Yadda ake gurasar fulawa
KALOLIN YADDA AKE GURASA
GURASAR TANDERU
KAYAN DA ZA KI TANADA
Fulawa
Yis
Kantu/ridi
Sikari
gishiriYADDA ZA KI YIKi sami fulawarki ki tankade ki zuba mata yis, ki zuba ruwa ki kwaba, ka da ki kwaba shi da ruwa, ki kwaba shi da dan tauri. Idan kina son Gurasa mai sikari, sai ki zuba sikari a cikin kwabin , idan kuma kina son mai gishiri ne, sai ki zuba gishiri a cikin kwabin. Idan lokacin zafi ne za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so ,awa uku zuwa hudu ya ishe shi ya tashi , amma idan lokacin sanyi ne yakan dade bai tashi ba. Idan kina so ki yi Gurasa da safe, to sai kin kwaba fulawarki tun da daddare, kuma kin nemi wuri mai dumi kin saka kin rufe sosai domin ya tashi. Idan kin tabbatar kwabinki ya tashi , sai ki zuba karare a cikin Tanderu, ki kunna wuta ...