kashe kansa a jihar Naija. Dansandan me suna shafi'u Bawa na tare da runduna ta 61 ce dake Kontagora a jihar Naija kuma wata majiya ta bayyanawa jaridar Daily Trust cewa ya kashe kansa ne ranar Asabar da yamma. An tarar gawarsa na reto ne a dakinsa da ya sagale kansa a jikin silin. Rahotanni sunce mahaifinsa, Mallam Usman Bawa ne ya fara kai rahoton mutuwar dan nasa a ofishin 'yansanda dake Kontagora. Kakakin 'yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an baiwa danginsa gawar inda kuma aka fara bincike akan lamarin.
Ko da dalibi ya ci jarabawar JAMB ba tabbacin zai samu admission a jami’a>>Inji Hukumar JAMB

Ko da dalibi ya ci jarabawar JAMB ba tabbacin zai samu admission a jami’a>>Inji Hukumar JAMB

Duk Labarai
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a ta JAMB ta bayyana cewa, ko da dalibi ya ci jarabawar ta JAMB to ba lallai ya sami damar shiga jami'a ba. Me magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu inda yace samun damar shiga jami'a na bukatar mutum ya samu sakamako na kammala sakandare me kyau da JAMB din da kuma Post UTME. JAMB ta bayar da wannan amsa ne bayan da iyaye ke ta korafin cewa 'ya'yansu na rubuta jarabawar JAMB kuma suna ci amma ba'a basu damar shiga jami'a. Ya kawo misalin wasu iyaye da suka yi korafin an hana 'ya'yansu shiga jami'a a jihohin Filato da Cross River amma yace daga baya da aka musu bayani sai suka gane cewa 'ya'yan nasu ne basu cancanci shiga jami'ar ba. Ya kuma jawo hankalin iyaye dasu fahimci tsarin baya...
Ya kamata a rage zagin da ake min a rika godemin domin gaba dayan kudaden da aka samu daga cire tallafin Man fetur na rabar dasu ga ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

Ya kamata a rage zagin da ake min a rika godemin domin gaba dayan kudaden da aka samu daga cire tallafin Man fetur na rabar dasu ga ‘yan Najeriya>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su rage sukar da suke masa maimakon hakan, su rika gode masa. Shugaban ya bayyana hakane ta bakin me bashi shawara ta musamman akan mazabu, Khadija Omotayo inda ta wakilceshi a Birnin Jos na jihar Filato wajan taron karawa juna sani da ya gudana a ranar Asabar. Khadija tace, shugaban kasar ya cire tallafin man fetur ne dan amfanin kowa, domin kuwa kudaden da aka samu daga cire tallafin man fetur din an rabasu ga kowace jiha ta hannun gwamnoni. Tace shugaban kasar ya kuma karawa ma'aikata Albashi sannan yace zai kara yin wani karin, tace gashi ya turata ta wakilceshi a taron a jihar da Jam'iyyar PDP ke shugabanci wanda hakan na nuna bashi nuna wariya kowa nashine, tace dan haka shugaban ya cancanci yabo. Khadija ta kuma ba...