Friday, December 13
Shadow

Abinci

Abubuwan dake kara ruwan jiki

Abinci, Kiwon Lafiya
Abubuwan dake kara ruwan jiki suna da yawa, a wannana rubutu zamu bayyana wasu daga cikinsu. Shan Ruwa: Shan ruwa ce babbar hanyar samarwa da jikin mutum ruwa, masana na asibitin The Mayo Clinic na kasar Amurka sun bayar da shawarar cewa, namiji kamata yayi ya rika shan ruwa a kalla Kofi 15.5 watau Kofi goma sha biyar da rabi a kullun. A yayin da ita kuma mace kamata yayi ta rika shan Kofi 11.5 watau Kofi goma sha daya da rabi kullun Dan samun isashshen ruwa a jiki. A shawarce ana son mutum ya rika shan ruwa a duk sanda ya ci abinci ko yaci wani Abu irin su masara, Gyada, kuli, cincin, cake da sauransu. Ana kuma son mutum ya rika shan ruwa tun kamin ya ji kishirwa. Hakanan mutum ya sha ruwa a yayin da yake aikin office, ko gudu ko tafiya me nisa ko motsa jiki, ko tukin mo...

Yadda ake aya mai sugar

Abinci
AYA MAI SUGAR INGREDIENTS :-▪Aya Kofi 4▪Sugar Kofi Biyu▪Gishiri Karamin Cokali▪Flavour Karamin Cokali Method: Ki surfa aya ki wanke ta tas, ki xuba a tukunya ki soyata har sai kinga ta soyu, ki ajeta a side. Ki zuba sugar 1 cup a tukunya da ruwa 1 cup da gishiri rabin karamin cokali ki dora a wuta ya dahu har sai sugar tayi danko ta fara kumfa sai ki zuba wannnan aya kina juyawa har sai ta hade. Ki juye a faranti. Ki dakko sauran sugar kiyi kamar na farko ki kuma xuba ita wannan ayar da kika sawa sugar da farko. In tayi ki juye a faranti ki zuba flavor ki juya. Amfanin sa sugar sau biyu yafi haske ne in ba kya so kina iya sawa sau daya.

Yadda ake wainar gero

Abinci
Kayan Hadi da za'a nema Kayan Hadi*Surfafen gero*Albasa*Yeast*Baking powder*Oil MethodNajika gero ya wuni da yamma na wanke na markaɗa saina rufe ya kwana da safe na tace ruwan saman na dafa wani geron rabin gwagwani na zuba akan markadan nasa albasa da yeast cokali (1) nasa baking powder na juya na rufe bayan 20minute ya tashi na dora kasko na soya yayi laushi sosai gaskiya kuma ku gwada Ki gwada in Sha Allah za ta yi armashi

Yadda ake yin pizza

Abinci
YADDA AKE YIN PIZZAAbubuwan Da Ake Bukata: Nikakken Nama Flour Albasa Yeast Tafarnuwa Mai Maggi Tumatur Farin masoro Yadda Ake Yi: Zaki Kwaba Flour ki da yeast da maggi da farin masoro da mai ko butter ki ajiye sai ya kumburo kaman kwabin cin~cin sai ki dauko nikakken namanki da kika soyashi sama~sama da maggi da garin tafarnuwa sai ki aje ki dauko flour nan ki gutsira ki murzata da dan tudu idan kuma falai~falai kikeso to sai kin gama murzawa sai ki debi wannan hadin ki zuba akai ki dauko tumatur dinki da kika jajjaga tare da attaruhu da albasa ki zuba akai ko kuma ki zuba kafin naman, sai ki murza wata flour kamar waccan sai ki rufeta dashi ki dora a farantin gashi bayan kin shafeshi da mai, ki barshi kamar 20 minutes sai ki fidda ita za kiga ya gasu ya...

Yadda ake scotch egg

Abinci
Yadda ake SCOTCH EGG Kayan hadi:- KwaiFlowerBaking powderMaggiCurryGishiriAlbasaAttaruguTattasai Yadda ake yi:- Zaki dafa kwai adadin yadda kike bukata sai ki yanka albasa attarugu da maggi da gishiri ki soyasu sama sama, sannan ki kwaba fulawarki da butter da kwai mu murza da fulawa ko da abun murza taliya sannan kidauko kwan da kika dafa Zaki yanka shi biyu da wuka sai ki dinga yanka kwababen fulawar nan sai kidinga zuba soyayyen kayan miyanki a ciki sannan kinade da fulawa bayan kin nade sai ki kada kwai kidinga daukowa kina tsomawa acikin ruwan kwai kina soyawa.

