Daga Adam Elduniya Shinkafi
Yau Asabar 05/10/2024 Allah Ya yi wa yayana Mukhtar Elduniya Shinkafi kuɓuta daga hannun ƴan bindiga bayan ya shafe sama da wata ɗaya a hannunsu.
Mun biya maƙuddan kuɗaɗe na fansar sa, bayan shekaranjiya sun bamu account number mun tura masu maira miliyan biyu advance jiya kuma mun kai masu cikon miliyoyinsu.
Muna godiya kwarai da gaske ga ƴan uwa da abokan arziki da suka taimake mu da gudunmawar kuɗi da kuma addu'a da masu ba mu shawarwari muna godiya kwarai da gaske ga kowa da kowa.
Muna addu'a Allah Ya tsare gaba, Ya tsare mu, Ya baiwa Mukhtar lafiya, Ya kuɓutar da sauran bayin Allah da suke hannunsu, Ya maida mana da alkairi akan abubuwan da muka yi asara, mun karɓi wannan ƙaddara/jarrabawa hannu bibbiyu, mun yarda cewa daga gare ka ne....
Tauraron Fina-finan Hausa, Adam A. Zango kenan yake yanka Kek din zagayowar ranar Haihuwarsa.
Ya wallafa hoton a shafinsa na sada zumunta inda ya godewa masoyansa bisa soyayyar da suka nuna masa a yayin bikin na zagayowar ranar haihuwartasa.
Kasar Faransa ta bayyana cewa ta daina sayarwa da kasar Israela makamai saboda kisan Falas-dinawa da kasar ta Israela ke yi.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kasar ta Faransa bayan da yaki tsakanin Israela da Hamas ya dauki tsawon kusan shekara guda ana yi.
Israela dai ta kashe mata da yara da fararen hula da dama a yakin wanda da yawa ke bayyana cewa tanawa Falasdinawan kisan kare dangine.
Da yawa sun ji dadin wannan mataki da kasar ta Faransa ta dauka inda rahotanni suka ce Faransar kuma ta yi kira ga sauran kasashen dakw sayarwa Israela makamai su daina.
Ta kara da cewa tana son a dauki hanyar diflomasiyya a matsayin wadda zata kawo karshen wannan rikici.
Ba sha a ji dadi a baki bane kadai amfanin Kankana, yana kuma da amfani masu yawa a jikin dan Adam musamman a fuska.
A wannan rubutu, zamu muku bayanin Amfanin bawon Kankana a fuska.
Bawon kankana idan aka shafashi a fuska yana sanya fuskar ta yi haske.
Hakanan kuma yana maganin abubuwan dake sa fuska ta tattare ta yi kamar ta tsaffi da kuma duhun da hasken rana ke sa fuska.
Amfani da bawon kankana ko kankanar kanta ko man shafawa da aka hada da kankana na taimakawa matuka wajan zaman fuska tana sheki irin ta matasa.
Hakanan ruwan kankana ko lemun da aka hada da kankana idan aka shafashi a fuska akai-akai, yana taimakawa wajan kawar da kurajen fuska.
Shafa ruwan kankana a fuska yana kawar da tabon bakaken abubuwan dake fuska masu kama da kuraje sannan yana hana sake fito...
Kankana na da matukar amfani sosai a jikin dan Adam musamman mata. A wannan rubutu, zamu bayyana amfanin Kankana a jikin mata.
Da farko dai kankana na da Sinadaran Vitamins A, B6, da C wanda suke karawa fata sheki, da lafiya.
Hakanan tana maganin bushewar fata, da maganin ciwon daji watau Cancer.
Ga mata masu ciki, Kankana na taimakawa sosai wajan nakuda da hana bari da haihuwar bakwaini.
Kankana na daya daga cikin kayan itatuwan da masana ilimin kimiyyar lafiya ke cewa mace me neman daukar ciki ta ci dan samun ciki cikin sauri.
Kankana na daya daga cikin kayan marmari da ake amfani dasu a kasar Hausa, a wannan rubutun, zamu kawo muku jawabin amfanin Kankana ga Namiji.
Kankana na taimakawa maza wajan lafiyar gabansu musamman maraina ga mazan da suka fara manyanta.
Tana da sinadaran Antioxidant wanda ke boye alamun tsufa.
Tana kara gudun jini a jikin mutum wanda hakan zai karawa namijin dake shanta karfin Azzakari.
Masana sunce ga maza wanda suka manyanta wanda ke amfani da maganin karfin maza dan Azzakarin su ya tashi, zasu iya yin amfani da kankana a madadin shan wadannan magunguna.
Kankana na taimakawa wajan samun ingantaccen bacci.
Kankana na taimakawa maza wajan kara ingancin maniyyinsu.
Kankana na taimakawa karin lafiya ga zuciya.
Kankana na kuma da sinadaran dake yaki da cutar Daji w...
Waken suya na daya daga cikin manyan abinci a kasar Hausa inda ake abubuwa dashi da yawa kama daga Awara, madara, kai wasu ma na soyashi a rika ci kamar gyada.
A wannan rubutu zamu bayyana amfanin waken suya a jikin mace.
Waken suya na da amfani sosai musamman ga mace wadda ta fara manyanta, alamomin tsufa da kuma sakin jiki ba zasu bayyana sosai ba idan tana amfani da waken suya.
Matan da suka kai matakin manyanta,sukan yi fama da zufar dare, yawan amfani da waken suya na magance wannan matsala.
Hakanan ga matan dake son rage kiba, waken suya na taimakawa sosai a wannan bangaren.
Hakanan yana taimakawa mata wajan rage matsalolin jinin al'ada.
Wani bincike yace waken suya na taimakawa wajan garkuwa ga hana kamuwa da cutar dajin mama watau Breast cancer.
Yana kuma taim...
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi kenan a wadannan Kayatattun hotunan nata a kusa da wata mota ta Alfarma.
Ta sakarwa masoyanta hotunan ne a shafinta na sada zumunta.
Bayan Shekara Goma Suna Soyayya A Karshe Dai Sun Yi Aure.
Ban taba ganin masoyan da suka rike amana kamar wadannan ba. Sun hadu a FCE Katsina tun a 2014.
Bayan kwashe sama da shekara goma suna soyayya, yanzu dai an daura musu aure.
Allah Ya sa alkairi ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba Abokina Jamilu Abubakar J-Star da Amaryar shi Zainab Galadanci.
Daga Sulaiman Lawal kamfani