Shahararren dan daundu, Bobrisky wanda ya sha dambarwar kame daga hukumomin Najeriya amma daga baya ya samu tsallakewa zuwa kasar waje ya sake bayyana.
Ya wallafa hotunan Bidiyo yana wasa da dalolin Amirka.
Wani har ya tsokaneshi da cewa aro kudin yayi amma ya mayar masa da martanin cewa a Najeriya ne ake iya yin haka amma banda kasar waje.
Bobrisky ya kara da cewa, Wani masoyinsa ne ya bashi wadannan kudade.