Saturday, December 14
Shadow

Duk Labarai

An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

An kashe jimullar Mutane 4,416 sannan an yi garkuwa da 4,334 a shekara 1 da Tinubu yayi yana mulkin Najeriya

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe jimullar mutane 4,416 da yin garkuwa da guda 4,334 a shekara 1 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi yana mulki. Wata gamayyar masu fafutukar kasa da kasa da kuma Najeriya su 84 ne suka fitar da wannan rahoto. Rahoton yace kungiyoyin basu saka abubuwan dake faruwa na fashi da makami da sauran laifuka ba. Sunce wannan lamari ya sanya 'yan Najeriya sun rasa 'yancin rayuwa me inganci da kuma rayuwa cikin walwala. Kungiyar tace ci gaba da wannan lamari ya jefawa 'yan Najeriya tsoro da fargaba da rashin tabbas. Kuma sun ce idan gwamnatin Tinubu bata dauki mataki kan lamarin ba, suna daf da fitar da rahoton yanke tsammani akanta. Sunce suna jawo hankalin gwamnatin Tinubu data yi kokari wajan sauke nauyin dake kanta na kare rayuwa da dukiy...
Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Hoton Sojan Najeriya da aka kama ya saci harsasai

Tsaro
Hukumomin soji dana CJTF a jihar Borno sun kama wani soja da laifin satar harsasai. An kama sojan ne me suna Corporal Francis Bako a tashar motar Kano dake Maiduguri. An kamashi ne bayan samun bayanan sirri akan satar harsasan da yayi. Sojan dai na kan hanyar zuwa Kadunane bayan da aka kamashi da harsasan guda 602 kuma yana tsare yanzu haka.
Labari Me Dadi:Zamu rabawa mutane Miliyan 75 kudade kyauta, tsarin Npower ya dawo>>Inji Gwamnatin Tinubu

Labari Me Dadi:Zamu rabawa mutane Miliyan 75 kudade kyauta, tsarin Npower ya dawo>>Inji Gwamnatin Tinubu

Siyasa
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana dawo da tsarin tallafawa mutane wanda ta tsayar a watannin da suka gabata. Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a matsayin shiri na cika shekara daya da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi. Tsarin dai wanda ya hada da ciyar da dalibai, da Npower, da baiwa mutane gajiyayyu kudin tallafi da tallafawa 'yan kasuwa da sauransu a yanzu ya dawo zai ci gaba da aiki. Ministan yace dama a baya an tsayar da tsare-tsarenne dan bincike da kuma kawar da matsalolin dake cikin tsarin kuma yanzu an kammala. A dambarwar da aka yi ta dakatar da tsarin, ta hada da dakatar da ministan jin kai Beta Edu wadda aka yi zargin ta aikata ba daidai ba. Saidai a yayin da yake maganar, Mi...
Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 ya soki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan da ta cika shekara guda da kafuwa. Atiku yace tsare-tsaren gwamnatin Tinubu ta jefa mafi yawan al'umma cikin halin wahala inda kuma ta talauta masu kudi. Atiku yace Najeriya bata aiki a karkashin Tinubu inda yace Tinubun ya kasa kawo canji da ci gaban da ya mutane alkawari. Yace matakan da Tinubu ya dauka sun ma kara jefa mutanene cikin halin kaka nikayi. Yace matsayin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki a yanzu yafi muni idan aka kwatanta da shekara daya data gabata. Yace gwamnatin Tinubun ta karawa mutane wahala ne akan wahalar da ake ciki wadda gwamnatin tsohon s...
Sai an shekara 6 ana shan wahalar da cire Tallafin man fetur ya kawo>>Inji Shugaban ADC

Sai an shekara 6 ana shan wahalar da cire Tallafin man fetur ya kawo>>Inji Shugaban ADC

Siyasa
Shugaban jam'iyyar ADC, Dr Ralphs Okey Nwosu ya bayyana cewa, sai an shekara 6 ana wahala kamin a kawo karshen wahalar da cire tallafin man fetur ya jefa mutane. Ya bayyana hakane hirar da Daily Trust ta yi dashi. Cire tallafin man fetur ya jefa mutane da yawa a cikin matsin rayuwa inda mutane suka rika fama da abinda zasu ci wanda a baya ba haka bane. Saidai Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, wannan mataki ne data dauka dan amfanar al'umma baki daya wanda kuma na dolene.
Ba A Taɓa Gwamnatin Da Ta Kawo Wa Nijeriya Bàĺà’ì Da Mùśìbà Kamar Gwamnatin Buhari Ba, Cewar Attahiru Bafarawa

Ba A Taɓa Gwamnatin Da Ta Kawo Wa Nijeriya Bàĺà’ì Da Mùśìbà Kamar Gwamnatin Buhari Ba, Cewar Attahiru Bafarawa

Duk Labarai
Daga Imam Aliyu Indabawa Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi Allah wadai da masu baiwa Buhari da gwamnatinsa kariya yana mai cewa duk mutumin da zai iya fitowa ya kare Buhari da gwamnatinsa to za su haɗu da shi a lahira a gaban Allah. A yayin tattaunawarsa da kamfanin watsa labarai na BBC Hausa tsohon gwamnan ya ce," Bala'in da Buhari ya kawo ƙasar nan na lalacewar damokraɗiya da cin hanci ni dai a rayuwata ban taba ganin gwamnatin da ta kawo mana bala'i da masifa kamar ta Buhari ba." Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin Buhari ta ciyowa Nijeriya mummunan bashi na tiriliyoyi amma babu wani aiki da aka yi da kuɗin, ya ce wannan sai an je lahira za a yi shari'a a kansa.

Saboda yawan kudin da ya sata, Idan aka sakani wuta iri daya data Hadi Sirika ba’a min Adalci ba>>Inji Wannan mutumin

Duk Labarai
Wani mutum dan Najeriya ya bayyana cewa, idan aka sakashi wuta iri daya da ta tsohon ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika ba'a masa adalci ba. Mutumin ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta kuma ya fadi dalilinsa na cewa Hadi Sirika ya saci kudi da yawa. Hadi Sirika dai na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin satar Biliyoyin Naira da suka hada da biliyan 2 wanda ake zargin ya sata shi da diyarsa da surukinsa da kuma Biliyan 19 wadda ake zargin ya sata tare da kaninsa.
Hoto:Wannan mutumin ya mutu a dakin Otal bayan yin lalata da karuwa

Hoto:Wannan mutumin ya mutu a dakin Otal bayan yin lalata da karuwa

Duk Labarai
Wani mutum a kasar Afrika ta kudu ya mutu a dakin Otal bayan yin fasadi da karuwa. Matan dake gidan karuwan sun dakata da aiki bayan faruwar lamarin da ya girgizasu. Rahoton yace bayan da suka gama abinda zasu yi, karuwar ta taba mutumin inda ta ga ya mutu baya motsi. Anan ne aka kira jami'an tsaro dana lafiya inda suka tabbatar da cewa ya mutu. Ana bincike dan gano abinda yayi sanadiyyar mutuwarsa.