Saturday, April 25
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Tsare-Tsarena sun sa farashin kayan abinci sun sauka fiye da kamin in hau mulki>>Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Tsare-Tsarena sun sa farashin kayan abinci sun sauka fiye da kamin in hau mulki>>Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, farashin kayan abincin ya sauka saboda tsare-tsaren gwamnatinsa. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV. Ya kara da cewa, idan aka kwatanta yanda Najeriya take a yanzu da yanda take kamin shugaba Tinubu ya hau mulki za'a ga banbanci. Ya koka da cewa kasafin kudin Najeriya duka bai wuce dala Biliyan $30 ba sannan ga asibitoci a lalace ga tituna a lalace da sauransu. A karshe dai ya tabbatar da cewa farashin kayan abinci ya sauka.
Dansandan Najeriya ya mutu a dakin Otal bayan ya shiga ciki da wata mata

Dansandan Najeriya ya mutu a dakin Otal bayan ya shiga ciki da wata mata

Duk Labarai
An gano gawar wani dansandan Najeriya a dakin otal dake Uzum Estate, Oyeyemi Akute jihar Ogun. Sunan Otal din Super G Royal Hotel sannan sunan dansandan da aka gawarsa, Inspector Haruna Mohammed. Saidai matar da suka shiga dakin otal din da ita ta tsere ba'a san inda ta yi ba. Rahoton jaridar thenation ya bayyana cewa, dansandan ya shiga otal din da matar ranar February 15, 2025 da misalin karfe 1 na dare. Ganin karshe da akawa matar da suka shiga dakin da ita shine da misalin karfe shida na safe inda ta bukaci a bata ruwan sha. Manajar otal din wadda macece ta fara ganin gawar dansandan inda tuni aka tafi da ita ofishin 'yansandan dan gudanar da bincike. Kakakin 'yansandan jihar, CSP Omolola Odutola ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun gano gawar babu wata alamar...
Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam’iyyar APC ba, masu koma kuwa suna yi ne dan samun na Abinci>>Tambuwal

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa duk dan siyasar da yasan abinda yake ba zai koma Jam'iyyar APC ba. Ya bayyana hakane a wajan taron Jam'iyyar PDP da aka gudamar a Jiya Asabar inda yace masu ruguguwar komawa APC suna yi ne dan neman na Abinci. Yace ba dan mutane 'yan siyasar suke komawa APC ba inda yace ta yaya zasu rika saurin komawa Jam'iyyar duk da matsin tattalin arzikin da ake fama dashi da kuma rashin iya mulki na Jam'iyyar. Yayi kira ga 'yan Adawa da su hada kai a shekarar 2027 su kawar da Jam'iyyar ta APC daga mulki.
A 2027 ‘yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa>>Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

A 2027 ‘yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa>>Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, a shekarar 2027 'yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa. Ya bayyana hakanne a ranar Asabar a Dandalin Murtala dake Kaduna inda aka yi bikin karbar wasu sabbin 'yan jam'iyyar APC. Yace 'yan Najeriya zasu sabi APC dinne saboda Adalcin data musu. Ya kara da cewa a shekarar 2027 za'a sake zabar Tinubu a matsayin shugaban kasa inda kuma za'a sake zabarsa a matsayin gwamna sannan duka 'yan majalisar wakilai da jihohi ma haka. Yace sabbin 'yan jam'iyyar da suka shigo ba za'a nuna musu wariya ba, zasu samu iko kamar kowane dan Jam'iyyar inda yace kan Jam'iyyar APC a hade yake.
Kiristancin Arewa, Maguzawa, da sauran mutanen Arewa ta tsakiya sunce basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Tinubu

Kiristancin Arewa, Maguzawa, da sauran mutanen Arewa ta tsakiya sunce basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Tinubu

Duk Labarai
Mutanen Arewa ta tsakiya da suka hada da Kiristoci da Maguzawa, da mutanen jihar Jos da sauransu sun bayyana cewa, basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Sun bayyana cewa su a shekarar 2027, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ne zabinsu. Saidai wadannan mutane dake son ballewa dan nuna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, kalilan ne daga cikin mutanen Arewa. Saidai a gefe daya kuma, Mafi yawan 'yan Arewa sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce ba zasu zabeshi ba a zaben 2027. Kungiyoyin fafutuka da yawa daga Arewa sun bayyana cewa ba zasu goyi bayan sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027 ba. Shugaban kungiyar hadaka ta kungiyoyin Arewar, Jamilu Charanchi ya bayyana cewa ...
Hukumomin sojin Amurka sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin kasar Abinci

