Thursday, July 9
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Duka ‘yan Siyasar Arewa Har ni mun baiwa mutanen Arewa Kunya, muna da hannu a lalacewar yankin Arewa dan haka dole mu fito mu baiwa mutane hakuri>>Inji Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani

Duka ‘yan Siyasar Arewa Har ni mun baiwa mutanen Arewa Kunya, muna da hannu a lalacewar yankin Arewa dan haka dole mu fito mu baiwa mutane hakuri>>Inji Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana cewa duk wani dan siyasar Arewa da ya taba rike mukami a cikin shekaru 20 da suka gabata, yana da hannu wajan lalacewar yankin. Yace matsalar Arewa ba a cikin shekaru 2 da suka gabata ta fara ba, ta dade ana fama da ita. Ya kara da cewa, kuma duk wani dan siyasa da ya taba rike mukami a yankin ya kamata ya fito ya baiwa mutane hakuri saboda sun gaza. Yace a lokacin Mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saki kudi sosai na tallafi yace amma da yake in dambu yayi yawa baya jin mai, hakan bai kawo karshen matsalar ba. Uba Sani yace mutane su yi hankali da 'yan siyasar da ana tare dasu a baya amma su rika warewa suna cewa wai su sun tuba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Trust TV.
INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Sama Da Mutàñe Gomà Suñ Ŕasù Sakamakòn Wani Hadaŕi Da Ya Auku A Garin Okène Dake Jihar Kogi

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN: Sama Da Mutàñe Gomà Suñ Ŕasù Sakamakòn Wani Hadaŕi Da Ya Auku A Garin Okène Dake Jihar Kogi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Sama Da Mutàñe Gomà Suñ Ŕasù Sakamakòn Wani Hadaŕi Da Ya Auku A Garin Okène Dake Jihar Kogi Lamarin ya auku ne a daren jiya, inda mutane sama da goma suka rasu, wanda hadarin ya shafi Keke napep guda biyu, karamar moto daya da kuma motar Dangote. Allah Ya gafarta musu. Daga Drezy Asad
An sace jakar shugabar hukumar tusaron kasar Amurka

An sace jakar shugabar hukumar tusaron kasar Amurka

Duk Labarai
Shugabar hukumar tsaron Homeland Security ta kasar Amurka, Kristi Noem ta gamu da 'yan sane inda suka sace mata karamar jaka ta mata da ake cewa Purse. Jakar dai na dauke da Dala $3000 da kuma katinta na aiki. Hakanan an sace jakar ne a wani wajen cin abinci dake baban birnin kasar watau Washington DC. Hakana Barawon ya kuma sace jakar dake dauke da magungunan matar. Ta je gidan abincinne dan cin abinci da danginta a matsayin ranar Bikin Easter.
Darajar hannun jari da Dala sun sake faduwa a Amurka saboda Trump

Darajar hannun jari da Dala sun sake faduwa a Amurka saboda Trump

Duk Labarai
Darajar hannun jari a Amurka da kuma kuɗin ƙasar Dala, ta ƙara faɗuwa, bayan da Shugaba Trump ya sake nanata sukar da yake yi wa shugaban babban bankin ƙasar. A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara na - Truth Social, Mista Trump ya kira, shugaban bankin Jerome Powell a matsayin babban mai asara, saboda ya ƙi rage yawan kuɗin ruwa. Wannan matsala da ke ci gaba ta sake tasowa ne a wannan karon yayin da shugabanni da jagororin harkokin kudade suke nufar babban birnin Amurka - Washington domin halartar taron Babban Bankin Duniya, da kuma Asusun Bayar da Lamuni na duniya, IMF. Shugaban kamfanin zuba jari na kamfanin Scharf Investments, Brian Krawez, ya yi bayani kan wannan hali na kara sulmiyowar darajar hannayen jari na Amurka da kuma darajar Dalar, bayan da Sh...
Mutanen jihar Zamfra sun biya Naira Miliyan 500 a matsayin kudin Haraji ga ‘yan Bìndìgà dan kada su kai musu hari a shekarar 2025

Mutanen jihar Zamfra sun biya Naira Miliyan 500 a matsayin kudin Haraji ga ‘yan Bìndìgà dan kada su kai musu hari a shekarar 2025

Duk Labarai
Kauyuka da yawa ne suke biyan 'yan Bindiga kudaden Haraji a jihar Zamfara dan kada su kai musu hari ko su yi garkuwa dasu. A shekarar 2025 dinnan da muke ciki kawai, watau daga watan Janairu zuwa yanzu Mutanen jiha Zamfarar sun biya 'yan Bindiga jimullar Harajin Naira Miliyan 500, kamar yanda jaridar Daily Trust ta bayyana. A watan Janairu kawai, marigayi dan Bindiga Isuhu Yellow, ya kakabawa mutanen kauyuka 25 harajin Naira Miliyan 172.7. Hakanan shima Dogo Gide ya kakabawa kauyuka 23 Harajin Naira Miliyan 100. Lamarin 'yan Bindiga dai na ci gaba da ta'azzara duk da ikirarin kokarin da gwamnati ke cewa tana yi.
Wutar Awanni 2 kacal jihohin Katsina, Jigawa da Kano ke samu

Wutar Awanni 2 kacal jihohin Katsina, Jigawa da Kano ke samu

Duk Labarai
Mutanen jihohin Katsina, Kano, da Jigawa na fuskantar matsi saboda karancin wutar lantarkin da suke samu inda a yanzu wutar awanni 2 kacal ake basu a yini. Da yawan kananan 'yan kasuwa sun koka da cewa suna fuskantar matsala wajan gudanar da ayyukansu saboda rashin ko karancin wutar a wadannan jihohi. Yawancin kasuwancin da wannan matsala tafi shafa sune Teloli, Masu sayar da kankara, mas cajin waya, masu sana'ar walda da sauransu. Hukumar wutar dake kula da wadannan jihohi, (KEDCO) ta bayyana cewa an samu karancin wutar ne saboda gyare-gyaren da take dan inganta ayyukanta.
Gidajen man fetur da ‘yan kasuwar man sun tafka Asara bayan da kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din inda a yanzu yake sayar dashi da Arha fiye da na Dangote

Gidajen man fetur da ‘yan kasuwar man sun tafka Asara bayan da kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din inda a yanzu yake sayar dashi da Arha fiye da na Dangote

Duk Labarai
' Yan kasuwar man fetur sun koka da sarar da suka tafka bayan da kamfanin mai na kasa NNPCL ya rage farashin man da yake sayarwa. A Legas, NNPCL na sayar da litar man fetur din aka farashin Naira 880 kan kowace lita yayin da a Abuja kuma NNPCL din na sayar da man fetur din akan farashin 935 akan kowace lita. Hakan na zuwane sati daya bayan da Dangote ya rage farashin man fetur din nasa. A Legas, Farashin man fetur din na NNPCL yafi na Dangote Arha da Naira 10. Saidai kamfanin na NNPCL ya baiwa 'yan kasuwar damar su sayar da tsohon man da suke dashi kamin fara amfani da sabon farashin.