Shugaba Tinubu zai tafi Saudi Arabia gobe don taron rikicin Gabas ta Tsakiya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da wasu ministoci tare da wasu shugabannin hukumomi za su bar Abuja a gobe Lahadi domin halartar taron koli na hadin gwiwa na kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a fara ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, a babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.
Za a yi taron ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bayan makamancin taron da aka yi a birnin a bara.
Taron zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki yanzu a Gabas ta Tsakiya.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya sanar da tafiyar a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a yau Asabar.
Sanarwar ta ce shugaban zai samu rakiyar mini...








