Friday, December 13
Shadow

Borno

Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno

Yawan wanda suka mutu bayan harin kunar bakin wake sun kai 30, guda 100 sun jikkata a jihar Borno

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, yawan wadanda suka mutu ya karu zuwa 30 daga 8 da jami'n tsaro suka bayyana a jiya. Hakanan yawan wadanda suka jikkata ya karu zuwa 100. Rahoton jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin. Jaridar tace Timta ya bayyana mata cewa 'yar kunar bakin wake ta farko ta je wajan bikine tare da yara inda ta tayar da bam sannan an samu ta biyu itama taje wajan wani bikin ta sake tayarwa. Timta ya kara da cewa, an sake samun wani tashin bam din a karo na 3. A baya dai, jaridar Premium times ta ce 'yan kunar bakin wake 4 ne suka tayar da bamabamai a Garin na Gwoza. Timta dai yace ba'a kammala samun bayanai ba amma zuwa yanzu mutum 100 sun jikkata kuma an garzaya da wasu zuwa Maiduguri.

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama. Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni. Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza. Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu. A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba'a kai ga tantance yawansu ba c...
Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu ‘yan Boko Haram da suka tuba

Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu ‘yan Boko Haram da suka tuba

Borno, Tsaro
Wannan matar an kamata da harsasai 2000 zata kaiwa 'yan Bindiga a jihar Zamfara. Jami'an tsaron sun kamata ne da makaman amma babu cikakken bayanan me ya faru. Hakanan wasu 'yan Boko Haram, Baana Duguri, Momodu Fantami, Abubakar Isani da Zainami Dauda sun mika kansu wajan jami'n tsaro inda suka ce sun tuba.  An kwace makaman Bindigar Ak47 guda 2, da Harsasai masu yawa, da wasu kananan bamabamai da mashina 2, da dai sauransu. Sun bayyana cewa, sun fito ne daga garin Damboa.
Al’umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP

Al’umma na tserewa daga ƙauye a Borno saboda barazanar ISWAP

Borno, Tsaro
Mayaƙan ISWAP sun bai wa mazauna Kukawa lga sanarwar su bar kauyensu ko kuma su fuskanci kisa kwanaki huɗu da kashe masunta goma sha biyar a yankin Tumbun Rogo. Wani mazaunin garin da ya gudu daga al’ummarsa zuwa Maiduguri sa’o’i uku da samun wannan barazana, ya bayyana hakan ga gidan talabijin na Channels. A yayin da ya ke bayar da labarin yadda lamarin yake, mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa mayakan sun tara jama’ar al’umma daban-daban a ƙaramar hukumar da sanyin safiyar Alhamis, inda suka ce su bar gidajensu kafin ranar Asabar, in ba haka ba za a kashe su. A cewarsa, bayan da suka samu barazanar ‘yan ISWAP din, al’ummomin suka fara barin yankunansu, yayin da wasu suka tafi Kross Kauwa, wasu kuma suka tafi Monguno. Kukawa lga ƙaramar hukuma ce a gefe...
Mayakan Kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Mayakan Kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Borno
Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno. Sun kashe masuntanne a karamar hukumar Kukawa i da kuma da yawa suka jikkata. Lamarin ya farune da misalin karfe 10:40 na dare yayin da masuntan ke shirin fara kamun kifi na dare. Mayakan na ISWAP sun isa wajan da masuntan suke suka zagayesu suka kuma bude musu wuta. Wata majiya ta bayyanawa Daily Trust cewa mayakan sun sacewa masuntan kifi da yawa. Wanda suka rasu kuma an binnesu kamar yanda addinin musulunci ya tanada. Saidai har yanzu akwai wanda suka bace ba'a san inda suke ba.