Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Addu’o’in mu ne yasa darajar Naira bata fadi aka rika sayar da dala daya akan Naira dubu 10,000 ba>>Inji Pasto Adebayo

Addu’o’in mu ne yasa darajar Naira bata fadi aka rika sayar da dala daya akan Naira dubu 10,000 ba>>Inji Pasto Adebayo

Duk Labarai
Babban Fasto na cocin (RCCG), Fasto Adebayo ya bayyana cewa addu'o'in da suke da taimakon Allah ne yasa darajar Naira bata fadi ba aka rika sayen dalar Amirka daya akan Naira dubu 10 ba. Tun bayan da Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta cire tallafin dala ne farashin dalar yayi tashin gwauron zabi zuwa sama da Naira 1,600. Hakan ya taimaka wajan hauhawar farashin kayan masarufi.
‘Yansanda sun kama masu gàrkùwà da mutane a Kano

‘Yansanda sun kama masu gàrkùwà da mutane a Kano

Duk Labarai
'Yansanda a jihar Kano sun kama masu laifi gida 82. An kamasu ne tsakanin Nov. 1 zuwa Nov. 14. Wanda aka kama din ana zarginsu da aikata laifukan kwacen waya, garkuwa da mutane da safarar kwaya. Kakakin 'yansandan jihar, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a hedikwatar 'yansandan jihar dake Bompai Kano. Ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne bayan wasu dabaru da suka fito dasu na kama masu laifi. Yace sun kwace makaman Bindiga AK 47 guda daya da bindigu kirar gida guda 3 da adduna da wukake guda 30 sai miyagun gwayoyi da sauransu. Ya bayar da tabbacin ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya a jihar da yaki da aikata miyagun laifuka.
Karya ake mana, bamu ce mun daina siyo man fetur daga kasar waje ba>>NNPCL

Karya ake mana, bamu ce mun daina siyo man fetur daga kasar waje ba>>NNPCL

Duk Labarai
Kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya musanta Rahotannin dake cewa ya daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje inda a yanzu yake sayen man daga matatar man fetur ta Dangote. Labarai sun yadu dai cewa NNPCL tace ta daina shigowa da man fetur daga kasashen waje. Saidai a sanarwar da kakakin NNPCL din Mr Femi Soneye ya fitar yace wannan rahoto ba gaskiya bane. Yace suna dubawane su ga idan shigo da man fetur din daga kasar waje yafi sauki to daga wajen zasu siyo idan kuma sayenshi a gida yafi sauki to sai su siya a gida. Yace lamarin labarin cewa sun daina shigo da man fetur ba gaskiya bane inda ya jawo hankalin 'yan jarida da su rika yin bincike kamin watsa labaransu.
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn na shekarar 2025

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn na shekarar 2025

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudin Naira Tiriliyan N47.9trn a matsayin kasafin kudin shekarar 2025. Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis bayan zaman majalisar zartaswa. Yace nan da ranar Juma'a ko Litinin ake tunanin gabatarwa da majalisar tarayya da kasafin kudin a hukumance.
An gano wani gidan Alfarma a kasar Amurka da ake zargin Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya siya da kudaden sata

An gano wani gidan Alfarma a kasar Amurka da ake zargin Tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya siya da kudaden sata

Duk Labarai
An gano wani gidan Alfarma na miliyoyin daloli da tsohon me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya saya a kasar Amurka. Sambo Dasuki dai an kamashi bisa zargin cinye Biliyoyin kudade da aka ware dan yaki da kungiyar Boko Haram a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan. Sannan a wannan sabon bincike da ya bayyana an gano Dasuki yayi amfani da kudaden wajan sayen godajen Alfarma a biranen Los Angeles, California da kuma babbar unguwar masu kudi ta McLean, Virginia, dake babban birnin kasar Amurka, Washington, DC. Wata kungiya dake bincike da kwarmaton yanda ake sace kudaden talakawa a kasar Afrika me suna (PPLAAF) ce ta gano lamarin. Kungiyar tace wasu dake taimakawa Dasuki sayen gidajen alfarmar Robert da Mimie Oshodin sun karbi akalla Da...
Labari me Dadi: Gwamnatin tarayya zata rika samu kudin shiga da ya kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata

