Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Yawan man fetur din da Najeriya take hakowa ya ragu

Yawan man fetur din da Najeriya take hakowa ya ragu

Duk Labarai
Bayanai daga babban bankin Najeriya sun nuna cewa yawan man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu a watanni 3 na biyu na shekarar 2024. Man fetur din da Najeriya ke hakowa ya ragu da kaso 4.51% cikin 100 inda a yanzu Najeriya ke hako ganga Miliyan 1.27 a duk rana. A watanni 3 na farkon shekarar 2024 kuwa, Najeriya na hako ganga miliyan 1.33 ne wanda hakan ke nuna cewa an samu koma baya kenan. An dora alhakin hakan akan satar danyen man da kuma lalata bututun man fetur din wasu bata gari ke yi a yankin Naija Delta. Hakanan yawan man fetur din da Najeriyar ke hakowa yayi kasa da yawan wanda kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC ta bukaci kowace kasa ta rika hakowa watau Ganga Miliyan 1.58 a duk rana. Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL dai ya sanar da cewa ya kashe Nair...
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daga zaman majalisar zartaswa har sai abinda hali yayi saboda mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daga zaman majalisar zartaswa har sai abinda hali yayi saboda mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya daga zaman majalisar zartaswa saboda mutuwar shugaban sojojin Najeriya Lt General Taoreed Lagbaja. Shugaban yace za'a sanar da sabuwar ranar yin zaman nan gaba. A yau, Larabane ya kamata a yi zaman na majalisar zartaswar amma aka dagashi sai abinda hali yayi saboda girmama shugaban sojojin da ya mutu. Shugaban ya kuma bayar da umarnin yin kasa-kasa sa tutocin Najeriya har nan da sati daya.
Ban san an kama kananan yara ba>>Gwamna Abba Kabir Yusuf

Ban san an kama kananan yara ba>>Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin cikinsa da sakin kananan yara da aka kama bisa zargin cin amanar kasa. Gwamnan yace bai san an kama yaran ba sai bayan da aka kaisu gaban kotu a Abuja. Ya bayyana hakane a Asibitin Muhammadu Buhari Special Hospital inda aka kai yaran dan a dubasu a tabbatar suna cikin koshin lafiya. Gwamnan ya kuma godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan yafewa yaran inda yace zai tabbatar an sada su da iyalansu sannan a tabbatar sun koma makaranta dan Inganta rayuwarsu.
Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka

Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasar a karo na 2 inda ya doke abokiyar takararsa Kamala Harris. Tuni dai ya bayyana cewa dama an gaya masa ba a banza Allah ya tsallakar dashi daga yunkirin kisan da aka so yi masa ba. Shuwagabannin kasashe irin na faransa, Israela, Firaministan Ingila tuni suka taya Donald Trump murnar lashe zaben.
Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya mutu

Da Duminsa: Shugaban Sojojin Najeriya ya mutu

Duk Labarai
Kakakin shugaban kasa,Bayo Onanuga ya tabbatar da mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Abiodun Lagbaja. Shugaban kasar ya bayyana cewa cikin takaici da alhini yana sanar da mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Lt. General Taoreed Abiodun Lagbaja. Ya mutu ne yana da shekaru 56. Sanarwar tace ya mutu ne a daren ranar Talata a Legas bayan wata rashin lafiya. An haifeshi a shekarar February 28, 1968 kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nadashi Shugaban sojojin Najeriya ranar June 19, 2023.
Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Jihar Gombe ta kulla yarjejeniya da kamfanin kasar China dan samarwa da kanta wutar Lantarki

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Gombe ta samarwa da kanta hanyar samun wutar lantarki wadda ba sai ta dogara da gwamnatin tarayya ba. Gwamnatin ta sakawa wata yarjejeniyar samar da wutar me karfin megawatt 100 daga hasken Rana hannu tare da kamfanin China18th Engineering na kasar China. Gwamnan jihar Inuwa Yahya ya bayyana cewa, hakan zai basu damar karfafa huldar kasuwanci a jihar. Yace kudirin dokar da majalisa ta yi da ya baiwa jihohi damar samarwa da kansu wutar lantarki da rabata ne ya basu damar kaiwa ga wannan mataki.
Kalli yanda wani bature ya ke zaune a Kauyen Legas inda yace abinda ke burgeshi shine baya biyan kudin haya

