Monday, April 21
Shadow

NDLEA Ta Cafke Shàķikai Biyu Dà Hodar Ìbĺìś Kilo 5 A Filin Jiŕgin Sàma Na Lagos Yayin Shirin Su Na Tafiya Zuwa Indiya

NDLEA Ta Cafke Shàķikai Biyu Dà Hodar Ìbĺìś Kilo 5 A Filin Jiŕgin Sàma Na Lagos Yayin Shirin Su Na Tafiya Zuwa Indiya

Yayin da aka kama matashi ɗan birtaniya da kwayar loud filin jirgi; tsoho mai shekaru 75 da Skunk a Abia; tare da lalata fiye da kilo dubu 250 na tabar wiwi a Cross River

Dakarun runduna ta musamman na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa, wato NDLEA, sun kama wasu ‘yan uwan juna guda biyu: John Abugu mai shekaru 43 da Kenneth Abugu mai shekaru 31 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA) da ke Ikeja, Legas. An kama su da hodar Iblis mai nauyin kilo 5 da aka ɓoye a bangon jakunkuninsu, yayin da suke ƙoƙarin shiga jirgin sama zuwa kasar Indiya.

An cafke su ne a ranar Alhamis 3 ga Afrilu, 2025, bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma saurin daukar matakin bincike daga jami’an NDLEA. Sun yi iƙirarin cewa suna kan hanyan tafiya Indiya ne domin neman magani, amma yayin cikakken binciken da jami’an suka yi, an gano farin gari, wanda da daga baya aka tabbatar hodar Iblis ne a bangon jakunkuninsu.

Karanta Wannan  An naushi wani ya mùtù yayin da ya je rabon fada a jihar Adamawa

A rana guda, dakarun sashen tsare-tsaren MMIA sun kama wani saurayi ɗan shekara 20 ɗan asalin Ghana kuma mazaunin ƙasar Birtaniya mai suna Parker Darren Hazekia Osei da ƙwayar Loud, nau’in wiwi mai ƙarfi, wanda ya kai kilo 19.40 da aka loda a cikin wata babbar jakar tafiye-tafiye. Ya ce shi ɗalibi ne a bangaren Kimiyyar Kwamfuta a jami’ar East London University a Birtaniya. An cafke shi ne yayin dubar fasinjoin da suka iso daga Bangkok, Thailand, ta jirgin Ethiopian Airlines, a harabar isowa ta E a filin jirgin Lagos.

A cewar sa, yana zaune da iyayensa a Birtaniya, sai dai ya bar London zuwa Bangkok mako guda kafin a kama shi, inda ya karɓi haramtacciyar kayan don kawo su Najeriya.

A Jihar Kogi kuwa, jami’an NDLEA sun kama wata mata mai shekaru 33 mai suna Ngozi Ogili da kwayar methamphetamine kilo 3 a cikin motar haya daga Legas zuwa Abuja, a ranar Litinin 31 ga Maris. Biyo bayan hakan, an kai farmaki a wurin da za ta kai kayan a unguwar Apo mechanic da ke Abuja, inda aka ƙwace wasu ƙwayoyi da suka haɗa da Loud da Colorado, nau’ikan gurbatattun tabar wiwi ne.

A jihar Abia, a ranar Asabar 5 ga Afrilu, an kama wani tsoho mai shekara 75 mai suna Nna Nnanna Felix da tabar wiwi mai nauyin kilo 1.6 a garin Umunteke Asa, ƙaramar hukumar Ukwa West. Haka zalika, an cafke wani saurayi David Chinemerem mai shekaru 21 da ƙwayoyi ampoules 2,050 na pentazocine a titin Umuode, Aba a ranar Talata 1 ga Afrilu.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya canja ra'ayi kan maganar sauya Fasalin Haraji

A Yobe kuwa, jami’an NDLEA sun kama wani Abdullahi Adamu a kan hanyar Potiskum-Damaturu a ranar Asabar 5 ga Afrilu da kwalabe 381 na syrup ɗin codeine da kuma ƙwayoyi 108 na tramadol. A Anambra kuwa, farmaki a tashar motar Osogbo, Onitsha, da wani gida a Oba cikin ƙaramar hukumar Idemili, ya kai ga cafke Obinna Sunday da ƙwayoyi 195,000 na tramadol. Haka kuma an kama Ugochukwu Ojalanonye a wajen da codeine kilo 4.2 da pentazocine kilo 5.4.

A babban birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis 3 ga Afrilu, jami’an NDLEA sun kama Sunday Ayogu mai shekara 51 da tabar wiwi kilo 25 da methamphetamine gram 90.4 a kasuwar Wuse. A ranar Juma’a 4 ga Afrilu kuwa, an kama wasu mata guda biyu: Faith Effiong Etim mai shekaru 64 da Victoria Asuquo Etim mai shekaru 40 yayin farmaki da jami’an NDLEA tare da hadin gwiwar sojojin Najeriya suka kai a gonakin tabar wiwi a Esuk-Odot cikin ƙaramar hukumar Odukpani ta Jihar Cross River, inda aka lalata sama da kilo 250,000 na tabar wiwi da aka shuka a fili mai fadin sama da hekta 100.
Haka zalika, reshen hukumar da ke sassa daban-daban na ƙasar nan sun ci gaba da gudanar da Yakin Yaki da Sha da Fataucin Kwayoyi (WADA), ta hanyar wayar da kai a makarantu, masallatai, majami’u, wuraren aiki da kuma cikin al’umma. Wasu daga ciki sun haɗa da: lacca ga ɗalibai da ma’aikatan Cave City Secondary School, Ogidi a Jihar Anambra; mazauna Dan’iyau village a Batagarawa, Jihar Katsina; da mambobin ƙungiyar masu sayar da magunguna a unguwannin Sangere da Kwanan Waya a Yola, Jihar Adamawa.

Karanta Wannan  Buhari ne ya gina ramin da Tinubu ya jefa mu>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa da ya ajiye aikinsa Hakeem Baba Ahmad

Yayin da yake yabawa da jinjina ga dakarun MMIA, SOU, Yobe, Abia, Kogi, Anambra, Cross River da FCT bisa nasarorin da suka samu, Shugaban Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd) ya jaddada cewa irin wannan nasara daga sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman a bangaren hana yaduwar kwayoyi da rage buƙatar su a cikin al’umma, abin alfahari ne matuƙa.

Femi BabafemiDaraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’aHedikwatar NDLEA, AbujaLahadi 6 ga Afrilu, 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *