Wednesday, February 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Najeriya ta ware biliyan 60 na ciyar da ƴan firamare a 2025

Najeriya ta ware biliyan 60 na ciyar da ƴan firamare a 2025

Duk Labarai
Gwamnatin Najeriya ta ware naira biliyan 60 domin ciyar da 'yan makarantar firamare a sassa daban-daban na kasar a cikin kasafin kudin 2025. Za ai aikin ne karkashin shirin gwamnati na farfado da tattalin arziki wato Economic Recovery Growth Plan (ERGP). Jaraidar Dailty Trust ta tawaito cewa, kafin a sauya ministan ilimin kasar ya fara sanar da hakan wanda dama shirin ciyar da daliban yake karkashin ma'aikatarsa, kafin daga bisani a mayar da shi karkashin ofishin shugaban kasa. An ware wa ma'aikatar ilimi kudi naira biliyan 348, cikin sama da naira tiriliyan 2. 517, wanda hakan na daga cikin fannin da ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin kudin, duk da bai kai adadin da Bankin Duniya ya bayar da shawara na kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na kasafin kudin ba. Har wa yau, ma'aikatar il...
An kuɓutar da wani yaro bayan kwana biyar tare da zakuna da giwaye

An kuɓutar da wani yaro bayan kwana biyar tare da zakuna da giwaye

Duk Labarai
An kuɓutar da wani yaro ɗan shekara takwas, bayan shafe kwana biyar a gandun dajin zakuna da giwaye a arewacin ƙasar Zimbabwe. Lamarin ya faru ne a lokacin da yaron mai suna Tinotenda Pudu ya yi ta gararamba a cikin gandun daji Matusadona Game Park, kamar yadda ɗan majalisar gabashin yankin Mashonaland, mai suna Mutsa Murombedzi ya kuma wallafa a shafinsa na X. Kwanan sa biyar a dajin yana bacci kan duwatsu, ga kuma gurnanin zakuna da wucewar giwaye, babu abin da ya ke ci sai 'ya'yan itatuwa. Gandun dajin Matusadona dai na ɗauke da zakuna 40, akwai lokacin da ya kasance wuri mafi yawan zakuna a Afirka, kamar yadda bayanan African Parks suka bayyana.
Ɗansanda ya sha barasa ya saki mutum 13 da ke tsare

Ɗansanda ya sha barasa ya saki mutum 13 da ke tsare

Duk Labarai
Wani jami'in ɗansanda da ya yi mankas da barasa a Zambiya ya saki wasu mutum 13 da ke tsare a ofishin 'yansanda domin su je su yi shagalin murnar sabuwar shekara. Jami'ai sun ce an kama sufeto Titus Phiri bayan sakin mutanen da ake tsare da su a wani ofishin 'yansanda a Lusaka, babban birnin ƙasar. Mutane 13 da ya saki, ana zarginsu da aikata manyan laifuka da suka haɗa da kisan kai da fashi. Yanzu haka mutanen sun tsere, kuma tuni aka ƙaddamar da farautarsu.
‘Yansandan Kano sun kama matashiyar da ake zargi da satar wayoyi

‘Yansandan Kano sun kama matashiyar da ake zargi da satar wayoyi

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan jihar Kano ta yi holen wata matashiya mai suna Shamsiyya da ake zargi da ƙwarewa wajen satar wayoyi a unguwanni daban-daban a Kano. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Abudullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an kama Shamsiyya ne ranar 21 ga watan Disamba bayan shafe tsawon shekara guda ana farautar ta. ''Shamsiyya ta ƙware wajen ɓullo da dabarun yaudara daban-daban don hilatar mutane wajen sace musu wayoyi'', in ji sanarwar. Kiyawa ya ƙara da cewa wadda ake zargin kan yi aiki ne tare da wasu mutu huɗu da ke taimaka mata ciki har da ɗan adaidaita sahu da ƙwararre wajen cire wayoyi daga makulli, wajen gudanar da ayyukanta. ''Ƙwararriyar mai yaudara ce da ke shiga gidajen matan aure tare da sace musu wayoyinsu da kuma yin amfani da wayoyin wajen sace musu k...
‘Yanbindiga sun kai hari kasuwar Shinkafi tare da sace gomman mutane

