Saturday, June 6
Shadow

Auratayya

An kama matar data kashe surukarta ta hanyar caka mata wuka

An kama matar data kashe surukarta ta hanyar caka mata wuka

Auratayya
Hukumar 'yansandan jihar Naija Sun kama wata mata me suna Fatima Sani wadda ake zargi da kashe surukarta ta hanyar caka mata wuka.   Kwamishinan 'yansandan jihar,Alhaji Adamu Usman ne ya bayyana haka ga manema labarai Ranar Litinin inda yace Fatima me shekaru 37 ta fitone daga kauyen Gobirawa a karamar Hukumar Mashegu dake jihar.   Yace sun samu matsalane da mijinta, Sani Umaru a ranar 23 ga watan Afrilu inda hakan yayi sanadin mijin ya saketa.   Ita kuwa sai ta zargi cewa mahaifiyar mijin nata, A'ishatu Umar me shekaru 70 ce ta sashi ya saketa dan haka taje har gida ta kasheta da wuka.   Yace ana ci gaba da bincike kuma za'a gurfanar da mai laifin a gaban kuliya dan hukuntata.
Yawa matarshi wanka da tafasashshen ruwan barkono tsakar dare saboda zargin cin Amana

Yawa matarshi wanka da tafasashshen ruwan barkono tsakar dare saboda zargin cin Amana

Auratayya
Wani magidanci dake zargin matarshi na cin amanarshi ya shammaceta cikin dare ya kwarara mata tafasasshen ruwan Barkono.   Mutum ya barine saida tsakar dare wajen karge 12:30 sannan ya je ya debo tafasashshen ruwan ya kwararawa matar.   Lamarin ya farune Oke-Owu, Modakeke dake jihar Osun.   Tuni dai aka garzaya da matar Debora Asibiti dan kula da ita.   Shi kuwa mijin, Adeniyi Akinde me kimanin shekaru 27 tuni 'yan sanda suka kamashi kamar yanda me magana da yawun 'yansanda na jihar, Yemisi Opatola ta bayyana   'Yansandan sun ziyarci Deborah a Asibiti inda kuma tuni suka fara bincike akan lamarin.
Mustapha na buruska yayi wuf da wata

Mustapha na buruska yayi wuf da wata

Auratayya
A yau ne jarumi Mustapha na Buruska ya kara aure wanda ya sanar da haka a shafinsa na Instagram. Mustaphan ya wallafa hoton sa shida amaryar sa mai suna fatima Shehu tare da godewa jama'ar da suka halacci zuwa wajan daurin auran sa. Tare da yin addu'ar Allah ya hada kan matan nasa amarya da uwargida.
Nima kwanannan zan samu Saurayi in Aura>>Meenah M Sadeeq

Nima kwanannan zan samu Saurayi in Aura>>Meenah M Sadeeq

Auratayya
Bayan auren da tauraron fim din Kwana Casa'in da Tara wanda tashar Arewa24 ke nunawa, Abdul yayi na wadda ta darashi da shekaru, lamarin ya dauki hankula sosai inda akaita samun mabanbanta ra'ayoyi.   Wasu ma basu yadda da cewa Abdul din yayi aure ba da gaske, saida ya fito a wani faifan Bidiyo yana gayawa mutane cewa hotunan da aka gani da gaskene.   Wata ma'abociyar shafukan sada zumunta, Meenah M. Sadeeq da take mayar da martani kan wannan lamari ta bayyana cewa babu wani abin abi dan mace me shekaru 40 zuwa sama ta auri matashi dan kimanin shekaru 30.   Ta kara da cewa, idan dai Tsoho ,zai auri budurwa me shekaru sha ko ashirin da wani abu to suma mata zasu iyayi.   Ta yi kira ga mata da suka manyanta dasu dain jira wai sai mai kudi zasu aura...
‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

‘Abin da ya ba ni karfin gwiwar in auri mata biyu a rana guda>>ango Ibrahim Kasimu Oboshi

Auratayya
Wani manomi dan shekaru 35 da haihuwa kuma mai wakiltar mazabar Iwogu a karamar hukumar Keana ta jihar Nasarawa, Ibrahim Kasimu Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah, ya auri wasu mata biyu a rana daya. Ya auri Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Isyaku Akose a ranar 28 ga Maris, 2020. A lokacin da yake Magana da jaridar Daily Trust a ranar Asabar, ya ce, “Ni maraya ne, mai yin noma kuma a yanzu ni kansila ne. A matsayina na maraya, na ɗauki noma da makaranta da muhimmanci, da harkar noma ne, na sami damar kula da mahaifiyata da kaina. Daga baya ne, na ci zabe don wakiltar garina. ”   Ya ce lokacin da mutane da yawa suka ji yana shirin auran mata biyu, sai suka yi mamaki ko shi ɗan sarki ne ko ɗan wani attajiri ne, amma an gaya musu cewa ni manomi ne. "A gaskiya na rike noma da matu
Abun tausayi baya karewa wata mata ta kone tare da yayanta sakamako gobara da ta ritsa da ita a jihar bauchi

