
DA ƊUMI-ƊUMINSA: Mawaki Rarara Zai Auri A’isha Humaira A Gobe Juma’a?
Cikin daren nan an fara yawo da hotunan shahararren mawaki Dauda Kahutu Rarara tare da abokiyar aikinsa A'isha Humaira da ke nuna zai angwance a gobe Juma'a.
Majiyar Kano Times ta ruwaito cewa za a ɗaura auren shahararren mawaki a Nijeriya Dauda Kahutu Rarara tare da abokiyar aikinsa A'isha Humaira a gobe Juma'a, a garin Maiduguri da ke jihar Borno.