Jam’iyyar Labour ta ce yajin aiki zai ƙara wa ƴan Najeriya wahala ne kawai
Jam'iyyar Labour ta yi kira ga ƙungiyoyin ƴan ƙwadago a Najeriya da su sake tattaunawa da gwamnati a kan maganar sabon albashi mafi ƙanƙanta maimakon shiga yajin aiki.
Jam'iyyar ta ce a halin da Najeriya take ciki yajin aiki ba shi da amfani hasali ma zai iya ƙara wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke ciki ne.
Babban sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN).
Ya ce tuni daman ƴan Najeriya na fama da katutun matsaloli, a don haka babu buƙatar yin abin da zai ƙara waɗannan wahalhalu.
'' Ina ganin neman Naira 494 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai yuwuwa ba. Abu ne da ba zai ɗore ba saboda hakan na nufin cewa Najeriya za ta ɗauki duk kuɗin da take da shi ta riƙa biyan ma'aikata,'' in ji ...