Wannan matar ta rika bi titi tana lika hotunan wata budurwa data ce ta mata kwacen miji.
Bidiyon lamarin ya dauki hankula kuma ya watsu a shafukan sada zumunta:
https://www.youtube.com/watch?v=_aSX_McPpos
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar canza taken Najeriya.
Wannan yana nufin daga yanzu za a daina National Anthem na "Arise O Compatriots" za a koma yin tsohon National Anthem da aka yi zamanin turawa "Nigeria, We hail thee".
Shin kuna marana da wannan mataki da shugaba Tinubu ya dauka ?
YANZU-YANZU: Ga sabon taken Najeriya da za a koma yin amfani dashi daga yau dinnan:
Wanda ya rubuta - Lilian Jean Williams (1960) wanda yayi kidansa - Franca Benda
Ga Sabon Taken National Anthem din Nigeria ⤵️
Nigeria, we hail thee,Our own dear native land,Though tribe and tongue may differ,In brotherhood, we stand,Nigerians all, and proud to serveOur sovereign Motherland.
Our flag shall be a symbolThat truth and justice reign,In peace or battle honour’d,And this we count as gain,To hand on to our childrenA banner without stain.
O God of all creation,Grant this our one request,Help us to build a nationWhere no man is oppressed,And so with peace and plentyNigeria may be blessed.
Ku bayyana mana ra'ayinku kan wannan mataki da shugaban kasa ya dauka na canja taken Najeriya....
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Hafiz Abubakar ya kaiwa me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ziyarar Mubaya'a.
Wadannan hotunane daga ziyarar da ya kaiwa sarkin:
A ranar Laraba, Gwamnatin tarayya ta janye zarge-zarge 3 na ta'ddanci da takewa shugaban Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo.
Tun a watan Janairu ne dai sojoji ke tsare da Bodejo bisa wannan zargi inda suka ki bayar da belinsa.
Saidai a ranar Laraba da Ministan Shari'a ya je gabatar da Zarge-Zargen da akewa Bodejo dan ci gaba da shari'a, sai ya ce gwamnati ta janye karar data shigar akanshi.
Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki ganin cewa a baya gwamnatin ko beli ta ki yadda ta bayar da Bodejon.
Ana dai zargin Bidejo ne da kafa wata kungiyar Funali wadda ake zargin ta ta'ddanci ce da kuma basu makamai da sauran kayan aiki.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a shekarar 2023 ya bayyana cewa, ya shirya mulkin Najeriya amma Shugaban kasaz Bola Ahmad Tinubu bai shirya ba.
Saidai Atiku yace amma Tinubu bai makara ba, zai iya daukar matakan da suka kamata wajan magance matsalolin kasarnan idan da gaske yake.
Atiku ya bayyana hakane a sakon da ya fitar na cikar mulkin Bola Ahmad Tinubu shekara daya akan mulki.
Ya kara da cewa, Tinubu da mukarrabansa basu san hanyar da zasu dauka ba wajan magance matsalolin Najeriya, suna canki cankane akan abinda suke tunanin zai iya yin aiki.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kashe jimullar mutane 4,416 da yin garkuwa da guda 4,334 a shekara 1 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi yana mulki.
Wata gamayyar masu fafutukar kasa da kasa da kuma Najeriya su 84 ne suka fitar da wannan rahoto.
Rahoton yace kungiyoyin basu saka abubuwan dake faruwa na fashi da makami da sauran laifuka ba.
Sunce wannan lamari ya sanya 'yan Najeriya sun rasa 'yancin rayuwa me inganci da kuma rayuwa cikin walwala.
Kungiyar tace ci gaba da wannan lamari ya jefawa 'yan Najeriya tsoro da fargaba da rashin tabbas.
Kuma sun ce idan gwamnatin Tinubu bata dauki mataki kan lamarin ba, suna daf da fitar da rahoton yanke tsammani akanta.
Sunce suna jawo hankalin gwamnatin Tinubu data yi kokari wajan sauke nauyin dake kanta na kare rayuwa da dukiy...
Hukumomin soji dana CJTF a jihar Borno sun kama wani soja da laifin satar harsasai.
An kama sojan ne me suna Corporal Francis Bako a tashar motar Kano dake Maiduguri.
An kamashi ne bayan samun bayanan sirri akan satar harsasan da yayi.
Sojan dai na kan hanyar zuwa Kadunane bayan da aka kamashi da harsasan guda 602 kuma yana tsare yanzu haka.
An ga gawar wata mata me ciki kwance tsirara akan titi wanda lamarin ya tayarwa da mutane hankali.
An ga gawarne a titin Amaraku-Umudim dake karamar hukumar Isiala-Mbano ta jihar Imo.
Saidai ba'a kai ga tantance menene sanadiyyar mutuwar matar ba.
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana dawo da tsarin tallafawa mutane wanda ta tsayar a watannin da suka gabata.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a matsayin shiri na cika shekara daya da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta yi.
Tsarin dai wanda ya hada da ciyar da dalibai, da Npower, da baiwa mutane gajiyayyu kudin tallafi da tallafawa 'yan kasuwa da sauransu a yanzu ya dawo zai ci gaba da aiki.
Ministan yace dama a baya an tsayar da tsare-tsarenne dan bincike da kuma kawar da matsalolin dake cikin tsarin kuma yanzu an kammala.
A dambarwar da aka yi ta dakatar da tsarin, ta hada da dakatar da ministan jin kai Beta Edu wadda aka yi zargin ta aikata ba daidai ba.
Saidai a yayin da yake maganar, Mi...