Wednesday, December 24
Shadow

Author: Bashir Ahmed

FIFA ta goge Fastar gasar cin kofin Duniya ta 2026 data wallafa a shafinta bayan data sha suka saboda babu hoton Ronaldo a fastar

FIFA ta goge Fastar gasar cin kofin Duniya ta 2026 data wallafa a shafinta bayan data sha suka saboda babu hoton Ronaldo a fastar

Duk Labarai
Hukumar kwallon kafa ta Duniya ta goge fastar gasar cin kofin Duniya na 2026 daga shafinta na sada zumunta bayan data wallafa shi amma ta sha suka saboda babu hoton Ronaldo a fastar. Magoya bayan Ronaldo da yawa ne suka rika sukar FIFA a comment bayan wallafa fastar, kuma da sukar ta yi yawa, dole FIFA ta goge hoton.
Duk Wanda yayi farin ciki da zuwan Amurka Najeriya, ya kafurta>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Wanda yayi farin ciki da zuwan Amurka Najeriya, ya kafurta>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Babbab malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, duk wanda yayi Murna da zuwan Amurka Najeriya ya kafurta. Ya bayyana hakane a wajan wa'azinsa da yake yi a masallacin Sultan Bello ranar Juma'a. Malam yace ko zuwan Amurkar da tace zata zo ta ceci Kiristoci ba abinda zai kawota kenan ba, suna neman inda zasu saci man fetur ne. Malam ya kara da cewa, niyyar Kisa kawai ta isa ta kai mutum zuwa wuta. Malam yace akwai hadisi dake cewa, a karshen Duniya, za'a rika kashe mutum wanda yayi kisan bai san dalili ba hakanan wanda aka kashe shima bai san dalilin ba. Malam yace kuma Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)yace da wanda yayi kisan da wanda aka kashe duka 'yan wuta ne. Malam yace hadda wanda yake son a rika yin kisan, misali masu son a shiga daji a kashe k...
Da Duminsa: Allah Sarki, Sojannnan Muhammad dake ta neman a bashi damar ya ajiye aiki aka ki bashi dama har ya fito yayi Bidiyo ya gayawa Duniya, an kamashi an daure a Guard Room

Da Duminsa: Allah Sarki, Sojannnan Muhammad dake ta neman a bashi damar ya ajiye aiki aka ki bashi dama har ya fito yayi Bidiyo ya gayawa Duniya, an kamashi an daure a Guard Room

Duk Labarai
Rahotannin da muke samu na cewa, sojan Najeriya, Muhammad da ya fito ya gayawa Duniya cewa, yana ta so ya ajiye aiki amma na sama dashi sun ki bashi dama, an kamashi an daureshi a Guard Room. Wani na kusa dashi me sunan Mustapha Muhammad ne ya bayyana hakan inda yace matar sojan ke gaya masa halin da mijinta ke ciki. Sojan dai ya bayyana cewa wata matsalar iyali ce tasa yake son ajiye aikin nasa inda yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Ministan tsaro da shuwagabannin soji da majalisar tarayya su taimaka masa kan maganar ajiye aikin.
Hukumar ‘Yansandan jihar Nasarawa tacw ba masu Ghàrkùwà da mutanene aka gani ba, Màfàràutà ne daliban makaranta suka gani suka firgitasu sun dauka Masu Ghàrkùwà da mutanene

Hukumar ‘Yansandan jihar Nasarawa tacw ba masu Ghàrkùwà da mutanene aka gani ba, Màfàràutà ne daliban makaranta suka gani suka firgitasu sun dauka Masu Ghàrkùwà da mutanene

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan jihar Nasarawa ta musanta cewa an yi garkuwa da wasu dalibai a makarantar Peter's Foundation Secondary School dake Rukubi Karamar hukumar Doma. Kakakin 'yansandan jihar, Ramhan Nansel ta bayyana cewa ta yi magana da shugaban makarantar yace labarin karyane. Shugaban makarantar yace dalibansa na wasa ne sai suka ga mutane da bindigu, inda suka ruga wajan malaminsu suna cewa ga masu garkuwa da mutane. Yace malamin ya ce musu su tafi aji, inda acan suka rika gayawa abokan karatunsu cewa masu garkuwa da mutane sun shigo makarantarsu. Daga nan ne labarin ya yadu, saidai yace maganar gaskiya, mafarauta ne dauke da bindigu ba masu garkuwa da mutane bane. A wani Bidiyo da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta, an ga makarantar a kidime inda iyaye suka rika zuwa dan...
Kalli Bidiyon yanda aka Gurfanar da wasu Qàrùwàì a kotu, Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ga Tshàgyèràn daji can an barsu suna cin kàrènsù ba babbaka

Kalli Bidiyon yanda aka Gurfanar da wasu Qàrùwàì a kotu, Lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa ga Tshàgyèràn daji can an barsu suna cin kàrènsù ba babbaka

