Tuesday, July 7
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Falalar Goma na karshe daga bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Falalar Goma na karshe daga bakin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Duk Labarai
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya kuma shugaban hukumar Hizba ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce duk da cewa dukkannin ranaku da dararen watan Ramadan na da falala amma kwanaki 10 na ƙarshen watan sun fita daban. "Goman ƙarshe na da wasu abubuwa guda uku masu muhimmancin kuma wannan ne ma ya sa ake fifita goman ƙarshen a kan goman farko da na tsakiya." In ji Sheikh Daurawa. Allah ya yi rantsuwa da darare 10: Na farko dai Allah ya yi rantsuwa da su inda a cikin Alƙur'ani ya ce Wal Fajr, Wa Layalil A'shar. Malamai sun ce wannan na nuni da kwanakin ƙarshe na Ramadan ko kuma goman farko na watan Zulhijja. Daren Laylatul Qadr ya faɗo a goman ƙarshe: Abu na biyu a cikin wannan watan akwai daren Laylatul Qadr. Idan mutum ya yi dace a daren 21 ko 23 ko ...
Kuma Dai:Akwai yiyuwar shugaba Tinubu zai sake dakatar da wani Gwamnan Nan Najeriya da sake saka dokar Ta baci a jiharsa

Kuma Dai:Akwai yiyuwar shugaba Tinubu zai sake dakatar da wani Gwamnan Nan Najeriya da sake saka dokar Ta baci a jiharsa

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saka dokar Ta baci a jihar Osun kamar yanda ya saka a jihar Rivers. Sakataren jam'iyyar APC, Ajibola Basiru ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace a jihar Osun an samu dakile ayyukan kananan hukumomi. A jiya ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamnan jihar, Simi Fubara da mataimakinsa da majalisar jihar.
Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakinsa daga mukaminsu

Da Duminsa: Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakinsa daga mukaminsu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers. Ya bayyana hakane a bayanin da yayi da yammacin yau na Talata inda ya sanar da dakatar da Gwamna Simi Fubara. Hakanan kuma Shugaban kasar ya sanar da dakatar da mataimakin gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Odu da duka 'yan majalisun jihar. Dakatarwar an yi ta ne na tsawon watanni 6. An dai samu fasa bututun man fetur a jihar ta Rivers har kusan aau biyu inda shugaba Tinubu yace babu shugaba me hankali da zai ci gaba da kallon wannan abu na faruwa. Shugaban yace ya baiwa sojoji Umarnin su tabbatar an samu tsaron dukiya da lafiyar jama'a a jihar
Kalli Bidiyo: A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita

Kalli Bidiyo: A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita

Duk Labarai
A Sati Idan Na Yi Buge-Bugena Ina Samun Naira Milyan 30, Ka Gaya Min Wane Muƙami Za A Ba Ni A Gwamnati Wanda Zai Rƙe Ni, Cewar Mawaƙi Ali Jita. Kalli Cikakkiyar Hirar da aka yi dashi: https://www.tiktok.com/@freedomradionigeria/video/7482070766842858807?_t=ZM-8un9GUPuTX3&_r=1 Me za ku ce? Daga Abubakar Shehu Dokoki ...
Zan bayyana fitattun mutune bakwai da na taɓa soyayya da su a Najeriya – Bobrisky

Zan bayyana fitattun mutune bakwai da na taɓa soyayya da su a Najeriya – Bobrisky

Duk Labarai
Shahararren ɗan daudun nan, Bobrisky, ya bayyana cewa ya taɓa yin soyayya da fitattun mutane bakwai a Najeriya a cikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta. Bobrisky, wanda aka san shi da halayensa masu jan hankali da faɗin albarkacin bakinsa, ya yi wannan bayani ne yayin da yake bayani kan cin amana da suka tilasta masa ficewa daga ƙasar. Jaridar The Nation ta rawaito cewa Bobrisky ya kuma yi alkawarin fallasa sunayen waɗanda ya ke magana a kansu, yana mai kwatanta su da “munafukai” a cikin masana’antar nishadi ta Najeriya. “Lokaci yana zuwa da zan bayyana sunayen fitattun mutune bakwai da na taɓa yin soyayya da su a Najeriya. Lokaci yana zuwa da zan fallasa munafukai a wannan ƙasa”, in ji shi. A cikin bidiyon, Bobrisky ya yi nazari kan suka da ya fuskanta daga wasu ...
Jam’iyyar SDP jam’iyyar karyace kanwar APC ce shiyasa kuka ga ‘yan APC ne kadai ke ta tururuwar shiga cikinta>>Inji Buba Galadima

