Friday, July 3
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda ‘yar uwar Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tace Bakin cikin kama El-Rufai ne ya kai Mahaifiyarsu lahira

Allah Sarki Kalli Bidiyon: Yanda ‘yar uwar Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai tace Bakin cikin kama El-Rufai ne ya kai Mahaifiyarsu lahira

Duk Labarai
Wata 'yar uwar Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta fito tana kuka inda tace bakin cikin kamashine ya Qasheta. Ta bayyana cewa, El-Rufai shi ne yakewa Mahaifiyarsu komai hadda wanka dan haka rashinsa ya sakata cikin damuwa. Ta zargi cewa, gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ne ya kama El-Rufai kuma koma menene suka yi, tare suka yi. https://twitter.com/i/status/2037676823069487281 A jiya ne dai Mahaifiyar El-Rufai ta rigamu gidan gaskiya a kasar Egypt. Hakakan rahotanni sun bayyana cewa, Tuni an saki Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.
Kalli Bidiyon: ‘Yan Arewa sun dauki hankula bayan da aka gansu kwance a harabar babban masallacin Abuja bayan da suka je babban taron jam’iyyar APC na kasa

Kalli Bidiyon: ‘Yan Arewa sun dauki hankula bayan da aka gansu kwance a harabar babban masallacin Abuja bayan da suka je babban taron jam’iyyar APC na kasa

Duk Labarai
Wasu 'yan Arewa da suka je babban taron jam'iyyar APC na kasa a Abuja, an gansu a kwance a harabar masallacin Abuja. Da yawa sun yi Allah wadai da wannan abu inda wasu ke cewa Abin kunyane ga APC din ace mutanen ta ba zata iya sama musu wajan kwana ba. https://twitter.com/i/status/2037490851476017519
Da Duminsa: Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa duk da yana APC, yawa Atiku Alkawarin bashi kudi dan yayi yakin neman zaben 2027

Da Duminsa: Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa duk da yana APC, yawa Atiku Alkawarin bashi kudi dan yayi yakin neman zaben 2027

Duk Labarai
created by photogrid Rahotanni daga kafar peoplesgazette sun bayyana cewa, Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a Saudiyya. Kafar tace wata majiya ta gaya mata cewa, Gwamna Sule yawa Atiku Alkawarin zai bashi kudi yayi yakin neman zabe sannan kuma ya bashi tabbacin shine zai ci jihar Nasarawa a zaben 2027. Kafar tace a yanzu Atiki bashi da isassun kudin da zai yi yakin neman zabe bayan da a baya yayi takara har sau 4 ba tare da nasara ba. Sannan a zamanin Mulkin Buhari an durkusar da kamfaninsa na Intel.
Kalli Bidiyon yanda matan unguwa suka taru suka hana a yanke musu wutar Lantarki, Har dan NEPA din ya hau saman Tsani zai yanke wutar, Aka kado dashi

Kalli Bidiyon yanda matan unguwa suka taru suka hana a yanke musu wutar Lantarki, Har dan NEPA din ya hau saman Tsani zai yanke wutar, Aka kado dashi

Duk Labarai
Bidiyon yanda wasu matan yarbawa a legas suka hana dan NEPA yanke musu wuta ya dauki hankula sosai. An ga dan NEPAN na shirin hawa saman Pol ya yanke wuta amma matan suka ce basu yadda ba, dole ya hakura. https://twitter.com/i/status/2037412356376928579 A wani Bidiyon na daban kuma wanda ke da alaka da wannan an ga dan NEPA din ya hau saman Pol amma aka kado dashi kasa., https://twitter.com/i/status/2037329438833074379
Da Duminsa: An bayyana halin da Sheikh Khalifa Sani Zaria ke ciki

Da Duminsa: An bayyana halin da Sheikh Khalifa Sani Zaria ke ciki

Duk Labarai
Biyo bayan rade-radin da ake ta yayatawa cewa Babban Malamin Addinin Islama dake tsare a hannun Hukumomin Najeriya, Sheikh Khalifa Sani Zaria ya rasu. Rahotanni daga PRNigeria sun tabbatar da cewa malam yana nan da ransa bai rasu ba. Wata majiya daga Hukumar ta DSS ce ta bayyanawa PRNigeria hakan inda tace malam nanan Hukumomin soji dana DSS na masa tambayoyi. Ana zargin Malam da karbar Naira Miliyan 2 ne dan yiwa sojan dake shirin yiwa shugaba Tinubu juyin Mulki Addu'a, saidai iyalan malam sun karyata wannan zargi.
Kalli Bidiyon: Jarumar fina-finan Hausa, Auta tawa Kannywood tonon Silili inda tace duka manyansu da yaransu ‘yan Isqa ne in banda ‘yan kadan

Kalli Bidiyon: Jarumar fina-finan Hausa, Auta tawa Kannywood tonon Silili inda tace duka manyansu da yaransu ‘yan Isqa ne in banda ‘yan kadan

Duk Labarai
Jarumar Fina-finan Hausa me suna Auta tawa masana'antarsu Tonon Silili inda tace duka manyan da yaransu da producers duk 'yan iskane in banda 'yan kadan. Tace manyan masu yin fina-finai wanda fina-finan su yanzu ake yayi da yawansu idan zasu tona musu asiri, mutane ba zasu gansu da mutunci ba. Ta yi gargadin masu tsokanarta su daina idan ba haka ba zata yi tonon Asiri da kiran suna wanda ba zaiwa kowa dadi ba. https://www.tiktok.com/@autamumunata/video/7621150666802711828?_r=1&_t=ZS-950ovNBm01p&sp_source=7537614245375297080
Bidiyo ya bayyana inda aka ce Sadiya Haruna ce ke fada da wata a Kasar Saudiyya

Bidiyo ya bayyana inda aka ce Sadiya Haruna ce ke fada da wata a Kasar Saudiyya

Duk Labarai
Wani Bidiyo ya bayyana inda aka yi ikirarin cewa, Sadiya Haruna ce ake fada da ita a kasar Saudiyya. Saidai Sadiya ta fito ta karyata Bidiyon inda tace Allah ya isa bata yafe ba. Tace mijinta ya kirata akan Bidiyon hakanan mahaifiyarta ma ta kirata dan haka wanda ya wallafa Bidiyon bata yafe masa ba. https://www.tiktok.com/@sayyada_sadiya_haruna/video/7621486374109072656?_r=1&_t=ZS-950gV18fbdo&sp_source=7537614245375297080