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Edo sun ce Karuwai ko mata masu zaman kansu ne da yawa aka kama aka gurfanar a gaban kotu saboda aikata aikin karuwanci. A Bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga yanda matan masu zaman kansu ke rufe fuska yayin da suka yi layi suka shiga cikin kotun. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1991805516075655192?t=G-76xlif9HE_Dx7PkdXpEw&s=19 Kalli Bidiyon anan Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu ke ganin cewa, 'yan Bindiga ne ya kamata ace an kamo ana hukuntawa kamin karuwan.
Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, An samu rahoton sake Dawuke Dalibai a jihar Nasarawa

Kalli Bidiyon: Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, An samu rahoton sake Dawuke Dalibai a jihar Nasarawa

Duk Labarai
Rahotannin dake fitowa daga jihar Nasarawa na cewa, an sake yin garkuwa da dalibai da ba'a san adadinsu ba a makarantar Peter’s Foundation Secondary School dake Rukubi, a karamar hukumar Doma, Kamar yanda shafin @ChuksEricE suka ruwaito. Rahoton yace 'yan Bindigar sun shiga makarantar ne suka rika zabar daliban da zasu yi garkuwa dasu. A Bidiyon da ya bayyana an ga iyaye sun shiga makarantar inda suka rika dauke 'ya'yansu. Tuni hukumomi suka bayar da umarnin Rufe makarantar, kamar yanda rahoton yace. jaridar Sunnews ta tabbatar da rahoton sace daliban inda tace tana kokarin jin ta bakin hukumar 'yansanda ta jihar. jaridar tace wasu shaidu sun tabbatar mata da satar daliban. Hakan na zuwa ne awanni kadan bayan yin garkuwa da dalibai a jihar Naija, hakanan kwanaki kadan ba...
An sake dawukye Dalibai a jihar Naija, Gwamnatin jihar Naija ta tabbatar da hakan saidai tace laifin hukumomin makarantar ne dan Gwamnati ta samu Rahoton hakan zai iya faruwa tace a kulle makarantu

Rahotanni daga jihar Naija na cewa, an sake yin garkuwa da dalibai na makatanta. An sace daliban makarantar St. Mary’s School ce dake Papiri a karamar hukumar Agwara dake jihar ta Naija. Daily Trust tace lamarin ya farune da misalin karfe 2 zuwa 3 na dare. Zuwa yanzu dai ba'a san yawan daliban da aka sace ba. Me magana da yawun gwamnatin jihar Naija, Abubakar Usman ya tabbatar da wannan labari inda yace ana kokarin kubutar da daliban. Saidai ya dora laifin faruwar hakan akan hukumomin makarantar inda yace Gwamnati ta samu rahoton cewa, hakan zai iya faruwa. Kuma ta bayar da sanarwa cewa, a kulle duka makarantu a yankin saidai wannan makaranta taki jin wannan shawara inda suka ci gaba da karatu.
An dakatar da bayar da làsìsìn Màkàmì irin su Bhìndìghà ga ‘yan Najeriya dan su yi amfani da ita wajan kare kansu>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

An dakatar da bayar da làsìsìn Màkàmì irin su Bhìndìghà ga ‘yan Najeriya dan su yi amfani da ita wajan kare kansu>>Inji Hukumar ‘yansandan Najeriya

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta tabbatar da cewa, dokar hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga a Najeriya dan kariyar kai har yanzu tana aiki. Me magana da yawun hukumar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wani martani da yayi game da ikirarin da wani yayi cewa ya mallaki Bindigar AK47. Benjamin yace a doka ko da ana bada lasisi, Bindigar AK47 bata cikin wadda aka amince farar hula su rike. Yace amma a yanzu har yanzu ba'a dage dokar data hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga dan kariyar kai ba. Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda mutane suka rika tambayar to su tsageran daji ina suka samo nasu Bindigun?
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un:Kalli Hotuna Masu tayar da hankali, Sun saki Hotunan Gawar Janar Muhammad Uba da kuma Screenshot na chatin din da yayi da sojoji yana gaya musu inda yake su zo su ceceshi

Kungiyar da ta kaiwa tawagar Brigadier General Muhammad Uba harin kwantan bauna, ta kamashi kuma ta kashe, watau ÌŚWÀP ta saki hoton gawarsa. Hakanan ta saki Hoton Screenshot na WhatsApp Chat da yayi da sojoji inda yake gaya musu inda yake dan su zo su ceceshi, an ga inda yake cewa, Su yi Sauri Chajin wayarsa ya kusa daukewa. Lamarin akwai sosa Zuciya sosai. Wani abin karin bacin rai shine yanda aka ga suna ta dariya suna mai shagube. A hoton an ga Jini yana kwarara daga kunnensa sannan a kafarsa akwai harbin Bindiga.