Saturday, January 4
Shadow

Author: Auwal Abubakar

ALHAMDULILLAH: Jama’ar Gari Sùn Yi Kukañ Kuŕa Sùñ Fataťtaki ‘Ýàñ Bìnďìga A Jihar Ķatsina, Tare Da Kwato Shanu

ALHAMDULILLAH: Jama’ar Gari Sùn Yi Kukañ Kuŕa Sùñ Fataťtaki ‘Ýàñ Bìnďìga A Jihar Ķatsina, Tare Da Kwato Shanu

Duk Labarai
Cikin ɗaren jiya ƴan ta'àďďa sun shiga ƙauyen Gidan Boka dake ƙaramar hukumar Malumfashi, sun ɗauki mutum ɗaya tare da kore shanu, amma jama'an gari sunmyi kukan kura sun bi su suka yi ta fafatawa da da su da bindìģùñ su na gida ƙarshe har saida suka fatat'taki ƴan ta'aďďan kuma suka kwace shanu da mutanan da suka ɗauka. Shugaban hukumar tsaro ta ƴan sanda na garin Malumfashi S.P: Bello Umar, ya yi yabo da jinjina ga wannan jarumta da mutanan garin suka nuna wajen yin ƙoƙarin iya fito na fito da ƴan ťa'aďďan, kuma suka fafata da su har suka samu nasara ta kwace shanun da suka ɗauka da ceton mutumin da suka ɗauka duk a cikin daren, tun kafin ƴan sanda su kai ga isowa. Haƙiƙa wannan ba ƙaramar nasara bace kuma abun koyi ne a gare, mu dukka al,ummah, nadade ina fadi mutane murinƙa ƙokar...
Nabil Shinkafi Ya Zama Shugaban Matasan Arewa

Nabil Shinkafi Ya Zama Shugaban Matasan Arewa

Duk Labarai
Nabil Shinkafi Ya Zama Shugaban Matasan Arewa Manyan kungiyoyin Arewacin Nijeriya masu zaman kansu, sun tabbatar da shugabancin Matashin ɗan kasuwa Nabil Shinkafi, a matsayin Shugaban Matasan Arewa, inda suka bashi takardar shedar shugabanci (Certificate) kuma sun karrama shi da Numbar yabo. Manyan kungiyoyin Matasan Arewa Youth Leadership groups sun karrama matashin ɗan kasuwar Nabil Shinkafi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagorori masu son ci gaban mutanen Arewacin Nijeriya, ta hanyar samar masu da abin yi; da kuma inganta iliminsu. An yi taron karrama matashin a jiya Talata, a babban birnin tarayya Abuja.
Kalli Bidiyon karya da ya nuna Momi Gombe da Umar M. Sharif sun Rungumi Juna

Kalli Bidiyon karya da ya nuna Momi Gombe da Umar M. Sharif sun Rungumi Juna

Umar M. Sharif
Wani Bidiyo na karya wanda aka yi Editing ya nuna yanda Wai mawaki Umar M. Sharif da abokiyar aikinsa,Momi Gombe sun rungumi juna. Bidiyon dai ya dauki hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta saidai da yawa sun fahimci cewa karyane. https://www.tiktok.com/@m.o.m.e.e.gombe/video/7410853116750335238?_t=8pc3cJSaebm&_r=1 A wannan zamani dai ana amfani da fasahar AI wajan hada abubuwan da a baya ake ganin kamar ba zasu iya haduwa ba.
NLC ta buƙaci a gaggauta sakin shugabanta

