Rahotanni daga kasar India sun ce sanata Godiya Akwashiki dake wakiltar jihar Nasarawa a majalisar tarayya ya rigamu gidan gaskiya.
Sanata Akwashiki dan jam'iyyar SDP ne.
Kuma ya rasu yana da shekaru 52
Golan Super Eagles, Stanley Nwabali ya bayyana cewa, da misalin karfe 2 na dare, Mahaifiyarsa ta rigamu gidan gaskiya.
Yace kuma dama mahaifinsa bai wece wata 2 da rasuwa ba
Yace ji yake kamar karya daina buga Kwallon saboda ba dadi.
https://twitter.com/DAMIADENUGA/status/2006449271948849440?t=fYaMTaXPRVe1T4W_T6kZ1g&s=19
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewa, Hukumar 'yansandan kasar sun kama fastonnan me suna Evans Eshun da yace wai za'a yi tashin Qiyama ranar 25 ga watan Disamba, watau ranar Kirsimeti.
Hukumar 'yansandan ta ce bata yadda da masu amfani da addini suna tayarwa da mutane hankali ba inda tace tabbas an kama Fasto Evans Noah.
Saidai bata bayyana laifukan da ake zarginsa da aikatawa ba.
Fasto Evans Noah yace wai an masa wahayin za'a yi tashin Qiyama ranar 25 watan Disamba sannan an bashi Umarnin sassaqa jirgin ruwa irin na Annabi Nuhu saboda wai za'a yi ruwan sama.
Saidai daga baya da ranar Kirsimeti ta zo ba'a yi tashin qiyamar ba, ya bayyana cewa shi ranar kawai aka sanar dashi, ba'a sanar dashi shekarar da za'a yi tashin qiyamar ba.
Rahotanni daga jihar Ogun sun tabbatar da cewa, an Sallami Shahararren dan Damben Najeriya, Anthony Joshua daga Asibiti bayan Khàdàrìn motar da ya rutsa dashi wanda har ta kai ga abokansa 2 suka rasa rayukansu.
Gwamnatin jihar Ogun ce ta tabbatar da cewa an Salami Anthony Joshua daga Asibitin.
Ta sanar da cewa, an sallameshi daga Asibitinne ranar Laraba da yamma.
Hukumar sojojin Najeriya ta yi martani kan kalaman Sheikh Gumi game da hare-haren da kasar Amurka ta kawo Najeriya.
Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya yi Allah wadai da harin da kasar Amurka ta kawo Najeriya inda yace hakan rainine.
A yayin da yake magana da manema labarai, me magana da yawun hukumar sojojin Najeriya ya amsa wata tambaya da aka masa cewa mw zasu ce kan Allah wadai da Gumi yayi da kawo harin da Amurka ta yi Najeriya?
Yace suna sane da abinda Gumi ke cewa, amma ba hakkinsu bane su dauki mataki akansa.
Yace akwai hukumomin da ke da wannan Alhakin kuma yasan cewa, zasu dauki matakin da ya dace.
https://twitter.com/AsakyGRN/status/2006390924893401363?t=tLObFx3bcrWl5goXd_Eb9g&s=19
Wannan matar me suna Aisha Isah Yelwa, ta mayar da Naira Miliyan 330 da aka tura bankinta bisa kuskure.
Tana zaunene a Lapai, Jihar Naija.
Da yawa sun jinjina mata da wannan namijin kokari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito kofar gidan Gwamnatin jihar Kano inda ya karbi masoyansa da suka je dan tayashi murnar shiga sabuwar shekarar 2026.
An ganshi yana dagawa masoyansa hannu a saman mota.
https://twitter.com/Noble_Hassan/status/2006519668509651005?t=NuyV3ytmCDY9G0n0RBMcvg&s=19
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yace shi da iyayensa duk musulunta suka yi.
Yace ya taso a matsayin Kirista kuma ya je makarantar Kiristoci.
Sannan yace a da sunansa Samuel amma aka ce ya je ya shiga Musulunci ya koma Mohammed, sannan yace mahaifiyarsa ma tana cikin matan zumunta amma daga baya duk sun musulunta.
Saidai yace a gidansu raba kafa aka yi, wasu suka zama musulmai, was suka zama Kirista ta yanda duk inda ta fadi sha.
https://twitter.com/OzorNdiOzor/status/2006458422951379229?t=aEfZBD7hjtLPnTHEV2ENmQ&s=19
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin shekarar 2026 hannu a yau, Laraba.
Kasafin kudin na Naira Tiriliyan 1.4 ne wanda hakan ya samu halartar manyan jami'an Gwamnatin Kano.
Saidai rashin ganin mataimakin Gwamnan jihar a wajan ya jawo cece-kuce.
Dama dai wata majiya tace Gwamna Abba shi kadai zai koma APC ba tare da mataimakin gwamnan ba.
Hakanan a dazu ne muka ga Abba ya gana da shuwagabannin jam'iyyar APC na jihar Kano.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya koma jam'iyyar ADC.
Atiku Abubakar ya tayashi murna inda yake cewa, yana masa maraba da shigowa jam'iyyar ta ADC.
Atiku yayi fatan zasu hada hannu dan ciyar da Najeriya gaba.