Addu’a ga masoyiyata
Ina fatan Allah ya haskaka rayuwarki.
Fatana shine ki fi kowa a tsakanin sa'anninki.
Allah yasa mu zama mata da miji.
Allah yawa soyayyarmu Albarka ta yanda zamu yi aure mu haifi 'ya'ya masu Albarka.
Ina fatan Allah ya kareki daga sharrin makiya, Mahassada da kambun baka, masoyiyata kada ki manta da karanta falaki da Nasi safe da yamma.
Kina da kyau, dan haka nasan akwai mahassada da masu mugun baki, fatana shine Allah ya kareki daga dukkan sharrinsu.
Kina da Basira, Fatana shine Allah ya kareki daga sharrin mahassada.
Babyna ki kasance kullun cikin zikiri, zaki rabauta daga sharrin shedan la'ananne.
Insha Allahu duk inda zaki shiga sai Allah ya hadaki da masoya na gaskiya.
Babban burina shine inga Allah ya daukakaki a tsakanin sa'anninki.
Masoyiyata Ki rike s...