Tuesday, January 21
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ji Abinda dan gidan Sarki Muhammad Sanusi II, Adam Sanusi yace bayan hukuncin kotu a yau wanda ya jawo cece-kuce

Ji Abinda dan gidan Sarki Muhammad Sanusi II, Adam Sanusi yace bayan hukuncin kotu a yau wanda ya jawo cece-kuce

Kano
Dan gidan me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, Adam Muhammad Sanusi wanda aka fi sani da Ashraf ya bayyana godiya ga Allah bayan hukuncin kotu a yau. https://twitter.com/Adam_L_Sanusi/status/1803838627111199087?t=kdRE0ZRuHq-RtRIePMxwNg&s=19 Kotu dai ta soke sabuwar dokar data soke sabbin masarautun Kano wanda lamarin ya kawo rudanin fahimta tsakanin masoyan Sarki Muhammad Sanusi II da Masoyan Sarki Aminu Ado Bayero. https://twitter.com/Adam_L_Sanusi/status/1803793847878574563?t=D9YU71bHREHJIdEAO8lqjw&s=19 Ya kara da cewa babansa, Watau sarki Sanusi yana nan dai kuma shine me gaskiya.
MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN’UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3

MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN’UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3

Duk Labarai
MASU GARKUWA SUN BIDIGE MUTUM DAYA KAI MUSU KUDIN FANSAR YAN'UWAN SA NERA MILIYAN 16 DA MASHINA 3. Daga Shuaibu Abdullahi Rahotanni sun tabbatar da cewar matashin da aka tura ya Kai kudin fansar wasu mutane 9 da masu garkuwa suka sace, kudin da ya kai Nera miliyan 16 da babura 3 shima sun halaka shi. City and Crime ta fitar da rahotan cewar masu garkuwa sun fara da bukatar Nera miliyan 30 bayan da suka kwashe Mutanen 9, a Unguwar Iya a Jeren Jihar Kaduna, tun ranar 16, ga watan afurelun wannan shekarar ta 2024. Rahotan ya ce Wani makusanci ne ya tabbatar da manema Labarai cewar masu garkuwan sun daure tare da harbe Abbas, Dan kimanin shekaru 27, a lokaci guda bayan da suka karbe adadin kudaden daya Kai musu. Daya daga cikin wadanda basu garkuwan suka saki, ya ce masu gar...
Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India

Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India

Duk Labarai
Mutane 30 Sun Mutu An Kwantar Da Wasu Gommai a Asibiti Bayan Sun Sha Burkutu a India Aƙalla mutane 30 ne suka rasa rayukan su inda kuma aka kwantar da gommai a asibiti bayan da suka sha wata giya haɗin gida a gundumar Kallakuruchi da ke jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya. Hukumomin Kasar sun ce yawancin waɗanda aka kwantar a asibitin sama da 80 suna fama ne da amai da gudawa da kuma ciwon ciki bayan sun sha giyar ta burkutu a ranar Talata da daddare. An kama jami'ai goma da suka haɗa da wani babban jami'in haraji da Baturen ƴan sanda a kan afkuwar lamarin. Babban minista na jihar ta Tamil Nadu, MK Stalin ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa lamarin ya girgiza shi matuka. Ministan ya kuma sanar da diyyar dala dubu 12 ga iyalan waɗanda suka mutu, su kuwa w...

Kalaman soyayya masu ratsa jiki da jijiyoyin

Kalaman Soyayya
Kece Dandamalin zuciyata. Ina sonki kuma ina fatan in aureki. Soyayyarki na ratsa jikina kamar yanda ruwan sanyi kewa jiki idan an kwararashi yayin da ake tsaka da sanyi me tsanani. Soyayyarki ta mamayeni kamar yanda manja ke mamaye farar jallabiya yaki fita. Soyayyarki ta yi naso a zuciyata kamar yanda bakin mai kewa kayan bakanike me gyaran mota naso. Na rasa ya akai zuciyata ta kamu da soyayyarki farat daya. Ina kallonki naji cewa na hadu da kalar matar da nake son aure. Kin yi min ta kowane bangare. Soyayyarmu ta yi fadi ta yanda babu littafin da zai dauki bayaninta. Ina sonki kamar ke kadaice mace a Duniya, kin zamar min sarauniyar mata wadda idan na rasata na yi babban rashin da ba zan iya maye gurbinsa ba. Saboda soyayyar da nake miki, ko mi kika min da...
Yanzu-Yanzu: Yawan alhazan da suka ŕàsu saboda tsananin zafi a kasar Saudiyya sun karu zuwa 1081

Yanzu-Yanzu: Yawan alhazan da suka ŕàsu saboda tsananin zafi a kasar Saudiyya sun karu zuwa 1081

Hajjin Bana
A rahoton farko an ji cewa: Tsananin zafi a hajjin bana alhazai 900 ne suka rasu! Kamfanin dillancin labarai na AFP bayan tattara bayanai daga ofisoshin jakadancin ƙasashe na cewa aƙalla alhazai 922 ne suka mutu yayin aikin Hajjin, akasari saboda tsananin zafi da aka yi fama da shi. Lokacin Hajji a kasar Saudia. 2024 Alkaluman sun tabbatar da cewa Aƙalla 'yan ƙasar Masar 1,400 ne aka ba da rahoton sun ɓace cikinsu har da 600 da suka mutu, kamar yadda wasu jami'an difilomasiyya suka shaida wa AFP. Saidai sabon rahoton daga AFP ya tabbatar da cewa yawan alhazan da suka mutu sun kai 1081.