Tuesday, July 7
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Banda mu a cikin wadanda suka saci man fetur daga tankar mai data fadi, Bidiyon karyane ake yadawa>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

Banda mu a cikin wadanda suka saci man fetur daga tankar mai data fadi, Bidiyon karyane ake yadawa>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta musanta cewa an ga jami'anta suna kwasar man fetur bayan da wata tankar mai ta fadi. Bidiyo ya watsu sosai inda aka ga wasu da kayan 'yansandan suma sun shiga sahu masu satarman daga tankar. Saidai a sanarwar da kakakin hukumar 'yansandan ta kasa, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, yace ba 'yansandan Najeriya ne ba a bidiyon, 'yansandan makwabtan Najeriya ne. Ya kara da cewa, an saki Bidiyonne kawai dan a batawa hukumar 'yansandan Najeriya suna. Yace jami'an tsaron dake bidiyon, faransanci suke ba Turanci ba yace dan haka ba 'yansandan Najeriya bane. Yace hukumar 'yansanda tana nan kan gudanar da aikinta bisa doka da kwarewa. Ya gargadi mutane su daina yada labarin da bai inganta ba.
Girman kai da haushine cike da zuciyar El-Rufai saboda bai samu Minista ba shiyasa ya koma SDP>>Inji APC

Girman kai da haushine cike da zuciyar El-Rufai saboda bai samu Minista ba shiyasa ya koma SDP>>Inji APC

Duk Labarai
jam'iyyar APC ta caccaki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda ta bayyanashi a matsayin wanda ke ci ke da girman kai da haushi saboda bai samu mukamin minista ba. Sakataren jam'iyyar, Felix Morka ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Yace El-Rufai ya kamata idan zai soki gwamnatin Tinubu yayi suka ta adalci. Felix yayi watsi da ikirarin El-Rufai na cewa jam'iyyar APC ta kauce daga kan turbar da aka kafata inda yace gwamnatin Tinubu ta samu ci gaba sosai da suka hada da cire tallafin man fetur da daidaita canjin kudi da sauransu.
Majalisar mu ta dattijai kamar kungiyar tsafi take, kowane Sanata na tsoron ya soki kakakin majalisa, Akpabio ya taba rike min hannu ya rika murzawa, kowace mace akawa haka tasan abinda ake nufi>>Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Akpabio tonon silili

Majalisar mu ta dattijai kamar kungiyar tsafi take, kowane Sanata na tsoron ya soki kakakin majalisa, Akpabio ya taba rike min hannu ya rika murzawa, kowace mace akawa haka tasan abinda ake nufi>>Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Akpabio tonon silili

Duk Labarai
Har yanzu dai Sanata Natasha Akpoti bata saurara ba da yiwa kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio tonon silili. A sabuwar hirar da ta yi da BBC Pidgin, Natasha tace majalisarsu kamar kungiyar tsafi take. Tace kowane sanata na tsoron ya bayyana ra'ayin da ya sha banban da na kakakin majalisar saboda tsoron kada a saka masa ido. Tace amma zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio da gaskene, ta sake maimaita cewa akwai sanda suka je gidansa ya kama hannunta a gaban mijinta ya ja ya suna tafiya, tace ya rika murza mata hannu, tace kowace mace akawa haka tasan abinda ake nufi. Tace hakanan akwai sanda ta manta ta tafi aiki da sauri bata dauki zoben alkawarinta na aure ba, tace Sanata Godswill Akpabio na ganinta sai yake ce mata yaya Natasha, naga baki saka zoben aurenk...
Dan Fim Din Kudu ya bayar da labarin yanda abokan aikinsa mata 3 suka masa fyàdè a yayin da suke wani otal daukar fim

Dan Fim Din Kudu ya bayar da labarin yanda abokan aikinsa mata 3 suka masa fyàdè a yayin da suke wani otal daukar fim

Duk Labarai
Dan fim din kudu, Lanre Adediwura ya bayyana yanda wasu mata 3 abokan aikinsa suka masa fyade a yayin da yaje aikin daukar wani fim. Yace da farko dai ya je wajan daukar fim dinne inda daga baya wata abokiyar aikinshi ta sameshi ta bayyana masa cewa, tana sonsa. Yace a nan ya sanar da ita yana da aure amma tace ta ji ta gani. Ya kara da cewa anan suka zauna suna buga karta ko wasan kati, da suka gama dare yayi, ya manta katin a hannunta. Yace ta je dakin otal dinsa dan ta kai masa katin, inda anan ne ya ganta da abokanta biyu sun je su masa fyade. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda lamarin ya jawo cece-kuce.
A kudancin Kaduna, Gwamnatin mu ta APC bata tabuka abin Arziki ba>>Inji Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

A kudancin Kaduna, Gwamnatin mu ta APC bata tabuka abin Arziki ba>>Inji Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Gwamnatinsu ta APC bata tabuka abin a zo a gani ba a kudancin jihar kaduna. Ya bayyana hakane a matsayin suka ga gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai. El-Rufai ya shafe shekaru 8 yana a matsayin gwamnan Kaduna saidai a kwanannan ya bar jam'iyyar APC zuwa PDP. A ci gaba da bayaninsa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Amma gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta canja akalar yankin inda ta kawo mai ci gaba. Ya bayar da misali na ci gaban da gwamnatin Tinubu ta kai yankin kudancin jihar Kaduna inda yace kwanannan Shugaba Tinubun ya sakawa kudirin dokar samar da jami'ar kimiyya da fasaha ta Federal University of Applied Sciences hannu wadda za'a bude a karamar hukumar Kachia.
El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani na Kaduna da sace kudaden kananan hukumomi ya je kasashen Ingila da Afrika ta kudu ya sayi gidaje