Hukumomin sojin Amurka sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin kasar Abinci

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa hukumomin sojin kasa na kasar ana zargin sun sace kudin da aka ware dan ciyar da sojojin abinci. Sojojin dai na kokawa da basu abinci musamman nama wanda bai dahu ba, sannan kuma abincin ana basu shi kamar na gidan yari babu wani dadi da kayan hadin da ya kamata. Jaridar Foxnews ta kasar ta ruwaito cewa ana zargin manyan sojojin da karkatar da makudan kudaden da aka ware dan ciyar da sojojin zuwa wata hanya ta daban. Jimullar dana Miliyan $225 ne aka ware dan ciyar da sojojin kasar a barikinsu daban-daban dake fadin kasar saidai bincike ya nuna cewa daga cikin kudin, an sace dala miliyan $151 inda aka karkatar dasu zuwa wasu gurare daban. Rahoton yace a kowane wata ana biyan kowane soja dala $465 wanda kuma ana cire haraji daga cikin kudin. ...
Kalli Bidiyon dalibar makarantar sakandare tana latata da maza abokan karatunta su 5 ya bayyana

Kalli Bidiyon dalibar makarantar sakandare tana latata da maza abokan karatunta su 5 ya bayyana

Duk Labarai
Bidiyon wata dalibar makarantar Sakandare da abokan karatunta maza su biyar suna lalata da ita ya karade kafafen sada zumunta. Lamarin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa karamar yarinya ce dalibar amma ta iya jure yin lalata da maza biyar. Rahotanni sun bayyana cewa, tuni an kori dalibar daga makarantar. Saboda tsiraici da ya bayyana karara a bidiyon yasa ba zamu iya kawo muku shi ba anan, saidai muce Allah ya kyauta. Saidai ga bidiyon yanda aka koreta daga makarantar kamar haka
Makaranta a Najeriya ta kori ɗalibar da ta fallawa malami mari kan ya hanata TikTok

Makaranta a Najeriya ta kori ɗalibar da ta fallawa malami mari kan ya hanata TikTok

Duk Labarai
Hukumomin Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke, Awka a jihar Anambra ta kori ɗalibar nan, Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cakuma tare da cin kwalar wani malamin jami'ar. A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga ɗalibar ta far wa malamin jami'ar, Dr Chukwudi Okoye, bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani lungu da ke harabar jami'ar. Cikin takardar korar da jami'ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wadda magatakardar jami'ar, Victor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami'ar ta kafa. ''Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami'ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)'', in ji takardar korar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito. ...
An ɗage taron mahaddata Qur’ani da aka shirya yi a Abuja

An ɗage taron mahaddata Qur’ani da aka shirya yi a Abuja

Duk Labarai
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur'ani da ake yi wa laƙabi da Qur'anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya. An dai saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 da ranar da za a yi taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur'ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya. Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa "tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro. Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC haƙiƙanin dalilin da ya sa aka ɗage taro ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba. "Ana sa ran sai bayan Ramadan." In ji majiyar. Manufar taron Taron dai wanda tuni allunan tallansa suka cika man...
Makaman da muke dasu zasu iya lalata duniya sau 100>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump

Makaman da muke dasu zasu iya lalata duniya sau 100>>Inji Shugaban Amurka, Donald Trump

Duk Labarai
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi yin taro da kasashen Duniya wanda suka hada da China, da Rasha inda yace zai bayar da shawarar su taru su 3 din suk su rage yawan makaman da suke dasu. Shugaban yace maimakon kashe makudan kudaden da suke akan tsaro, kamata yayi su mayar da hankali wajan kashe irin wadanna kudaden akan ayyukan ci gaban wa mutanen kasarsu. Yace zai nemi duka su ukun su rage kashe kudi akan tsaro da kaso 50 cikin 100 watau su raba kudin gida biyu inda yace yayi amannar kuma zasu amince. Trump yace a yanzu Amurka na da makamai na kare dangi wanda zasu iya lalata Duniya har sau 100 dan haka babu bukatar a ci gaba da kera makaman kare dangi. Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da shugaban India, Nedradi Modi.