Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyo: Crypto Halal Ne, Ya Halatta Ana Karatu Na Musamman Akansa, Ana Diploma Da Digiri Akansa. Masu Cewa Haram Ne Ba Su San Shi Ba Ne, Inji Sheik Ibrahim Khalil

Kasuwanci
Crypto Halal Ne, Ya Halatta Ana Karatu Na Musamman Akansa, Ana Diploma Da Digiri Akansa. Masu Cewa Haram Ne Ba Su San Shi Ba Ne, Inji Sheik Ibrahim Khalil. Malamin ya bayyana hakane a wani wa'azi da ya gudanar. Hakan na zuwane kwana daya bayan da Nazir Ahmad Sarkin Waka yayi cece-kuce da 'yan Cryptocurrency a kafafen sada zumunta.
Ji yanda sojan Najeriya da aka yi gar-ku-wa dashi ya kwace Bin-di-gar maharan ya kubutar da kanshi da sauran mutane

Ji yanda sojan Najeriya da aka yi gar-ku-wa dashi ya kwace Bin-di-gar maharan ya kubutar da kanshi da sauran mutane

Tsaro
Wani sojan Najeriya me mukamin Kyaftin yayi abin yabo inda ya kubutar da kansa da wansu sauran mutane da aka yi garkuwa dasu tare. Sojan me suna Captain J.O. Abalaka Ya kubutar da kansa ne a jihar Kogi bayan da aka yi garkuwa dashi. Lamarin ya farune makon da ya gabata a yayin da sojan ke kan hanyar zuwa Borno inda aka mayar dashi daga Jihar Rivers inda yake aiki. Sojan na cikin motarsa me kirar Toyota Corolla tare da karensa yayin da lamarin ya faru, saidai ya yi nasarar kwace bindigar AK47 daga hannun daya daga cikin 'yan Bindigar inda ya kori sauran. Sojan ya kuka kwace bindiga kirar hannu da sauran wasu abubuwa.
Irin Namijin da nake so shine wanda idan na tambayeshi Naira Miliyan 1 zai bani Miliyan 20>>Inji ‘Yar Fim, Yvonne Jegede

Irin Namijin da nake so shine wanda idan na tambayeshi Naira Miliyan 1 zai bani Miliyan 20>>Inji ‘Yar Fim, Yvonne Jegede

Nishadi
'Yar Fim din kudancin Najeriya, Yvonne Jegede ta bayyana cewa, irin namijin da take so shine wanda idan ta tambayeshi kudi, zai bata fiye da abinda ta tambaya ba tare da ya tambayeta me zata yi dasu ba. Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita. Tace tana son mijin da idan ta tambayeshi Miliyan 1, zai bata miliyan 20. Ba wanda idan ta tambayeshi ba zai zageta yace mata kudin ubanta ne?

Sau nawa ake jima’i: Sau nawa ya kamata ayi jima’i

Duk Labarai, Jima'i, Kiwon Lafiya
Wani bincike ya nuna cewa yin jima'i sau daya a sati yana baiwa ma'aurata natsuwa. Hakanan kuma wasu masana halittar dan adam sun bayyana cewa, yin jima'i kasa da sau 10 a shekara na nufin cewa ma'aurata na cikin auren da babu jima'i, watau hakan yayi kadan matuka. Saidai kuma wani bincike ya nuna cewa, idan aka yi sabon aure, yayin da suke amarya da ango, ma'aurata kan yi jima'i kusan har sau 3 ko 4 a rana. Hakanan, idan ma'aurata na son samun haihuwa, shima sukan yi jima'i da yawa da tunanin ko ciki zai shiga. Magana mafi inganci itace, babu wata matsala idan mutum na yin jima'i a kullun. Masana sunce, Jima'i na saka mutum farin ciki nan take kuma yana yayewa mutum damuwa. Jima'i yakan iya zama yana da illa ne kawai idan: Ya zamana ya hana ka yin ayyukan ci gaban ra...
Da Duminsa: Majalisar Tarayyar Najeriya ta nemi a canja tsarin mulki da zai baiwa shugaban kasa damar yin zango daya na shekaru 6

Da Duminsa: Majalisar Tarayyar Najeriya ta nemi a canja tsarin mulki da zai baiwa shugaban kasa damar yin zango daya na shekaru 6

Siyasa
Wasu 'yan majalisar wakilai sun nemi cewa, a canja tsarin mulkin Najeriya da zai baiwa shugaban kasa damar yin mulki na shekaru 6 wa'di daya. Sannan sun nemi a rika yin karba-karbar mulki tsakanin yankuna 6 da ake dasu a kasarnan. Dan majalisar daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere ne ya bayyana hakan inda yace idan shugaban kasa, Gwamnoni suka rika yin wa'adi daya na shekaru 6 kawao, za'a samu saukin kashe kudi da kuma yin aiki me kyau.
DA ƊUMI-ƊUMI: An yanke wa magoya bayan Valencia su uku ɗaurin wata 8 bisa nuna wariyar launin fata a kan Vinicious Junior na Real Madrid.

DA ƊUMI-ƊUMI: An yanke wa magoya bayan Valencia su uku ɗaurin wata 8 bisa nuna wariyar launin fata a kan Vinicious Junior na Real Madrid.

Real Madrid, Vinicius Jr
An yanke wa magoya bayan Valencia su uku ɗaurin wata 8 bisa nuna wariyar launin fata a kan Vinicious Junior na Real Madrid. Tun a cikin watan Mayu ne su ka nuna wa ɗan wasan gaban na Madrid da Brazil wariyar launin fata. Sky Sports News ta rawaito cewa wannan shi ne karo na farko da aka taba hukunta masu nuna wariyar launin fata a kan ƴan wasa a Spain.
A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

A wannan satin ake sa ran Manchester United zata kori Ten Hag

Kwallon Kafa, Labaran Manchester United
A wannan satin da muke ciki ake sa ran Kungiyar Manchester United zata kori me horas da 'yan wasanta Erik Ten Hag. Thomas Tuchel ne dai ake tsammanin zai maye gurbin Ten Hag a matsayin sabon kocin United. Tuni kuma har Thomas Tuchel ya gana da wakilin Manchester United, Sir Jim Ratcliffe Tuchel ya bayyana cewa idan aka bashi aikin horas da Manchester United, zai dawo da Jadon Sancho zai kuma yi aiki da Mason Mount.
PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu

PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu

Siyasa
PDP Ta Sanya Ranar Da Za ta Yi Taron NEC Karo Na Biyu Jam’iyyar PDP ta bayyana ranar Alhamis 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta gudanar da taron majalisar zartarwa ta kasa karo na biyu a shekarar 2024. Idan za a iya tunawa, a taron farko da hukumar NEC ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu,an tattauna batutuwan da suka hada da makomar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Illiya Damagum, an daga shi zuwa taron NEC na gaba wanda aka shirya tun watan Agusta. Kungiyar ‘yan jam’iyyar ta Arewa ta tsakiya ta ce za a zabi dan takara daga shiyyar don kammala wa’adin tsohon shugaban Jam'iyyar na kasa, Dr. Iyiorchia Ayu, wanda ya yi murabus kusan shekaru biyu cikin wa'adinsa na shekaru hudu. Gabanin taron NEC na watan Satumba, jam’iyyar ta tsayar da ranar 27 ga wata...