Jam’iyyar SDP jam’iyyar karyace kanwar APC ce shiyasa kuka ga ‘yan APC ne kadai ke ta tururuwar shiga cikinta>>Inji Buba Galadima

Duk Labarai
Babban dan siyasa, Buba Galadima ya bayyana cewa, jam'iyyar SDP kanwar jam'iyyar APC ce, kuma za'a yi amfani da itace dan murkushe 'yan Adawa. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace idan aka lura yawanci 'yan APC ne ke komawa cikin jam'iyyar. Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne dai ya fara komawa jam'iyyar SDP wanda daga baya aka samu da yawa suka bishi cikin jam'iyyar.
Shahararriyar ‘yar fim din kudu, Destiny Etiko da aka saba gani sanye da kaya tsirara-tsirara ta yi bayanin dalilin da ya sa ta sanya Hijabi a cikin watan Azumi

Shahararriyar ‘yar fim din kudu, Destiny Etiko da aka saba gani sanye da kaya tsirara-tsirara ta yi bayanin dalilin da ya sa ta sanya Hijabi a cikin watan Azumi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Turaruwar fina-finan Kudu, Destiny Etiko da aka saba gani sanye da kaya tsirara-tsirara a cikin watan Azumi sai gata sanye da Hijabi. Abin ya baiwa masoyanta mamaki inda akai ta tambayarta menene dalili. A cikin wani bidiyo data wallafa a shafinta na sada zumunta, ta fadi daliinta na yin hakan. Tace wani fim ne ta fito a ciki a matsayin bahaushiya, shiyasa ake ta ganinta sanye da Hijabi kwana biyu.
Allah ko a Lahira karkaba mijina matan Hurul ayn kodaya sabida za’a iya samun matsala, wlh na tsani kishiya>>Inji Fatima

Allah ko a Lahira karkaba mijina matan Hurul ayn kodaya sabida za’a iya samun matsala, wlh na tsani kishiya>>Inji Fatima

Duk Labarai
Wata Matashiya me suna Fatima ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta inda take wa mijinta fatan ko a Lahira kada Allah ya baiwa mijinta Hurul ayn. Ga abinda ta rubuta kamar haka: "Allah ko a Lahira karkaba mijina matan Hurul ayn kodaya sabida za'a iya samun matsala, wlh na tsani kishiya" Da yawa dai sun mayar mata da martanin wannan addu'a bata dace ba.
Kaso 90 cikin 100 na Kiristocin da ake ķķàshèwà a Duniya a Najeriya ake ķķàshèsu, Najeriya ta kasa baiwa Kiristoci kariya dan haka zamu Kakaba mata Takunkumi>>Inji Kasar Amurka

Kaso 90 cikin 100 na Kiristocin da ake ķķàshèwà a Duniya a Najeriya ake ķķàshèsu, Najeriya ta kasa baiwa Kiristoci kariya dan haka zamu Kakaba mata Takunkumi>>Inji Kasar Amurka

Duk Labarai
Majalisar kasar Amurka ta baiwa shugaban kasar, Donald Trump shawarar ya kakabawa Najeriya takunkumi saboda yawan kashe kiristoci da ake yi a kasar. Majalisar ta cimma wannan matsayane bayan samun bayanai daga wani bincike da aka gudanar da yake nuna cewa kaso 90 na kiristocin da ake kashewa a Duniya a Najeriya ne hakan ke faruwa. Majalisar ta kasar Amurka ta zargi Najeriya da kasa daukar matakan da suka kamata dan baiwa Kiristocin kariya daga hare-haren ta'addanci dake yin sanadiyyar mutuwarsu. Saidai a martanin Gwamnatin Najeriya tace wannan magana ba gaskiya bace. Sanarwar da ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta fitar ta hannun kakakinta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya bayyana cewa, tabbas akwai matsalar tsaro a Najeriya. Amma ba wani addini daya aka ware shi k...
Hukumar babban birnin tarayya, Abuja ta kwacewa PDP filinta da babban Ofishinta na kasa dake Abuje ke gine

Hukumar babban birnin tarayya, Abuja ta kwacewa PDP filinta da babban Ofishinta na kasa dake Abuje ke gine

Duk Labarai
Hukumar kula da babban birnin Tarayya, Abuja, FCTA ta kwace filin hedikwatar jam'iyyar PDP dake Abuja. A takardar kwace filin da hutudole ya karanta, hukumar FCTA tace PDP taki biyan harajin da ya kamata ta biya na kan filin kusan tsawon shekaru 20 da suka gabata kenan. Kuma tun shekarar 2023 ake ta tunatar da PDP game da biyan harajin amma ta yi kunnen uwar shegu. Dan hakane yanzu an kwace filin ya zama mallakin hukumar FCTA din dake Abuja.