Abun tausayi baya karewa wata mata ta kone tare da yayanta sakamako gobara da ta ritsa da ita a jihar bauchi

Auratayya
Lamari dai ya faru ne a sabon gida a Yelwa dake jihar bauchi a ranar litinin. Matar mai kimanin shekaru 26 ta gamu da ajalinta ne ita da ya'yan ta biyu kamar yadda jaridar Punch ta rawaito cewa mijin matar ya kasance yana zuba mai a cikin injin janareta a rashin sani sai man fetir dake zubawa a cikin injin ke kwaranya har zuwa cikin kicin inda matar ke dafa abinci, nan take wuta ta fara bin nason fetir din inda har ta cimma mai inda yake. Nantake sai wuta takama kamashi bayan ganin haka sai yayi cilli da jarkar fetir din dake hannun sa, inda nan take wutar ta kara kankama wanda ta kai takama kan injin tare da wani babur dinsa da ke a jiye a gefe. Bayan faruwar lamarin sai matar tai yun kurin shiga cikin gidan dan ta dauko yaranta amma Ina ajali yayi kira. An samu gawar matar ...
An kame amare da angwaye a zariya sabuda karya dokar gwamnati da sukai na hada tarun jama’a a bikin auran su

An kame amare da angwaye a zariya sabuda karya dokar gwamnati da sukai na hada tarun jama’a a bikin auran su

Auratayya
Yan aikin sa kai dan tabbatar da tsaron unguwanni (kadVS) sun cafke Amare 4 da an gwayan su a ranar asabar a Zariya domin keta dokar gwamnatin jihar da ta sanya na hana taron jama'a. Bala Galadima, shine Kwamandan Rundunar yace an kama wadanda ake zargin hada taron ne a wajajan Lowcost, Mangwaron Babayo, Magajiya da Bakin Kasuwa. Kwamandan na shiyya ya ce tun da farko rundunar ta samu bayanan sirri na amaran tare da angwayan inda rundunar ta bisu tare da cafke ko wanne daga cikin wanda suka shirya tarukan bikin tare da sauran baki. Jihar Kaduna ta sanya dokar hana taruwar jama'a tare da sanya dokar zaman gida wanda gwamnan jihar ya sanya bisa fargabar annobar cutar Covid-19 data barke.
Magidanci ya kashe me gidan hayar da yake ciki bayan kamashi da matarshi turmi da tabarya

Magidanci ya kashe me gidan hayar da yake ciki bayan kamashi da matarshi turmi da tabarya

Auratayya
Wani me gidan haya ya gamu da ajalinsa bai shirya ba bayan da kwadai ya kaishi neman matar wanda ke zaman haya a gidanshi kuma ya kamasu turmi da tabarya.   Damilaye Adeoya me shekaru 42 da a yanzu yana hannun 'yan sandan jihar Ogun Osun ya bayyana cewa bai damu da hukuncin da za'a yanke masa ba tunda dai ya sheke me gidan hayar dake lalata da matarsa.   PMExpress ta ruwaito Damilaye na cewa ya dade yana zargin akwai wani abu dake faruwa tsakanin matar tashi da me gidan da yake haya, amma sai matar ta rika gayamai ma ita ta tsani mutumin.   Yace wani sako daya ga matarshi ta aikawa wani na cewa "Karfe 11" ne ya sa bayan ya fita daga gida sai ya dawo da wuri.   Yace ya shigo ta kofar bayane inda ya iske matar tashi da me gidan hayan nasu suna sha'...
Bayan Sallah za mu yi aure>>Saurayin Baturiya na Panshekara

Bayan Sallah za mu yi aure>>Saurayin Baturiya na Panshekara

Auratayya
Saurayin nan da budurwarsa ‘yar Amurka ta biyo shi Kano mai suna Isa Suleiman Panshekara ya ce a bayan Karamar Sallah zai angwance da amaryarsa  Janine Sanchez.     Saurayin mai shekara 26 ya ce sun dage shagulgulan bikin nasu ne saboda wasu dalilai ba kamar yadda ake rade-radi ba a shafukan sada zumunta cewa saboda Shugaba Trump ya hana ’yan Najeriya shiga Amurka ne.     “Sosai kuwa, yanzun nan kafin ka kira ni muka gama waya ta bidiyo, ka ga kuwa alama ce da ke nuna muna tare ba kamar yadda kafafen watsa labarai ke fada ba.”     Ya ci gaba da cewa: “Babu wani bambanci gaskiya, illa in ce ma so ne ya sake karuwa.     “Mafi yawa ta Facebook Messenger muke magana kuma waya muka fi yi ba rubutu ba (chatting) ba kamar