Abinda Gwamnatin Kano ta yi, Adalci ne kan rashin adalcin da aka min a baya>>Sarki Muhammad Sanusi II ya gayawa jami’an tsaro
Me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ya bayyanawa jami'an tsaro cewa abinda Gwamnatin jihar Kano ta yi na sauke Aminu Ado Bayero ta mayar dashi kan kujerar sarautar Kano, Adalci ne.
Ya bayyana hakane a wani zama da suka yi shi da shuwagabannin jami'an tsaro na Sojoji, DSS, da 'yansanda.
Jami'an tsaron sun bayyanawa sarkin cewa, akwai dokar data ce a dakatar da mayar dashi akan kujerar sarautar Kano.
Saidai ya bayyana musu cewa, shi bai san da hakan ba, bai ma san da zaman kotun ba, kotun yanar gizo ce.
A lokacin da ya karbi takardar sake nadashi sarautar Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, dama a baya ya fada, Allah ne me bayar da mulki kuma ya karba a lokacin da ya so.