‘Yanbindiga sun kai hari kasuwar Shinkafi tare da sace gomman mutane

Duk Labarai
Al’ummar garin shinkafin jihar Zamfara sun ce 'yanta’adda sun kai wani hari kasuwar garin inda suka tafi da gwammon mutane tare da jikkata wasu. Mazauna yankin sun ce 'yanbindigar sun kai harin ne ana tsaka da cin kasuwar Shinkafin da ranar yau Alhamis. Sai dai har kawo yanzu rundunar 'yansandan jihar ta Zamfara ba ta ce komai kan harin. Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da gawurtaccen ɗanbindingar nan da ke cin karensa babu babbaka a jihar Zamfara, Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al'umma. A makon da ya gabata ne dai sojoji suka kama wani makusancin ɗanbindigar al'amarin da ya ce ya fusata shi kuma zai ɗauki fansa.
Shan Giya ba haramun bane >>Inji malamin Kirista, Apostle Abel Damina

Shan Giya ba haramun bane >>Inji malamin Kirista, Apostle Abel Damina

Duk Labarai
Babban malamin Kirista, Apostle Abel Damina ya bayyana cewa Annabi Adamu (AS) da Hauwa (AS) basu ci komai a gidan Aljannah ba. Ya bayyana hakane a yayin da yake magana a cocinsa. Ya yi ta nanata cewa basu ci komi ba inda yace waye a wajan da zai iya bayar da labari? Hakanan ya kara da cewa, Shan giya da shan taba ba haramun bane mutum ne da kansa zaiwa kansa fada dan daina yinsu. Wadannan maganganu nashi sun jawo cece-kuce sosai inda da yawa suna tafi akan cewa baya kan daidai. Kalli bidiyon jawabin nasa anan
Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama’armu cikin talauci – Gwamnatin Kano

Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama’armu cikin talauci – Gwamnatin Kano

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hamayyarta ga ƙudirin dokar harajin da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin Najeriya wanda shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ne ya bayyana haka a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 a dandalin Ma'ahaha da ke birnin Kano. Wata sanarwa da ke ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ta ce gwamnan ya ce "wannan kundin dokar harajin ba za ta magance matsalar tattalin arziƙinmu ba. Kano tana hamayya da wannan ƙudiri da zai shafi walwalaw al'umma." Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tankiyya tsakaninta da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya soki kundin.
Kalli Kwalliyar Sabuwar Shekara ta Rahama Sadau

Kalli Kwalliyar Sabuwar Shekara ta Rahama Sadau

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata data sha kwalliyar Sabuwar shekara. Tawa masoyanta fatan Alheri.
Kungiyar Kwadago tace zata nemi karin mafi karancin Albashi a shekarar 2025 saboda tsadar rayuwa

Kungiyar Kwadago tace zata nemi karin mafi karancin Albashi a shekarar 2025 saboda tsadar rayuwa

Duk Labarai
Kungiyar kwadago tace zata nemi a kara mata yawan mafi karancin albashi daga dubu 70 zuwa sama a shekarar 2025. Kunguyar tace a kowace shekara ya kamata a rika lura da yanayin tsadar rayuwa dan karawa ma'aikata Albashi. Shugaban kungiyar kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana hakan inda yace me zai hana a rika la'akari da yanayin tsadar rayuwa kowace shekara dan karawa ma'aikata Albashi maimakon jira sai bayan shekara 5. Yace su da NLC sun fara tattaunawa kan maganar. A watan Yuli da ya gabata ne dai kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya suka cimma matsaya game da karin Albashi zuwa Naira dubu 70 maimakon Naira dubu 30 da ake biya a baya. Hakan na zuwane bayan shekaru 5 da yin karin farko.
An haramta jin wakokin Rarara a Jamhuriyar Nijar bayan da yawa shugaban kasar Barazana

An haramta jin wakokin Rarara a Jamhuriyar Nijar bayan da yawa shugaban kasar Barazana

Duk Labarai
Rahotannin da muke samu daga kasar Nijar na cewa hukumomi a kasar sun sanar da haramta jin wakokin mawakin siyasa Dauda Kahutu, Rarara. Hakan na zuwane bayan da Rarara yawa shugaban kasar Nijar Tchadi Barazanar ya dawo da Bazoum kan mulki ko kuma ya fara zubo masa wakoki. Rarara yace "Na bawa Tchani kwana 20 ya dawo da Bazoum ko ya sanya lokacin zabe, ko kuma na soma zubo masa wakoki ba kakkautawa" A sanarwar da kafar Damagaram Post ta ruwaito tace ne kawai an haramta jin wakokin Rarara din a Jamhuriyar Nijar amma basu bayar da cikakken bayani ba.