Wednesday, January 8
Shadow

Duk Labarai

Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a sansu ba, watau Unknown Gunmen, amma ana kyautata zaton 'yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kashe sojoji 2 a jihar Abia. Sun kashe sojojinne a wani shingen sojojin dake Obikabia jihar ta Abia a ranar tunawa da wadanda suka yi yakin Biafra. A wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumunta, an ga 'yan Bindigar bayan sun kashe sojojin suka kuma kona motarsu kurmus. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/MaziEminent/status/1796136640034873771?t=HYb-5JLLECXTz_AC98Phxw&s=19 https://twitter.com/PIDOMNIGERIA/status/1796144862313468210?t=hzr4r1n221O86UTZxEnPQw&s=19 https://twitter.com/Tony_Ogbuagu/status/1796123554682966269?t=rFUU8b3uT0UElDumzNKfSQ&s=19 Tuni dai gwa...
Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci. Ministan kimiyya da fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji ne ya bayyana haka. Ya bayyana cewa, za'a saka kirkire-kirkiren da matasa ke yi a gida Najeriya cikin abubuwan da za'a rika kallo a matsayin abin afanarwa ga 'yan kasa. Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro na musamman. Yace tattalin arziki na habakane idan aka ta'allakashi akan kirkire-kirkire da fasaha.
A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

Siyasa
Shugaban kasar Kenya, William Ruto yace ba zai iya daukar hayar jirgin sama akan kudi dala Miliyan 150 ba ya dauki tawagarsa zuwa taro a kasar Amurka ba. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a kasarsa. Ya bayyana muhimmancin yin tattalin kudin talakawa inda yace kuma ya kamata shi ya fara nuna alamar abinda yake kira akai, watau rashin almubazzaranci. A baya dai, shima shugaban kasar Kenyan an zargeshi da yin wadaka da kudin talakawa.
A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Siyasa
Shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa 'yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri. Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki. Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.
Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Bidiyo: Sabuwar Rawar da gwamnan Osun yayi ta dauki hankula

Duk Labarai
Sabuwar rawar da gwamnan Osun, Ademola Adeleke yayi ta dauki hankula a shafukan sada zumunta. Gwamna Adeleke ya shahara wajan rawa a guraren taruka da yake halarta. Gwamnan dai kawu ne ga shahararren mawakin Najeriya, Davido. A wannan karin ma ya sake taka rawar a wajan taron karrama mutane da jaridar Vanguard ta yi. Kalli Bidiyon a kasa: https://www.tiktok.com/@gbaramatuvoice/video/7372692648819215622?_t=8mnncGdWWP8&_r=1 Yayin da wasu ke yaba mai, wasu na ganin hakan bai dace ba a matsayinsa na gwamna.
Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Hoto: ‘Yan Sanda Sun Cafke Masu Karbar Adai-daita Sahu Na Sata

Tsaro
Jami’an ‘yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu matasa biyu da ake zargi da karbar babur mai uku na sata. Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta samu ranar Alhamis, inda ta ce ta kuma kwato babur din da aka sace. “A ranar 28 ga watan Mayu, 2024, rundunar ‘yan sandan Adamawa ta samu bayanai game da wani keken napep da aka sace a kan titin Chochi, Rumde, Yola ta Arewa” in ji rundunar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai daukar hotonta na SP Suleiman Nguroje. “Bayan samun labarin, an tura tawagar ‘yan sanda masu sanya ido a hedikwatar Jimeta Divisional ba tare da bata lokaci ba. An yi sa’a, an kama wani Yusuf Adamu mai shekara 18 da kuma Abdul Salam Abubakar mai shekaru 18 a lokacin da suke kokarin sayar da babur din,” in ji ‘yan sandan. ...
YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

YANZU – YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe

Siyasa
YANZU - YANZU: Shugaba Tinubu ya roƙi kungiyar dattawan Arewa su ja kunnen Gwamnonin yankin dake zuwa su tare a Abuja bayan sun ci zabe. Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Shugaban ya ce yana bakin ƙoƙarinsa a matakin tarayya amma ya kamata a sanya ido kan Gwamnoni su ma su riƙa yin abunda ya dace, su taimaki talakawa, "A lokacin zaɓe ana bin mutane lungu-lungu, gida-gida don neman ƙuri'unsu amma da zaran anci zabe sai kaga Gwamna ko dan siyasa ya tare a Abuja ya mance da talakawansa" inji Tinubu. Me zaku ce?