Tuesday, May 19
Shadow

Kalli Bidiyon: Rikici tsakanin mijin diyar Ministan Tsaro Bello Matawalle na kara kazancewa, inda a yanzu wasu rahotanni suka bayyana cewa kawar matar tasa da yake soyayya da ita dama tsohuwar Budurwarsa ce

A dazu ne dai muka samu Rahotanni Rade-radin da ake a kafafen sada zumunta cewa, daya daga cikin wadanda suka auri ‘ya’yan karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle yana soyayya da kawar matarsa.

Rahotanni dake sake fitowa a yanzu daga wani shafuka masu suna @fatyma_BintMuhd da shafin @chubbyfourth dana @Nimisioluwa da sauransu da dama na cewa wadda yake soyayyar da ita dama can tsohuwar Budurwarsa ce.

Wai ashe ma ya taba daukarta Bidiyonta tsyrara ya rika nunawa abokansa har DSS suka kamashi.

Wannan Rahoto nata yawo a kafafen sada zumunta, saidai har zuwa yanzu ma’auratan basu fito sun ce uffan kan lamarin ba.

Da yawan mutane na ta bayyana mabanbanta ra’ayoyi akan wannan lamari da ya baiwa da yawa mamaki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kama wata me sayar da abinci na fitsari a cikin tukunyar miyar abincin da take sayarwa

A wani Bidiyo da ya rika yawo, an ji wata mata na cewa, har gidan aurensu, mijin yake kai Budurwar tasa.

Saidai duka wannan zargine wanda bai tabbata ba tukunna

https://twitter.com/i/status/2048885750087680493

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *