
Bankin Citibank dake kasar Amurka yayi kuskuren aikawa wani kwastomansa Dala Tiriliyan 1 a asusun jiyarsa maimakon Dala $280.
Saidai an gyara kuskuren da gaggawa bayan gano hakan.
Kuskuren ya farune a ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar data gabata, kamar yanda jaridar Financial Times ta ruwaito.
Saidai kwana daya da yin kuskuren, Tuni aka gyarashi.
Bankin ya sanar da cewa ba’a yi asarar ko sisi daga cikin kudin ba.