Sojojin Najeriya sun soma fatattakar Làkùràwà daga sassan jihar Kebbi
Rundunar sojin Najeriya ta ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar 'yanbindiga ta Lakurawa da ta ɓulla a wasu sassan jihohin Kebbi da Sokoto na arewa maso yammacin ƙasar.
Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Augie na jihar Kebbi, sun ce sojojin ƙasar sun shiga wuraren da 'yan ƙungiyar suka kakkafa sansanoni tare da lalata su.
Sojojin sun kuma kori Lakurawan a dazukan ƙaramar hukumar, tare da kuɓutar da wasu daga cikin dabbobin da masu gwagwarmaya da makaman suka sace.
Matakin na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da 'yan ƙungiyar suka yi artabu da mutanen gari Mera na yankin ƙaramar hukumar, tare da kashe mutum 15 da sace shanu masu yawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Augie, Hon Yahaya Muhammad Augie, ya shaida wa BBC cewa bayan dakarun ƙasar sun soma ƙaddamar da hare-hare kan ƙungiyar, yanzu ha...








