Sunday, February 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Na tuba na daina maganganun Batsa, kuma Sheikh Daurawa ya sakani a Islamiya>>G-Fresh Al’amin

G-Fresh Al'amin, Nishadi
Tauraron mawaki kuma dan Tiktok, G-Fresh Al'amin ya bayyana cewa, ya tuba ya daina maganganin batsa. Ya bayyana hakane a shafinsa inda yace manya sun masa maganar rashin dacewar hakan. Saidai yace ba zai daina yaki da kamfanin dan malele ba. Ya kuma bayyana cewa Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya sakashi a Islamiya, zai rika zuwa daukar darasi. https://www.tiktok.com/@kanostatematerial/video/7376403600743877893?_t=8mu4XA2C5oL&_r=1 A baya dai, mun ji rahoton yanda Hukumar Hizbah dake Kano ta Kama G-Fresh Al'amin bisa zarge-zarge.

KARANTA KA KARU: Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji

Ilimi
An karbo Hadisi daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi..(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada ..(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa..(4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai kare shi daga talauci da m...
Da Duminsa: Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan ci gaba da tattaunawa da Gwamnati

Da Duminsa: Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan ci gaba da tattaunawa da Gwamnati

Siyasa
Rahotannin da muke samu na cewa, Kungiyar Kwadago ta NLC da TUC sun amince su janye yajin aiki da suke dan ci gaba da tattaunawa da gwamnati. An samu wannan matsaya ne bayan zaman da wakilan kungiyoyin kwadagon da gwamnatin tarayya. Kungiyoyin zasu zauna da membobinsu gobe dan tattauna maganar janye yajin aikin. Gwamnatin tarayya ta amince a ci gaba da tattaunawa akan mafi karancin Albashi sama da Naira Dubu 60.
Mafarauci ya harbe abokin farautarsa inda yayi tsammanin dabbace

Mafarauci ya harbe abokin farautarsa inda yayi tsammanin dabbace

Tsaro
An kashe wani mafarauci Sunday Ijiola a Yewa jihar Ogun inda aka yi tsammanin dabbace. Atanda Agbobiado ne yayi kisan ranar 28 ga watan Mayu. Mafarauta kusan 15 ne suka fita farautar inda suka raba kawunansu a cikin daji. Da Atanda ya tabbatar da abinda ya aikata sai ya tsere. Wanda aka harba din dan kimanin shekaru 43 ya mutu akan hanyar zuwa Asibiti. Kakakin 'yansandan jihar Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace suna bincike akai.

Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Murik ta jawo hankalin musulmai da kada su shiga yajin aiki

Duk Labarai
Kungiyar kare hakkin Musulmi ta murik ta bayyana cewa, yajin aikin da ake zai jefa rayuwar musulmai cikin wahala musamman ma ya dake fuskantar babbar Sallah. Dan haka kungiyar ta yi kira ga kungiyar kwadago data daga yajin aikin nada sai bayan sallah. Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta hannun babban daraktanta Professor Ishaq Akintola a yau Litinin. Ya bayyana cewa wannan yajin aiki zai saka musulmai wahalar ababen hawa dan haka suna kiran da a canja lokacin yin yajin aikin.
Dakarun da suka kewaye wurin tattaunawa da NLC masu gadin Ribadu ne – Sojin Najeriya

Dakarun da suka kewaye wurin tattaunawa da NLC masu gadin Ribadu ne – Sojin Najeriya

Siyasa
Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar ƙwadago ta yi cewa sojoji sun kewaye wurin da suke tattaunawa da wakilan gwamnatin ƙasar, tana mai cewa masu ba da kariya ne ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro. Ɗazun nan muka kawo muku rahoton cewa NLC ta yi zargin sojoji sun yi wa ofishin sakataren gwamnatin tarayya tsinke yayin da suke ganawa da wakilan gwamnati kan yajin aikin da suke yi. Sai dai cikin wani martani da ta mayar a kan saƙon da NLC ta wallafa a dandalin X, rundunar sojan ta ce ba haka abin yake ba. "Ku sani cewa Mallam Nuhu Ribadu ma yana halartar ganawar kuma ya isa wurin ne da sojoji masu gadinsa da doka tanada," in ji saƙon. "Da zarar ganawar ta ƙare jami'an tsaron za su fice daga wurin tare da shi."
Za’a rataye matar da ta hallaka tsohon mijinta a Kebbi

Za’a rataye matar da ta hallaka tsohon mijinta a Kebbi

Duk Labarai
A ranar Litinin ɗin nan ne wata babbar kotu a Birnin Kebbi ta yanke wa wata mata Farida Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe tsohon mijinta, Alkalin Alkalai Attahiru Muhammad-Ibrahim. Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, an gurfanar da Abubakar a gaban kotu bisa laifin kisan kai a ranar 25 ga watan Agusta, 2022, yayin da aka shigar da babban tuhumar a ranar 26 ga Yuli, 2023. Mai gabatar da kara ya ce mai laifin ya daba wa tsohon mijin nata wani abu mai kaifi a cikinsa da wuyansa da kuma hannun hagu wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa. Da yake yanke hukunci, babban alkalin jihar, wanda ya yanke hukunci kan karar, Mai shari’a Umar Abubakar, ya ce kotun ta gamsu cewa wadda ake tuhumar ya aikata laifin, bisa ga hujjojin da masu gabatar d...
Kasar Yahudawan Israela ta ce ‘yan kasarta su fice daga kasar Maldives bayan da ta haramtawa Yahudawan shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa

Kasar Yahudawan Israela ta ce ‘yan kasarta su fice daga kasar Maldives bayan da ta haramtawa Yahudawan shiga kasarta saboda kisan da sukewa Falas-dinawa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Kasar Maldives ta hana Yahudawan Israela shiga kasarta saboda kisan da Israela kewa Falas-dinawa. Shugaban kasar, Mohamed Muizzu ne ya bayyana hakan a ranar Litinin. Jimullar Yahudawan Israela dubu 11 ne suka je kasar ta Maldives yawom shakatawa a shekarar data gabata. A matsayin martani ga wannan matakin na kasar Maldives, ministan harkokin kasashen waje na Israelan Israelan Oren Marmorstein yace duk 'yan kasarsu da suke kasar ta Maldives su fice.