Barka da safiya matata insha Allah, wataran da hannuna zan tasheki daga bacci.
Barka da safiya matata insha Allah, wataran a gado daya zamu kwana.
Barka da safiya matata insha Allah, wataran akan kirjina bacci zai kwasheki.
Barka da safiya matata insha Allah ina miki fatan samun alkhairin wannan yini.
Salam Masoyiyata, na kwanta da sonki na tashi dashi, ina fatan kema kin tuna dani.
Salam Masoyiyata ina sonki a ko da yaushe, yanzu ma sonki ne ya tasheni, ina miki fatan alkhairin wannan jini.
Masoyiyata na yi mafarkinki, kema kin yi mafarkina kuwa?
Salam Farkawa na yi, na yi sallar Asuba, na yi zikirin safiya, na dauko abincin kari zanci, sai naji bana jin dandanonsa a bakina, ina ta tunane-tunane sai na tuna ashe muryarki ce da ban ji ba.
Salam Inawa 'yar Alkhairi f...