Sunday, November 22
Shadow

Duk Labarai

Kiran da Atiku yayi cewa a saki mahaifiyata lokacin da aka sace ta cutar dani yayi>>inji Rarara

Kiran da Atiku yayi cewa a saki mahaifiyata lokacin da aka sace ta cutar dani yayi>>inji Rarara

Duk Labarai
Tauraron mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa, Kiran da Atiku Abubakar ya yi a lokacin da aka sace mahaifiyarsa cewa a saketa cutar dashi yayi. Yace suna daf da karbota sai Atiku ya wallafa a kafar sada zumunta cewa a saki mahaifiyarsa. Yace Atiku na fadin hakan sai wasu mutanen dajin suka je suka fanshi mahaifiyar tasa a hannun wadanda ke rike da ita. Yace hakan yasa aka kara daukar lokaci me tsawo kamin kubutar da mahaifiyar tasa. https://vt.tiktok.com/ZSQsF42NY
Kaddara ce kuma wannan zai iya faruwa ga kowa>>Inji Matar da maza 8 suka mata cikin shege kuma ta haifama kowannensu dan

Kaddara ce kuma wannan zai iya faruwa ga kowa>>Inji Matar da maza 8 suka mata cikin shege kuma ta haifama kowannensu dan

Duk Labarai
Matar da ta haifi yaran gaba da fatiha 8 da maza daban-daban watau kowanne yaro da mahaifinsa ta bayyana cewa kaddara ce. Matar tace ana ta maganarta a garinsu ana nunata a matsayin abin kwatance. Saidai tace hakan bai dace ba dan wannan abu ta daukeshi kaddarace kuma zata iya fadawa kan kowa. https://twitter.com/i/status/2067170298437230736
Da Duminsa: Davido yawa Rarara Martani

Da Duminsa: Davido yawa Rarara Martani

Duk Labarai
Bayan sukar da Rarara yawa mawaki Davido saboda Davido din ya saka riga me dauke da sunayen dalibai da aka sace a jihar Oyo. Davido din ya masa martani da safiyar yau. Davido yayi repost na abinda Rarara ya gaya masa inda ya rubuta cewa Rarara ko sunansa bai iya fada ba wai Debidoo yake cewa. https://twitter.com/i/status/2067162958384513472
Da Duminsa: Ji matakin da aka dauka akan Sadiq Sani Sadiq saboda yace zai shirya zàngà-zàngà

Da Duminsa: Ji matakin da aka dauka akan Sadiq Sani Sadiq saboda yace zai shirya zàngà-zàngà

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Sadiq Sani Sadiq da yake shirin shirya zanga-zanga akan matsalar tsaro ya bayyana cewa an nemeshi. Baidai bayyana su wanene suka gayyaceshi ba amma da yawa na kyautata zaton DSS ne. Sadiq yace zai amsa gayyata amma zai sanar da lauyoyinsa kuma ko da an jishi shiru sai a nemeshi a wajan wanda suka gayyaceshi. Sadiq dai ya ce rubuce-rubuce basu kawo karshen matsalar tsaro ba shiyasa suke shirin yin zanga-zanga.