Yadda ake lemun kwakwa
Abubuwan da ake bukada dan hada lemun kwakwa:
Kwakwa Kwallo daya:
Madarar Ruwa gwagwani daya
Madarar Gari kofi daya.
Suga babban cokali 5.
Citta Kwaya daya, danya ba busassa ba.
Kanunfari kwaya 6
Kankarar ruwa me sanyi.
Yanda za'a hada:
A fasa kwakwar a juye ruwa a kofi ko mazubu me kyau, a cire bawon kwakwar a yayyankata kananan-kanana. A zuba a blender a zuba ruwan kwakar a ciki a markada.
Idan ba'a da blender ana iya yin amfani da turmi ko a kai markade.
A zuba cittar da Kanunfarin da aka tanada.
A zuba sukarin da aka tanada.
A zuba masarar garin da aka tanada.
A markade ko a yi blending ko a daka har sai yayi sosai duk sun hade. Sai a tace.
A zuba madarar ruwan da aka tanada.
Idan ana so ana iya kara sukari.
Sai a saka kankara me sanyi...