Labari me Dadi: Gwamnatin tarayya zata rika samu kudin shiga da ya kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata

Duk Labarai
Rahotanni sun ce biyo bayan karuwar yawan man fetur din da kamfanin man fetur na kasa NNPCL ya sanar da cewa an samu na ganga Miliyan 1.8 duk kullun, yawan kudin da gwamnatin tarayya ke samu zai karu zuwa Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata. Farashin man Brent yana a matsayin dala $81 kowace ganga. Idan ana samun ganga Miliyan 1.8 kullun hakan na nufin Najeriya zata samu kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N6.99tn duk wata. Shugaban kamfanin man fetur dun na kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis inda yace yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya karu.
An kori malaman jami’a 4 saboda lalata da dalibai mata

An kori malaman jami’a 4 saboda lalata da dalibai mata

Duk Labarai
Masu gudanarwa na makarantar jami'ar Federal University, Lokoja, dale jihar Kogi, sun sallami malamai 4 daga aiki saboda samunsu da aikata ba daidai ba wajan jarabawa da kuma yin lalata da dalibai mata. Sun zartar da wannan hukunci ne ranar Alhamis bayan wani zama da suka yi kan batun. Hakan ya biyo bayan zargin da akawa malaman na yin lalata da dalibai mata da kuma aikata ba daidai ba wajan jarabawa. Shugaban kwamitin gudanarwar makarantar, Senator Victor Ndoma-Egba ya yabawa wadanda suka yi wannan bincike inda yace sun kyauta da suka bi ka'ida wajan yin binciken. Yace kuma su gaggauta kammala sauran binciken da ake yo akan malamai. Ya jawo hankalin malaman kada su saka kansu wajan cin zarafin dalibai sannan ya jawo hankalin daliban da duk wanda aka ci zarafinsa da ya fito ...
Ka Hakura da neman zama shugaban kasa, Allah be kaddaro maka zaka mulki Najeriya ba>>Wike ya gayawa Atiku

Ka Hakura da neman zama shugaban kasa, Allah be kaddaro maka zaka mulki Najeriya ba>>Wike ya gayawa Atiku

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesome Wike ya gayawa Alhaji Atiku Abubakar cewa ya daina neman takarar shugabancin Najeriya dan ba zai samu ba saboda Allah be kaddaro masa zai mulki Najeriya ba. Wike ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka inda ya kara da cewa, laifuka da cin amanar da yawa jam'iyyar PDP ne a baya ke tambayarsa. Yace ya kamata Atiku ya gane cewa shi yanzu ya zama uba dan a lokacin da yayi takara a jami'iyyar SDP Wike bai wuce shekaru 25 ba. Dan haka yace Atikun ya hakura dan a shekarar 2027, PDP ba zata sake bata tikitin takarar shugaban kasarta ta baiwa wanda ba zai ci zabe ba dama.

Maganin kaikayin fuska

Gyaran Fuska
Fuskar mutum na iya yin kaikayi saboda dalilai daban-daban. Zai iya zama saboda bushewa, cizon wani kwaro ko wata rashin lafiyar fata. Maganin kaikayin fuskar ya danganta ne ga irin dalilin da yasa take kaikayin. Idan ya zamana lokacin sanyi ne ko kuma ka dade a waje yasa fuskarka ta bushe, to hanya mafi sauki shine a shafa mai. Hakanan mutanen da suka manyanta, suma fuskarsu na daukar kaikayi saboda yawan shekaru, suma dai masana kiwon lafiya sun ce shafa mai shine mafita. Bayan wannan kuma akwai wanda ake samun kaikayin fuska saboda cizon wani kwaro kamar sauro da sauransu. Irin wannan ana barinshi ya warke da kanshi, idan kuma bai warke da kanshi ba to ana iya amfani da soso da sabulu a wanke fuskar. Ana kuma iya dora ruwan sanyi ko a samu kankara a nade a fuska a dora...