Yadda ake dafa kazar amarya

Abinci
Hadin Kazar? Amare* Yanzu zamuyi bayanin sirrin dafa kazar Amare wanda idan har mace tayi kafin Aurenta da kamar sati 1 zataga amfaninsa,Irin wannan ne idan baki San sirrin ba zakije ki saya da tsada. ??Koda yake wasu kiwa ke hanasu yadawa da Kansu. To ga sirrin Yadda ake :Anaso kisamu bushashen ganyen magarya da kanunfari da idon zakara duk ki hadasu waje daya ki dakasu ki tankade su zama gari to idan kika samu:Budurwar kazar? kika gyarata saiki zuba wannan garin acikin tukunyar sannan zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso. Bayan ta dafu saiki cinye gaba daya. Yana saka Farjin mace ya kumbura ya ciko da Ni'ima, kuma yana karawa mace dàn dàno… Matar Aure ma zata iya wannan Hadin ba lallai sai Amarya ba.

Yadda ake dafa ganda

Abinci
SLMYau nazo muku da yadda ake dafa ganda within some minutes duk taurinta,daga yau Baku basa qusa ko paracetamol ayayin dahuwar ganda. Dafarko zaki dauki gandarki kisa atukunya kisa ruwa yasha kanta,seki saka kanwa ungurnu babba aciki kirufe,kidora awuta kibarshi yayi tafasa kamar 3. Zakiga ruwan yayi baqi sosae,seki sauke ki barshi ya huce idan ya huce seki samu soson qarfe ki wanke abarki Tass se bakin yafita da qasar jiki. Seki sake dorata awuta kisa wata kanwar kadan kibarta taqara tafarfasa,zakiga ruwan yayi danqo seki zubar ki dauraye. Ki sa kayam qamshi da daddawa da seasoning and spices kisa ruwa kisake dorawa taqarasa dahuwa,wlh daga yau kin dena jiqa ganda tsahon kwana1-2, tasted and trusted.

Yadda ake zobo mai dadi

Abinci
YADDA AKE ZOBO DRINK Abubuwan buqata Sobo/zoboCucumberBawon abarbaDanyar cittaKanumfariFlavorSugarBevi mix cola da Bevi mix mangoKamshi (Wanda ake samu a cikin kayan yaji amma optional ne)Sai barkono kadan (optional) Da farko za a tsince dim dattin da ke cikin zobo sai a zuba a tukunya babba a markada cucumber a wanke bawon abarba dik azuba akai,a zuba barkono kadan da kamshin kayan yaji (optionals ne) a zuba kanumfari da jajjagaggiyar citta akai sai a zuba ruwa a Dora kan wuta ya tafasa sosai a tace a kara ruwa akai a sake tacewa har sai zobon ya salamce sai a ajiye domin ya rage zafi sai a zuba sugar,flavor na ruwa,da kuma Bevi mix (wadanda ba sa so wannan zasu iya Saka iya sugar kawai) sai juya su su hade jikinsu sosai a kara tacewa sai a juye a jug or a kulla a Leda ko a robob...

Yadda ake miyar zogale danye

Abinci
MIYAR ZOGALE AttaruhuTumaturAlbasaMaggiZogale danyeTafarnuwaManjaGyada Step 1Ki wanke kayan miya kiyi grating dinsu dasu tafarnuwa albasa a tare, ki daka gyadarki kar ta daku sosai Step 2Ki soya manja ki zuba kayan miyanki gyada ki qara ruwa dan daidai ki rufe, in ta fara dahuwa kizuba maggi kibarta ta dahu saiki zuba zogalen ki kibarshi ya fara nuna saiki zuba albasa ki barta ta qarasa saiki sauke

Yadda ake kunun gyada

Abinci
YADDA AKE YIN KUNUN GYADA Kayan da ake bukata; Farar shinkafa 3 tins Danyar gyada 4 tins Sugar dai-dai misali. Abu na farko da ake bukata uwar gida ta yi, shi ne ta gyara farar shinkafarta danya sai ta wanke ta ta tsane tsaf, Bayan haka,dama kin soya gyadarki sama-sama kin murje bayan km kin bushe sai ki kai a markado miki bayan an markado ki tace. Sai ki zuba tataccen ruwan gyadar a tukunya in ya tafasa, sai ki dakko wanna shinkafar da ki ka wanke kk km tsane sai ki zuba ta a ciki suyi ta dahuwa har sai ta dahu sosai in kina gudun kada ya tsinke zaki iya zuba ruwan lemon tsami kadan. Idan kuma kin ga bai yi miki kauri ba sai ki dan dibi gasarar koko ki dama da ruwan sanyi sai ki zuba ki juya sosai zai yi kauri insha Allah.