An ga Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo tare da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Peter Obi suna raha.
An dauki Bidiyon ne a Lagos wajan wani taron Bikin Birthday.
https://twitter.com/i/status/2068092100369842382
An yi janaʼizar matashi Ismaʼil Makaye da ke sanaʼar sayar da kayan kwalliya a unguwar Hotoro Tishama rasuwa, bayan ya rasu a gidan budurwarsa fitacciyar ƴar rawar Solon nan kuma ƴar TikTok Fati Cele.
Daya daga makusantansa ya shaida wa Arewa Updates cewa, Cele ce ta fito daga cikin gidanta da safiyar Jumuʼa tana ihun gobara, kuma ko da aka shiga an tarar da shi ya ƙone kuma da alamun jini a jikinsa.
Ya ce, ƴan sandan Dorayi Babba na tsare da Cele yayin da su ke ci gaba da bincike.
Abokanansa da ƙawayenta sun ce, dama a baya sun samu saɓani tsakaninsu har ta kai sun rabu kafin a baya-bayan nan su sake daidaitawa.
Fati Cele dai ƴar asalin jihar Borno ce da ke haya a unguwar ta Danbare, inda ta ke wasan Solo a wani gidan Gala da ke unguwar Sabon Garin Kano.
Makusancin nasa...
Tauraruwar Tiktok, Alpha Charles Borno ta bayyana rashin jin dadinta da kalaman Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Muhammad inda tace bai kama Musulmai su rika goyon bayan Arne, Davido suna kin dan uwansu Musulmi Rarara ba
Alpha tace taji dadin yanda taga a Comment mafi yawan musulmai basu goyi bayan Fati Muhammad ba inda tace a yanzu mutane sun waye an daina Amfani da addini ana cutarsu.
Tace ita ta taso tana son Musulmai kuma ta daukesu a matsayin 'yan uwa.
Tacewa Fati Muhammad ko dan ita abin bai taba shafarta ba ko wani nata shine take kare gwamnati akai?
https://www.tiktok.com/@alphacharlesborno/video/7653282745698913543?_r=1&_t=ZS-97MgXt3OXqc
Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi wadda a cikin kwanakinnan ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta saboda ta bayyana rashin muhimmancin aure da bayyana cewa ba lallai ta yi auren ba.
A yanzu tace ko da ace zata yi aure, to Bature zata aura.
Nafisa ta koka da cewa, A arewa sai a rika cewa wai mace ba'a sakinta sakaka sai an rika tallafota.
Tace shin wai su mata mashinane ko motoci?
https://www.tiktok.com/@nafeesat_official/video/7653059629332614430?_r=1&_t=ZS-97MX9KnEX2e
Wata 'yar Najta dauki hankula a kafafen sadarwa bayan data koka da cewa me gidan da take haya ya mata karin kudin haya.
Matar ta fito tana kokawa inda tace me gidan yana son ya tashe ta daga gidan saboda yana son kara kudin hayarsa kuma karin da zai yi yasan yana da yawa ba lallai ta yadda ba.
Tace ya tashi mutane da yawa daga gidan saboda su shidane a gidan amma da ya zo kanta sai ta rokeshi har ta samu wani da ya sani dan ya sa baki.
Sai yace mata amma saidai idan zata yadda da sabon kudin hayar da zai saka.
Tace ta amince inda a baya tana biyan wajan Miliyan 20 a shekara, yanzu kuma aka mayar dashi Miliyan 50 a shekara.
Tace duk da haka tace ta amince amma sai ya ci gaba da matsa mata sai ta tashi daga gidan sannan har ya cire mata wutar Lantarki daga gidan.
Ta dai nem...
Wani ya zargi dan Rarara da taka Qur'ani.
A cewarsa, tunda har yaron ya taka Allo me dauke da rubutun Qur'ani, to kamar ya taka Qur'ani ne.
Yace kuma hakan ya samo Asali ne daga rashin tarbiyyar da yaron ya samu.
https://www.tiktok.com/@gishazu_kano/video/7653188405257424135?_r=1&_t=ZS-97Lw6iRpS2E
Tauraruwar fina-finan Hausa, Amal Umar ta bayyana cewa, ta daina siyasa.
Ta bayyana cewa tun a farkon mulkin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta daina tallata Gwamnatinsa.
Tace dalili shine bata son ta tallatawa mutane wanda daga baya zai zo yayi ba daidai ba a zo a zageta, dan haka tace masu mata maganar siyasa a comment ma su daina.
Amal ta kara da cewa, ko nawa za'a bata ta hakura, Mutuncinta yafi mata komai.
https://www.tiktok.com/@iamamalumar/video/7653166132571966740?_r=1&_t=ZS-97LuiHT3ZG4
Wata Fitsararriyar matashi ya a Tiktok ta bayyana cewa an biyata Miliyan daya an yi order dinta yanzu ma zata je ta samu wanda ya biya.
Tace duk wanda ya shirya ya mata magana ta DM
.https://www.tiktok.com/@queenminatbackup/video/7652679622244683029?_r=1&_t=ZS-97Lt8GfZNJQ
https://www.tiktok.com/@queenminatbackup/video/7652679622244683029?_r=1&_t=ZS-97Lt8GfZNJQ
Bayan da Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta fito ta yi magana akan cewa ba lallai ta yi aure inda tace tunda ba dole bane.
Ta sha suka sosai a wajan al'ummar Arewa.
A yanzu kuma wadanda suka santa ne suka fito suka fadi gari da unguwar data taso a Jos da halayyar 'yan gidansu.
An bayyana 'yan gidansu da cewa mutanen kirki ne.
https://www.tiktok.com/@muhammadsunnahaljosawy/video/7652737958570708231?_r=1&_t=ZS-97Ls36lSyKl
Tauraron mawakin Hausa, Rarara ya wallafa Bidiyon inda aka ganshi yana Rubutun Qur'ani a Allo irin na Almajirai.
Rarara yayi hakanne bayan da Davido ya kirashi da Jahili a yakin cacar bakin da suka yi.
https://www.tiktok.com/@kahuturarara/video/7653132778753510674?_r=1&_t=ZS-97LWMeYMjtV