Tuesday, January 14
Shadow

Bidiyon Wata Minista ya bayyana tsiràrà

Bidiyon ministar mata da yara da tallafi ta kasar Fiji, MP Lynda Tabuya ya fita inda aka ganta tsirara haihuwar uwarta.

Ministar tace wannan bidiyo ta yi shi ne ta aikawa mijinta amma bata da masaniyar yanda aka yi ya watsu a kafafen sada zumunta.

Tuni dai Firaiministan kasar, Sitiveni Rabuka ya sauke ta daga mukaminta dalilin wannan badakala.

Saiai tace ita bata aikata laifin komai ba dan kuwa mijinta ta aikawa bidiyon amma bata san yanda aka yi bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta ba.

Ta gargadi masu watsa bidiyon da su yi hankali dan tasa a yi bincike dan gano wanda suka watsa shi kuma zata dauki hukuncin shari’a akansu.

Karanta Wannan  Yansandan Najeriya sun kama saurayin da ya haɗa baki da budurwarsa don 'damfarar' iyayenta

Mataimakin Kwamishinan ‘yansandan kasar, Livai Driu ya bayyana cewa, suna kan binciken lamarin bayan korafin da Ministar ta kai musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *