TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure
TIRKASHI: Ya Saki Matarsa Saboda Ganyen Shayi, Bayan Tsawon Shakara Goma Suna Zaman Aure
Daga Mubarak Ibrahim Lawan
"Da Asubahi ta gaya wa mijin cewa ganyan shayi ya ƙare. Wajen ƙarfe shida na safe kuma ƙaninsa ya zo ya ɗauke shi suka tafi jana'izar wani abokin kasuwancinsu. Bayan ya dawo gida wajen ƙarfe 9 na safiyar, sai ya tarar yaransa ba su tafi makaranta ba. Ya tambayi dalili sai ta ce ai bai kawo ganyen shayin da za su yi karin kumallo ba. Daga nan fitina ta fara. A yinin ya sallame ta.
Lokacin da iyaye suka shiga maganar, sai ya ce ya gaji da zama da macen da ta ke kasa yi masa hidimar naira 100 duk da cewa shi ya na iya yi mata hidimar miliyan 5 domin, a shekarar bara ma ya kai ta Hajji, ya canja mata kujeru, kuma ya tabbatar cewa shi ya sama mata aikin da ta ke yi. Ya ƙa...