El-Rufai ya zargi Gwamna Uba Sani na Kaduna da sace kudaden kananan hukumomi ya je kasashen Ingila da Afrika ta kudu ya sayi gidaje

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zargi Gwamnan jihar me ci, Malam Uba Sani da yin amfani da kudaden kananan hukumomi ya sayi gidaje a kasashen Seychelles, South Africa, da the United Kingdom.  EL-RUFAI wanda bai dade da barin jam'iyyar APC zuwa SDP ba ya bayyana hakane a yayin hirar da aka yi dashi a gidan rediyon Najeriya dake Kaduna ranar Talata. Yace gwamna Uba Sani na karkatar da kudaden kananan hukumomi inda yake canjasu zuwa dala bisa shirin sayen gidaje. Yace amma shi a zamanin mulkinsa ba abinda yayi kenan ba. Yace a zamaninsa suna baiwa kananan hukumomi kudadensu, yace shuwagabannin kananan hukumomi na APC da PDP duk suna nan da rai kuma zasu iya bayar da shaida akan hakan. Yace amma hukumomin gwamnatin tarayya sun ki cewa uffan kan abinda...
Tanko Yakasai yayi kiran Arewa ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu saboda kokarinsa na tada komadar tattalin arziki na samar da sakamako me kyau

Tanko Yakasai yayi kiran Arewa ta ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu saboda kokarinsa na tada komadar tattalin arziki na samar da sakamako me kyau

Duk Labarai
Dattijon Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya yabawa Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda kokarin tayar da komadar tattalin arzikin da take. A bayanin da ya yiwa 'yan Jarida ranar Lahadi a Kano, Tanko Yakasai ya bayyana cewa, 'yan Najeriya sun fara samun sauki daga matsin tattalin arzikin da suke fuskanta. Yace farashin kayan masarufi da na man fetur na ci gaba da sauka. Yakasai yayi kira ga 'Yan Arewa dama Najeriya baki daya dasu ci gaba da baiwa gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu goyon baya. Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu na kokarin samar da ci gaban kasa kuma Arewa ba'a barta a baya ba a wannan kokari.
Me magana da yawun shugaban kasa ya nemi a zartar da hukuncin ķķìsà kan matashiya ‘yar bautar kasa data soki Gwammatin Tinubu

Me magana da yawun shugaban kasa ya nemi a zartar da hukuncin ķķìsà kan matashiya ‘yar bautar kasa data soki Gwammatin Tinubu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, me taimakawa shugaban kasa kan yada labarai, Temitope Ajayi ya nemi a zartar da hukuncin kisa kan matashiya Ushie Uguamaye saboda sukar da tawa shugaba Bola Ahmad Tinubu. Kafar peoplesgazette ce ta wallafa cewa Temitope Ajayi ya nemi a yankewa Ushie hukuncin kisa saboda yace a zartar mata hukunci mafi tsanani da hukumar bautar kasa ta NYSC ta tanadar. Saidai a bayaninsa, Ajayi, ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba, an canja masa manufar bayaninsa ne dan cimma wani buri. Yace abinda yake nufi da zartarwa da Ushie hukunci mafi tsanani a dokar NYSC shine a koreta daga aikin bautar kasar, yace shi a iya saninsa wannan ne hukunci mafi tsanani a dokar NYSC ba hukuncin kisa ba. Lamarin Ushie ya dauki hankula sosai inda ciki hadda Atiku Abubakar, da Pet...
Gwamnatin Shugaban kasa, Donald Trump zata kulle gidan yada labarai na VOA

Gwamnatin Shugaban kasa, Donald Trump zata kulle gidan yada labarai na VOA

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana cewa, shugaban kasar, Donald Trump yace zai kulle kafar yada labarai ta VOA. Dalili kuwa shine ana zargin kafar da rashin nuna goyon baya ga shugaba Trump. Shugaban VOA, Mike Abramowitz ya bayyana cewa, shi da ma'aikatansa, 1,300 duk an ce su tafi hutu kuma an dakatar da Albashinsu. Ya bayyana cewa, wannan na zuwane a yayin da kasashe irin su Iran, China da Rasha ke yada labaran karya game da kasar ta Amurka. Ana ganin dai wannan matakin kamar hanyace ta dakile aikin jarida da Shugaba Trump ya dauko.
Ji labarin Ushie Uguamaye, ‘Yar bautar kasa data tayarwa da gwamnatin Tarayya hankali saboda sukar Gwamnatin Tinubu, Saidai Atiku, da Peter Obi sun goyi bayanta

Ji labarin Ushie Uguamaye, ‘Yar bautar kasa data tayarwa da gwamnatin Tarayya hankali saboda sukar Gwamnatin Tinubu, Saidai Atiku, da Peter Obi sun goyi bayanta

Duk Labarai
Ƴan Najeriya na ta musayar yawu dangane da makomar Ushie Uguamaye mai yi wa ƙasa hidima mazauniyar birnin Legas, tun bayan da ta yi zargin fuskantar barazana sakamakon kalamanta da ta yi a shafinta na tiktok inda ta soki gwamnatin Bola Tinubu. Tuni dai jagororin adawa na Najeriya da kuma ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin bil'adama suka nemi da hukumar yi wa ƙasa hidima ta NYSC ta tabbatar da cewa babu abin da ya samu Ushie Uguamaye. Ita dai hukumar ta NYSC ba ta ce uffan ba dangane da zargin barazanar da Ushie Uguamaye ta yi. Me Ushie Uguamaye ta faɗi? A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na tiktok ranar Asabar, Ushie Rita Uguamaye ta bayyana damuwa kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi a Najeriya inda ta nuna takaicinta kan yadda jajircewa ke neman zama aikin banza. Ta kuma fit...