Monday, November 23
Shadow

Duk Labarai

Gwamnatin tarayya ta bude sabbin tashoshin talabijin 100 da ‘yan Najeriya zasu rika kallo Kyauta

Gwamnatin tarayya ta bude sabbin tashoshin talabijin 100 da ‘yan Najeriya zasu rika kallo Kyauta

Duk Labarai
Gwammatin tarayya na sanar da bude gidajen talabijin 100 da 'yan kasa zasu rika kallo kyauta ba tare da biyan kudi duk wata ba. A jumlace an musu sunan FreeTV. Fadar shugabab kasa ce ta sanar da wannan a ranar Laraba. Sanarwar tace gidajen Talabijin din sun hada dana labarai dana wakoki dana wasannin yara dana ilimi a ciki da wajen Najeriya. Sanarwar tace wannan mataki ne na inganta kafofin watsa labarai zuwa na zamani.
Idan Zarmalulun ka na mikewa amma baka ganin Jijiyoyi akwai matsala>>Inji Malama Kausar inda ta bayar da maganin da zaia iya hadawa da kanka a gida

Idan Zarmalulun ka na mikewa amma baka ganin Jijiyoyi akwai matsala>>Inji Malama Kausar inda ta bayar da maganin da zaia iya hadawa da kanka a gida

Duk Labarai
Malama Kausar ta bayyana cewa, idan Zarmalulun mutum ya mike amma bai ga jijiyoyi akai ba to akwai matsala. Hakan na nufin jini baya yawo a wajan yanda ya kamata. Ta bayyana cewa akwai maganin da ake yi wanda shine shan kankana da 'ya'yan kankanar. https://twitter.com/i/status/2067381396314771921
Turawa sun ce wai dala Biliyan $38 na mallaka to ko Matatar man fetur dina kadai ta zarta dala Biliyan $40 kuma ina da kamfanoni da sauran kadarori da basu sakasu a lissafi ba>>Inji Dangote

A wata hira da aka yi dashi, Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, bayanin da turawa suke cewa wai kudinsa dala Biliyan $38 ne ba gaskiya bane. Dangote yace ko matatar man fetur dinsa kawai ta fi Dala Biliyan $40. Sannan kuma akwai wasu kadarorinsa da ba'a sakasu a lissafi ba. Dangote da aka tambayeshi gashi yana da kudi amma baya alfahari sai yace tarbiyyar da ya samu daga gidane ba'a koya musu Alfahari ba. https://twitter.com/i/status/2067288672043446613
Kalli Bidiyon: Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta shigarwa makarantar da ‘yata ta rasu, dan haka nima ina neman idan akwai kungiyar Musulmai nima su shigar min>>Inji Mahaifiyar Nihal

Kalli Bidiyon: Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta shigarwa makarantar da ‘yata ta rasu, dan haka nima ina neman idan akwai kungiyar Musulmai nima su shigar min>>Inji Mahaifiyar Nihal

Duk Labarai
A jiyane dai muka kawo muku rahoton wata yarinya Nihal daga Kano wadda ta rasu a makarantar kwana. Rahotannin farko sun bayyana cewa Gwale-gwale aka baiwa Nihal saboda bata yi sallah ba duk da ta gayawa malamin su cewa tana fama da rashin lafiya amma aka tilasta mata yin gwale-gwalen wanda shine yayi sanadiyyar mutuwarta. Mahaifiyar Nihal a hirar da Freedom Radio suka yi da ita tace masu makarantar sun je gida suka mata gaisuwa suka ce mata wai diyarta bata da lafiyane shine aka mata addu'a a ruwa aka bata tasha daga nan ta rasu. Tace amma sun gargadeta kada ta saurari duk wani labarin da za'a kawo mata. Tace sun kaiwa 'yansanda rahoto aka je makarantar dan zantawa da dalibai amma makarantar tace ba za'a zanta da daliban ba, inda suka iske Lauyoyi da Kungiyar Kiristoci ta Naje...
Da Duminsa: Hadiza Gabon ta saki Bidiyo a karin farko tun bayan da matar Salim Goje ta zargeta da yin soyayya da mijinta

Da Duminsa: Hadiza Gabon ta saki Bidiyo a karin farko tun bayan da matar Salim Goje ta zargeta da yin soyayya da mijinta

Duk Labarai
A karin Farko, Hadiza Gabon ta saki Bidiyo a shafinta na sada zumunta tun bayan zargin da aka mata cewa tana soyayya da Saleem Goje. Saidai ba kalar Bidiyon da ake tsammanine Hadiza Gabon ta saki ba. Da yawa zasu yi tsammanin Hadiza Gabon zata fito ta wanke kanta daga zargin da ake mata ko kuma ta fadi yanda lamura suka kasance. Saidai kawai ta ci gaba da harkokinta ne inda ta saki Bidiyon hirar da ta saba yi da jarumai. Saidai me hakan ke nufi? Wata kila shikenan ba zamu ji ainahin abinda ya faru ba ko kuma ta gaya mana bangarenta na zargin da ake mata. https://www.tiktok.com/@hadizaaliyugabon/video/7652456983181921538?_r=1&_t=ZS-97IQPF8sRxk
Da Duminsa: Davido ya kara yiwa Rarara zazzafan Martani da Hausa

Da Duminsa: Davido ya kara yiwa Rarara zazzafan Martani da Hausa

Duk Labarai
A yayin da a dazu muka kawo muku cewa, Davido ya saka kalaman da Rarara ya masa, a shafinsa na X. Inda ya rubuta cewa, Rararan ko sunansa bai iya fada ba, Debidoo yake cewa. A yanzu Davido yayiwa Rarara martani da Hausa. Ya wallafa a Story dinsa na Instagram cewa, Rarara ya kamata ya zama dan kishin kasa sannan ya daina fifita son ransa akan abinda ya shafi al'umma. Sannan ya daina zama karan farautar 'yan siyasa. Yace kuma duk mutum me kishin kasa ba zai yi shiru akan abinda ke faruwa a Najeriya ba. Davido ya kara da cewa, da ace kana da Ilimi da na tsaya na yi magana da kai, amma komai baka sani ba sakarai kawai.
Ni nasan ba zan dade a Duniya ba saboda suna neman rayuwata ruwa a jallo>>Sheikh Salihu Zaria ya fallasa wasu mugaye da suka sakoshi gaba

Ni nasan ba zan dade a Duniya ba saboda suna neman rayuwata ruwa a jallo>>Sheikh Salihu Zaria ya fallasa wasu mugaye da suka sakoshi gaba

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Salihu Zaria ya bayyana cewa yasan ba zai dade a Duniya ba dan haka mutane su zama shaida ya isar da sakon Allah da ya zo dashi. Malam yace yasani cikin wadanda za'a nemi rayuwarsu akwaishi a ciki. Malam ya bayyana hakane a wajan wani majalisi da yayi me cike da taba zuciya. https://www.tiktok.com/@voiceoftheyouths_0/video/7652274408437878036?_r=1&_t=ZS-97HoMB2GsUs