Kalli yanda wani bature ya ke zaune a Kauyen Legas inda yace abinda ke burgeshi shine baya biyan kudin haya

Duk Labarai
Wani bature dake zaune a Kauyen Legas ya bayyana cewa, Abinda ke burgeshi shine baya biyan kudin haya. Bauturen na zaunene a kauyen Legas da ake kira Makoko wanda ke akan ruwa. https://twitter.com/whatsappblog9ja/status/1853830143988343061?t=1fO--driHjmkmz2HNDONxQ&s=19 Kuma an shiga dashi ya nuna ko ina a cikin dakinsa. An tambayeshi me yasa be je unguwar masu kudi ya zauna ba, sai ya kayar da baki yace idan dai ka iya zama da mutane lafiya, babu inda ba zaka je ka zauna ba.
Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki

Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki

Duk Labarai
Majalisar wakilai ta gayyaci ministoci 3 da suka hada da na Noma, da samar da abinci, Abubakar Kyari da na kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, Uche Nnaji, dana kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu dan su mata bayani kan yanda aka kashe Dala Biliyan $2 da aka bayar dan samarwa da Najeriya wutar lantarki. Kwamitin kula da makamashi na zamani na majalisar ne suka gayyaci ministocin. Kudin an samo su ne daga tallafi da kuma zuba jari dan samarwa da Najeriya wata hanya ta daban ta samun wutar lantarki banda wadda ake da ita. Kuma an samu kudinne daga shekarar 2015 zuwa yanzu. A ranar Talata da Larabane dai ministocin zasu gurfanar gaban majalisar dan bayar da ba'asi kan yanda aka kashe wadannan kudade. Majalisar ta nuna damuwa kan cewa duk da wadannan kudade amma gashi wut...
Muna da Hujjojin cewa kun aikata laifin cin amanar kasa amma dai Tausayine yasa muka yafe muku>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa kananan yaran da ta yiwa Afuwa

Muna da Hujjojin cewa kun aikata laifin cin amanar kasa amma dai Tausayine yasa muka yafe muku>>Gwamnatin Tarayya ta gayawa kananan yaran da ta yiwa Afuwa

Duk Labarai
Kananan yaran da aka kama aka gurfabar a kotu bisa zargin cin amanar kasa da yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu amma Shugaban ya yafe musu sun koma gida Kano. Kamin komawarsu, sai da suka je fadar shugaban kasa suka gana da mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima inda ya bayyana musu cewa suna da Bidiyo da hotuna dake nuna cewa sun aikata laifi amma tausayi irin na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne yasa ya yafe musu. Ya bayyana cewa zanga-zangar tsadat rayuwa ta jawo asarar Naira Biliyan 300. Ya jawo hankalin matasan da cewa kada su yadda ayi amfani dasu wajan tayar da fitina inda yace wannan dama ce da suka sake samu ta su zama na gari. Tuni dai aka mika su hannun gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ina shima ya daukesu zuwa gida.
Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

Najeriya ta fada Duhu yayin da matsalar wutar lantarki ta sake aukuwa, Ji Jihohinnda lamarin ya shafa

Duk Labarai
'Yan Najeriya sun fada duhu biyo bayan sake samun matsala da wutar lantarkin kasar ta yi. Wannan shine karo na 3 da wutar lantarkin kasar ke samun matsala a shekarar 2024. Da Misalin karfe 1:50 pm. Na ranar Talata ne wutar lantarkin ta sake samun matsala. Kamfanin kula da wutar na kasa,TCN ya tabbatar da hakan amma yace ba gaba daya wutar bace ta samu matsala. Kakakin hukumar, Ndidi Mbah ne ya tabbatar da hakan inda yace injiniyoyinsu na aiki tukuru dan dawo da wutar. Ya kara da cewa An samu dawo da wutar a babban birnin tarayya Abuja kuma suna kokarin dawo da ita a sauran jihohi.