NLC ta buƙaci a gaggauta sakin shugabanta

Duk Labarai
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta buƙaci hukumomin ƙasar su gaggauta sakin shugabanta ba tare da wani sharaɗi ba. Da safiyar ranar Litinin ne hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta kama Mista Ajaero a filin jirgin saman Abuja, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya domin halartar taron ƙungiyar kwadago TUC, ta Birtnaiya Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ƙungiyar, Benson Upah ya fitar, ya ce ta sanya rassanta na jihohi da manyan ƙungiyoyin da ke ƙawance da ita cikin shirin ko-ta-kwana, kan lamarin da ta kira mai ''tayar da hankali''. “Ƙungiyarmu ba za ta zuba ido tana ganin ana tozarta shugabanni da mambobinta ba, don haka muke buƙatar a gaggauta sakin Kwamared Ajaero, ba tare da gindaya kowane irin sharaɗi ba'', kamar yadda sanarwar ta ...
Kwankwaso ba shi da wani muhimmanci a siyasar Najeriya – PDP

Kwankwaso ba shi da wani muhimmanci a siyasar Najeriya – PDP

Duk Labarai
Jam’iyyar PDP ta mayar da martani kan kalaman da sanata Rabi’u Kwankwaso, dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 ya yi wanda ya yi iƙirarin cewa jam’iyyar PDP ba ta da wani tasiri a siyasar Najeriya, inda ya ce jam’iyyar ta mutu. A ranar Asabar ne dai Sanata Kwankwaso yayin buɗe ofishin jam'iyyar NNPP na jihar Katsina, jagoran Kwankwasiyyar ya zargi jam'iyyar PDP da APC mai mulki da jefa kanta cikin abin da ya kira ''halaka''. A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar na ƙasa Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi, PDP ta bayyana Kwankwaso a matsayin "mara muhimmanci a siyasar Najeriya" tare da zargin sa da son kai. Ologunagba, ya soki kalaman Kwankwaso, inda ya nuna cewa jam’iyyar NNPP a karkashin shugabancin Kwankwaso na ƙoƙarin gina kanta ne a ...
Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus – Rundunar sojin Najeriya

Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus – Rundunar sojin Najeriya

Duk Labarai
Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami'anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala. A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci "da ya yi wa aikin katutu". A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan. A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta. Sanarwar ta kara da cewa: "Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin...
DSS ta kama shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero

DSS ta kama shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero

Duk Labarai
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero. Kungiyar ta NLC ta bayyana a shafin sada zumuntarta na X cewa an kama shugaban nasu ne a yau, Litinin da safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja. Ƙungiyar ta NLC ta ce "har yanzu ana ci gaba da cin zarafin ma'aikatan Najeriya yayin da shugabanmu Joe Ajaero ya shiga hannun jami'an DSS da safiyar yau." "Jami'an sun kama shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Birtaniya." NLC ta ce yanzu haka ana tsare da shugaban a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA. A baya dai, shugaban NLC ɗin ya mutunta gayyatar da ƴansanda suka yi masa kan zarginsa da hannu a tallafawa ayyukian ta'addanci, da kuma cin amanar ƙasa
An damƙa wa kowane gwamna tallafin shinkafa ban da na Kano – Kwankwaso

An damƙa wa kowane gwamna tallafin shinkafa ban da na Kano – Kwankwaso

Duk Labarai
Jagoran jam'iyyar NNPP, mai mulkin jihar kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana takaicinsa kan yadda ya ce gwamnatin tarayya ta raba kayan tallafin shinkafa ga Jihohi 35 duk ta hannun Gwamnonin su, amma ban da Jihar Kano. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Jagoran Kwankwasiyyar ya yi zargin cewa gwamnatin tarayyar ta miƙa kason jihar Kano hannun jiga-jigan jam'iyyar APC, wanda a cewarsa hakan ya saɓa wa dimikraɗiyya. ''Wannan babban cin fuska ne ga dimokradiyya da kuma tsarin mulkin ƙasar mu. Wannan mataki dai nuna ɓangaranci ne da ya wuce gona da iri,'' in ji jagoran jam'iyyar NNPP. Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasar ya gagguata dakatar da abin da ya kira karan-tsaye wa tsarin dimikraɗiyyar ƙasar. Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP ya kuma nun...