Kalli hoton Maryam Yahya da Masoyanta ke sam barka suna cewa ta ciko ta yi Bulbul
Tauraruwar Fina-finan, Maryam Yahya kenan a wannan kayataccen hoton nata da masoyanta da dama suka yaba.
Maryam ta saka hoton a shafinta na Instagram inda aka ganta zaune a wani gidan sayar da abinci.
Saidai masoyanta da yawa hakalinsu ya kai ne kan kibar da Maryam ta yi.
Da yawa dai sun yaba da Masha Allah, inda wani yace:
"Kin cika kin yi kyau, Masha Allah"
"Shi kuwa wani cewa yayi, anya a wannan harkar babu kari?"
"Wani kuma cewa yayi, Kai Maryam Gaskiya kin ciko"