Wednesday, February 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Amarya ta zuba Gguba a Abincin walimar aurenta a jihar Jigawa, Mutum daya ya mutu, Ango ya kwanta rashin lafiya

Amarya ta zuba Gguba a Abincin walimar aurenta a jihar Jigawa, Mutum daya ya mutu, Ango ya kwanta rashin lafiya

Duk Labarai
Wata amarya a jihar Jigawa ta zubawa abincin walimar bikinta guba. Dalilin hakan Ango ya kwanta rashin lafiya inda kuma mutum daya daga cikin mahalarta bikin ya mutu. Lamarin ya farune a karamar Hukumar Jahun dake jihar. Kakakin 'yansandan jihar, Shi’isu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna kan bincike. Yace sun kama amaryar da wata kuma suna bincike akansu.
Wani Dan Crypto Ya Je Bompai Neman Auren Shamsiya

Wani Dan Crypto Ya Je Bompai Neman Auren Shamsiya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan Crypto mai suna Dogo Yaro Yola, ya ce ya kamu da sun shaharariyar barauniyar nan Shamsiya, inda yayi tattaku har wajen 'yan sanda a Bompai, yq nemi a sakan masa ita domin ya aure ta. Ya ce, "Wallahi Ina Son Shamsiyya Da Aure, Don Haka Ina Rokon Abdullahi Kiyawa Da Ya Sako Min Ita, Inji Dogo Yaro Yola Crypto.
Yahaya Bello ya buƙaci ƴan Nijeriya da su taimaka wa Tinubu da addu’a

Yahaya Bello ya buƙaci ƴan Nijeriya da su taimaka wa Tinubu da addu’a

Duk Labarai
Yahaya Bello ya buƙaci ƴan Nijeriya da su taimaka wa Tinubu da addu'a Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya roki ƴan Najeriya da su yi hakuri da shugaban kasa Bola Tinubu, tare da tallafa masa da addu’o’i domin samun nasara a kan manufofinsa na gyaran tattalin arzikin ƙasa. Bello ya yi wannan jawabi ne a jiya Talata a fadar Ohinoyi na Ebiraland da ke Okene, inda ita ce fitar shi ta farko a bainar jama’a tun bayan da ya samu ’yancinsa daga gidan yari, inda bayan da koru ta bayar da belinsa a gaban kotu bisa tuhumarsa da laifin karkatar nlda N110bn. Tsohon gwamnan wanda ya samu tarba daga dimbin magoya bayansa a yankin Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, ya yi kira da bukatar hadin kai da hakuri da shugaban ƙasa. Bello, wanda ke tare da magajinsa, Gwamna Usman Ododo, y...
Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba, Wayau Tinubun ya mai shiyasa ya samu nasara>>Inji Tsohon Hadiminsa

Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba, Wayau Tinubun ya mai shiyasa ya samu nasara>>Inji Tsohon Hadiminsa

Duk Labarai
Tsohon hadimin Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari me suna Babafemi Ojudu da yayi aikin bada shawara akan harkar siyasa a ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Buhari bai so Osinbajo ko Tinubu su zama shugaban Najeriya ba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a wani gidan rediyo na yanar gizo me suna Edmund Obilo’s State Affairs. Ya kuma ce zagayen neman delegates kadai bai isa ba su ci zabe inda yace kamata yayi ace shugaba Buhari ya baiwa hadimansa baki kan su taimakaw Osinbajo amma yaki. Yace koda Tinubu ma yawa Buharin wayaune shiyasa ya samu nasara.
Kamfanonin Sadarwa, MTN, Airtel da saransu sun mikawa gwamnati bukatar kara farashin katin waya dana data, suna son nunka kudin da suke caji

Kamfanonin Sadarwa, MTN, Airtel da saransu sun mikawa gwamnati bukatar kara farashin katin waya dana data, suna son nunka kudin da suke caji

Duk Labarai
Kungiyar kamfanonin sadarwa sun nemi gwamnati ta basu dama su nunka kudin kati dana data. Wakilin kamfanin MTN, Karl Toriola ne ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise TV yayi dashi. Saidai ya bayyana cewa da wuya, musamman saboda halin matsi da mutane ke ciki Gwamnati ta amince da bukatar tasu. Yace amma karin ya zama dolene saboda la'akari da kudin da suke kashewa wajan yin aiki da hauhawar farashin kayan masarufi da kuma karuwar yawan mutanen dake amfani da waya.
Bidiyo: Yanda Dogarin Shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi a bainar jama’a

Bidiyo: Yanda Dogarin Shugaban kasa ya yanke jiki ya fadi a bainar jama’a

Duk Labarai
Dogarin shugaban kasar Ghana, Colonel Isaac Amponsah ya yanke jiki ya fadi a yayin da shugaban kasar kewa majalisar kasar jawabi. Lamarin ya farune ranar January 3, 2025 inda nan da nan mutane suka kaiwa dogarin dauki, bayan bashi kulawar gaggawa, an kuma garzaya dashi zuwa Asibiti. Shugaban kasar Ghanan, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya dakatar da jawabin nasa inda ya juya dan tabbatar da hadimin nasa ya samu kulawa, kamin daga baya ya juya ya ci gaba da yin jawabin.
NNPCL ya fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

NNPCL ya fara gyaran matatar man fetur ta Kaduna

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya bayyana cewa suna kan aikin gyaran matatar man Kaduna data Fatakwal. Yace za'a yiwa matatan man fetur din aikin da zasu sama aun zo daidai da takwarorinsu na sauran kasashen Duniya ne. Ya kuma bayyana cewa matatun man fetur na Fatakwal da Warri da aka kammala an kammalasu ne bayan yi musu gyaran da zasu yi gogayya da sauran na kasashen Duniya. Shugaban bangaren yada labarai na kamfanin ne ya bayyana hakan.